← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 149

Sashe 23

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

,yayi shr yana tunanin ta inda zai soma ,itama shr tayi Sai dai,haka kawai ta tsinci kanta da jin ,faduwar gaba. haka nan kallon da yaya faruk din kema ,yasa taji wani iri ajikinta ,dan haka ,ta sunkuyar da kanta kasa kawai tana Jira daga gareshi.
,can ya numfasa,hade da jin kwarin gwiwa yazo masa ,ya danyi gyaran murya" tukun yace daman nazo ne na fayace miki abinda na dade Ina boyewa akanki , .
Take taji gabanta yashiga faduwa ,ta dan dago kadan ,taga ita yake kallo , ahankali tace akan mefa?
Sannan ta km maida kanta kasa tana jin yadda gabanta ke lugude faduwa.
Yayi murmushi yana cigaba da kallonta, cikin natsuwa da jarumta.
yasanar mata da komai .

tun da yasoma maganar sa tayi shr kawai hade da sake sunkuyar da kanta kasa, sosai badan tana jin dadin sauraron abinda yake kokarin fahimtar daita bane ,taji hankalinta ya yayi matukar tashi dan haka , ahankali ta dago kanta , ta zuba masa idanunta , Sai data tabbatar daya gama fadar abinda yakawoshi, a dan frigice tace ,dan Allah yaya kayi hakuri wlh akwai wanda zuciyata ta dade da kamuwa da soyayyarsa , Amman kayi hakuri idan maganata ta bata maka rai ,yace Ina fa za bata min rai Ai iya gaskiyar ki kika fada Sai dai ki sani zuciyata bazata iya wannan hakuri dake bani ba, Sai dai zan baki lokaci kiyi tunani akai , tace tunanin me km zanyi?byn na fada gsky nifa bawani tunanin dazanyi ka dai yi hakuri kawai ka nemi wata.
,ta juya ta wuce tabar sa nan tsaye .
,da mamaki yabi bayanta da kallo ya dauki lokacin tsaye a gurin batare da yasan abinda zaiyi ba , Ganin tsayuwa nasa bata da wani amfani yasa yasoma kokarin daga kafafunsa da suka masa mugun nauyi.
, ahankali yake daga kafafunsa yana saka da warwara" da tunanin makomasarsa a gurinta .
,a fusace shemah tashiga part dinsu tana zuba tsaki da zage zage iri iri har mmnta ta tambayeta abinda yasameta tace mata bakomai.

Byn kwana biyu

Da misalin karfe takwas na dare fk ya km samu shemah da zance ,shi fa bai ji zai iya wani hakura daita ka " kawai tayi hakuri ta amincewa aurensa .
,tace ni dai dan Allah yaya kayi hakuri karabudani, wlh da bbu wanda nake so ne ,zan iya aurenka dan kaima baka rasa komai da zankika ba .
kadai yi hakuri kawai .

al'amarin dayayi matukar dagawa fk hankali kennan ,yayi shr kawai yana kallon yanayinta tare da nazarin kalamanta masu kokarin tarwatsa masa zuciyar rasa "
yarasa yadda zaiyi daita, can dabara tazo masa, dan haka ya tsareta da idanunshi Yace ke banso iskanci da rainin hankali fa" ni zaki cewa kina da wanda kike so byn Banga uban da kike saurara ba.
,lafazinsa yayi,
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Page 23-24

Ni dan girman Allah kabarni na wuce tun kafin laifina ya Karu.

,Murmushi karfin hali kawai yayi ,tare da nuna mata hanya da hannushi alamun ta wuce din.

, kasa tafiya tayi " sakamakon idanushi da taji yana mata yawo a gangar ajikinta . Gabadaya taji tamkar ya daureta ne .
takasa kwakwaran motsi" jikinta yayi bala'in yin sanyi.
,taji ina ma zuciyarta na da yanci da bata kamu da soyayyayar deeni ba.

