← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 149

Sashe 54

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

' kusan minti goma ya dauka Yana kallonta batare da yayi yunkurin dakatar daita ko ce mata wani abu ba ' kafin daga baya ' ya gyara zamansa Tare da numfasawa. cikin tsantsar ladabi da laushin murya yasoma magana, Dan Allah inna kiyi hakuri ki tafiyarki abinki "tunda yarinyar nan Ta nuna bazata biki ba.

, Say da inna ta tabe bakinta tukun sannan tace "yo Ai ka kace min nayi tafiyata man " tunda fadeela da danta sunfini daraja da kima a idanunku" duk irin wulakanta min jika da wannan banza yaron nata yayi baku Gani ba Sai na laifin zakugani .

,big dady sam Bai damu ko jin mamakin abinda inna tace ba, dan yasan kadan daga cikin aikinta. domin zata iya fadar fiyye da abinda yafi haka ma.

Dan haka big Dady Bai damu da abinda tace ba ya kara kwantar da murya cike da girmamawa ya sake cewa , Dan girma Allah inna kiyi hakuri kiyi tafiyarki tare da yiwa yaran nan fatar alkhari a rayuwar aurensu tunda komai yazo da sauki saki daya ne yayi mata . Km ya maidaita .
Duk ma da abinda Deeni yayi mata Ai bai laifi bane tunda ita tajawa kanta .

,inna ta katse big Dady Ta hanyar daga masa hannuta,dakata... ya isa haka karka cika min kunne" naji zan tafi amman wlh wlh kaji na rantse ,to kagayawa wannan gantalallan "dan 'naka yakiyaye ni" kar ya km yin gigin kai hannushi da sunan sake taba min lafiyar jikata.

Domin ita ba jakar gidan ubansa bace .
Big Dady yace shikennan kiyi hakuri ki yi tafiyarki zan gaya masa .

Inna Tace da dai yafi dan wlh idan ya km yunkurin kai hannushi jikinta ba yarda zanyi ba .

, da kyar da Allah da rarrashi, big Dady da sauran mutane dake zaune a parlour aka samu inna ta fice daga parlour tana zage zage.

'ahankali big Dady Ya sake numfasawa tare da duban inda Deeni ke zaune ya hade fuska tamkar hadari suna fuskartar juna ,tsawon lokaci big Dady ya dauka Yana dubansa ,kafin daga baya yayi masa fada sosai akan irin hukuncin daya dauka akan Zeenat din sannan daga karshe ya bige dayi masu nasiha mai shiga jiki shi da Zeenat ,akan su taru su zauna lfy.

Yace deeni Kayi hakuri akan laifin da Zeenat ta aikata a gareka, hakika munsa bata kyauta ba amman ka dauka daman can haka Allah ya rubuto cikin data zubar maka ba masu rayuwa bane a doron kasa.

Dan haka kayi hakuri ku zauna lfy hakan kadai shine muradinmu da km kwanciyar hankalinmu dana umminku gabadayan .

Sauran en'uwa ma kowa ya tofa albarka bakinsa sannan
,Jiki a sanyaye Deeni yace yaji tare da yin musu godeya , duk da ran nan nashi , in yayi dubu to a jagule yake .
da kyar ya samu ya kokarta ya mike tsaye dan kokarin barin parlour har yakai daidai bakin kofar fita .

" cak yaja ya tsaya jikinsa har wani shake yayi sakamakon jin sautin muryar umminsa mafi soyuwa a zuciyarsa .
' ,kaje gida kajirani gani nan zuwa yanzu, abubuwa dayawa suka zo masa tare da tsaya masa a rai .
jin yadda ummi tayi maganar kadai yaisa yasan yadda ranta yayi kololuwar bace ..
dan gane da abubuwan dake faruwa a atsakaninsa da Zeenat kasa cewa komai yayi sai , kansa kawai daya iya daga mata alamun yaji 'sannan Yakarasa barin parlour .