Da bbu shakka zata iya hakura da kamil tunda shima yana da nashi kyawun daidai gwargwado .

Yayi shr kawai yana kallonta" kaunarta ce ke tasomasa tare da nukurkusan zuciyarsa.
,ya dinga jin tamkar ya halaka kanshi lokacin daya tsinci idanun deeni akan su.
ya dinga kallonta "yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa " da gske dai yana shirin yarasata kennan ,rashima na har abada.
km ta haramta ta zama matarsa wani irin zugi zuciyarsa keyi ahankali
Yakira sunanta..Zeenat kina son deeni sosai ko ? Cikin sanyi
ta dago kanunun idanunta ta kalleshi dasu "sannan tace , wannan wace irin tmby ce ? Yace amsa kawai nake bukata ,tace to bana son shi shikennan.
Karkimin karya mana Kina son shi kalli...kalli yadda yanayinki ya canza jikinki har rawa yake saboda kin ganshi .
ya tabbata kennan baki sona ,rainamin hankali kawai kika dinyi .

A fusace Zeenat tace Nifa karka zageni da laifi da bansan na aikata ba. mgnr ina sonshi ko bana sonshi ma duk bata taso ba .

kai kanka kasan bantaba amsa maka da Ina sonka ba.
ballanantana kace yaudararka nayi ka dai yi hakuri Allah ya hada kowa da rabonsa , yace ok yanzun duk tarin son da na miki yazama tarihi kennan ?
Ta zuba mishi ido kawai dan tasan duk abinda zata gaya masa ahalin yanzu ba fahinmta zai yi ba shiyasa tayi shr taki cewa komai
Ahankali Ya girgiza kanshi kawai batare da sake cewa mata komai ba ya juya yasoma tafiya.

, Tayi jim jikinta ya mata tsanyi ,bata ji dadin yadda taga reaction dinsa ba .
tasan kwata kwata bata kyautawa masa ba. Amman ba yadda taiya da zuciyarta " DEENi shine muradin ranta .
raba zuciyarta dashi tamkar barazana ce ga rayuwarta.
Duk da taji ba dadi ba hakan bai sa taji tausayinsa yashigeta har taji zata iya hakura da auren DEENi . Dan haka ko ajikinta ta wuce.

Jikinta a sanyaye yashigo part dinsu hankalinta a tashe
Tana shiga daki Ta daure fuskarta "ganin ya shigo dan a zatonta yana shigowa zai zabgamata mari.
sanye yake da t shirt din su na sojoji da wando.

Tana jinshi yacewa Ummi shi ya wuce sai da safe "Ummi tace can zaka kwana ne yau ?
yace eh "akwai abinda zai maidani tace to Allah ya tsare min kai ya km bada sa'a ,ka yawaita addu'a dan Allah yace Ina yi sai dai zan kara kulawa .
ya sake wuce zeenat zaune ko kallon inda take baiyi ba .

bayansa tabi da kallo tana jin wata irin masefaffiyar kaunarsa nabin jininta, hade da ratsa kowani part na jikinta.
, aranta tace attajirina kennan ,miskilili zaki maza .
nan ya fita yabarta da dadeden kamshinsa tare da fargaba.
sai dai, da ganin yanayinsa yana cikin tsananin fushi .

da misalin karfe tara dare tana kwance akan gado" juyi kawai take, yayinda zuciyarta ke nazari akan irin kallon da yaya deeni yayi mata, dazu sakamakon ganin da yayi mata tare da kamil .

ta ji tamkar takirashi tabashi hakuri amman tsananin tsoransa ya hanata aikata hakan , zuciyarta ce ta bata shawara kan tura masa text ba sai takirashi ba .
dan haka ahankali ta mirgina ta janyo wayar Ummi dake kan bedside .
ta soma rubuta masa text da niyar turawa masa " sai km taji zuciyata na gargadinta akan kar ta sake ta tura masa text din . Tayi tana tunanin ,ta tura ne ko ta share
Tayi haka ya yafi sau goma kafin daga karshe tayi jahadi ta tura masa .

Yaya dan Allah kayi hakuri idan na bata maka rai dazu wlh bazan sake ba ... daga zeenat

Byn ta tura sakon ne ta goge "sannan takoma ta kwanta lamo tana jin yadda kirjinta ke tsarkewa ,ahankali ta lumshe" idanunta ,xuciyarta ke beating tare da yi mata fadar abinda ta aikata .
ita kanta tasan tayi babban kuskure sosai wajen tura masa text ,dan tasha jin yadda yake yawan yi complain akan tura masa sako ko kiran wayarsa yayinda yake kan aiki ,
Sai dashi duk lokacin daya gadama zai kiraka idan km baka dauka ba yazama matsala .
dan haka tayi shr kawai tana fidda numfashi sama sama .

Tsawon lokaci tana kwance "tana tunanin abinda zai biyo baya idan yaga sakonta , addu'a take Allah yasa ba karawa kanta laifi tayi ba agurinsa .

take tsoro da fargaba suka taru suka dira mata " alokaci daya.
Idanunta a lumshe har lokacin tana saka da warwara deeni dan ra'ayi baka masa dole ballanantana ta tursashi .

can taji alamun shigowar sako a zaburi ta mike" ta rarumi wayar jikinta har rawa yake .
idanunta ne suka ci karo da reply dinsa .
hankalinta a tashe tasoma karanta text din .

Ke ... Banida lokacin karanta wannan shirmen naki na baza , aikina yana da mahimmanci a wajena banida lokacin hada aikina da zantuttukan marasa ma'ana dan haka ki kiyaye gaba ..

Tana gama karantawa ta sauke ajiyar zuciya sannan ta sulale takoma ta kwanta tare da lumshe idanunta.
Tabbas tasan ta daukarwa kanta abinda yafi karfinta .
tayi shr ,tana son tayi nazari akan kalamansa tasan dai yakaranta sakonta sarai .

tsabar rainin wayo ne da miskilanci irin nasa .
yasa ya nuna kmr bai da lokacinta .
tayi juyi tana mai tausayawa kanta na nacewa auren DEENi.
yanzu Gabadaya son aurensa ya sire mata ya fita akanta.
, tsoro aurensa take km sai yanzu maganganun Ummi ke sake shigarta .
Inda tace zeenat ,kin fahimtata ne kawai deeni dana ne dana haifa a cikina.
baki fini sonshi ba sanin halin miskilancinsa da girman kai irin nasa yasa kikaga naki amincewa da aurenku wahala kawai zakisha a hannushi .
, gara yaje waje can ya nemo matarsa.

batayi aune ba taji saukar hawaye nabin kuncinta" bata hana su zubowa ba ,domin ita kanta zata fi so ta zubar dasu ,kodan samun natsuwarta.
Km ko ba komai hakan zaisa taji sanyi da ragewa kanta radadin abinda ke nukurkusan ruhinta.

Jikinta yayi matukar yin tsanyi ahankali tasoma sambatu ..
Wayo Allahna... ni zeenat yaya zanyi da zuciyata data ta makance akan kaunarka.

Ina sonka yaya deeni har bansan yadda zan misalta tarin soyayyata gareka ba.
kaunarka ajinina da ruhina yake .
daita Allah ya hallice . bazan iya daina sonka ba muddin rai .
koda baka sona ni Ina sonka km zan iya jurar komai akanka ,raba zuciyata da soyayyarka tamkar rasa numfashina ne .
Haka tayi surutai har sanda Tajiyo motsen shigowar Ummi .
tayi shr tare da saurin juya mata baya.
tana cigaba kukanta, kasa kasa batare Ummi ta Gane halin da take ciki ba .
Zuciyarta ke mata wani irin ciwo da radadi mai zafi .
Chapter 23 · 0% Book details