Byn kmr minti ashirin Zaune Ummi da Zeenat suka taddashi kan kujerar one siter hannushi rike da waya yana daddannawa " a yadda yake operating din phone dinsa zaka dauka kwata kwata baya tattare da wata matsala ne" ballanantana wani abu makamanci damuwa , amman a hakikanin gsky kallo daya zaka yi masa kasan cewa yana tattare da kunci may tarin yawa .

,a fusace Ummi take kallonsa ganin yadda Ya hakince tamkar Bai san da tsatuwar wasu halitu a gurin ba.
,' yayinda gabadaya ranta a dagule yake da abubuwan da ya dinga yiwa inna a gaban dangi .
wanda inda wani ne yasanar daita zai iya yin abinda yayi" zata iya ransuwa da Allah akan sharri aka,a masa ,amman Sai gashi a gabanta komai ya faru.

ahankali DEENI ya dago rikitattun idanushin dasuka gama canza kala tsabar tashin hankali dayake ciki " ya zubawa ummi yana kallonnta ..

Ganin haka tasa , ummi sake hade ranta tamau dan batason yakawo mata rainin wayonsa dayasa ba "sannan ta cigaba dubansa .
,'tare da cewa yayi maka kyau... Deeni, da duk ma abinda kayi min, na gode matuka "tun daga kan dukar min yarinya dakayi tamkar kasamu baiwa tare da hado min ita da takarda saki har kawo abubuwan da suka faru a yau .
Dan wulakanci ma yau kusan tsawon kwanaka uku kennan rabon daka Tako kafafunka cikin gidan nan . tsabar kagama rainani .

shr yayi still yana sauranta ya kasa koda furta mata daidai da kalma daya ce .

, Ummi ta dubi inda Zeenat ke tsaye wace gabadaya atsorace take dangane da yanayin rayuwar data jefa yayan nata ciki .
,ummi tacigaba' ai kinga irin abinda nake gudar miki a cikin aurensa, wahala da zaman kunci tattare da nadama" Amman kike nace akan kinji kin Gani ' bbu wani abunda zai faru Sai alkhari " yanzu wa gari ya waya.
dubi yadda kika koma dan girman Allah tamkar wacce aka hako daga cikin kabari .

Da gani ba say ma an tmby ba nasa zaman hakuri da kunci kikeyi agidansa dan nasan may hali baya canza halinsa .

Deeni dake zaune yayi shr tare da cigaba da duban ummi kawai batare da yace mata komai " dan ma rasa abinda zaice mata yayi km yana son ta fahimce shi tasan duk abinda take tunani akansa ba haka bane amman Sam yakasa magana .
Ummi ta sake juyowa inda Deeni ke zaune suna fuskantar juna dashi .

" Tambayar da zan maka yanzu nake son ka amsa min d eh ko A'a.
daman can ba kai ne da kanka ,ka nemi auren Zeenat din a gurina ba?

.'ahankali Deeni ya dagawa Ummi kansa .alamun shine ya furta Yana son ta aura masa Zeenat din .

Ummi Tacigaba To yanzu dan ta zubar da ciki ne yasa har ka iya mata irin wannan dukan mutuwar ?
Km har da ikirarin zaka kashe min Ita dan baka san ciwonta ba .

Ko kana tunanin idan ka mata illa zan barka ne kaima .

Kai gaka sarkin en zuciya madadin ka kawo maganar gabana nasan yadda zanyi solving din matsalar batare da kowa yasani ba , shine ka tuzartata Tare da zartar da hukunci ta hanyar azabtar min da yarinya tamkar kasamu baiwa.

Sai lokacin deeni yaji wani kuzarin yazo masa Dan haka cikin , tsanyin murya tamkar may shirin zubda kwalla Deeni soma magana " kwarai first lov nayi kuskure guda daya narashin sanar min ki kafin zartar da komai amman na rokike kiyi hakuri.

Amman ta ya zuciyata zatayi sanadiyyar barinta cikin kunci da cuta alhalin nasan amanarta kika damka min acikin tafin hannuna' ya fadi haka tare duban tafin hannun nashi da kwayar idanushi
, indai akwai wanda na cuta to kece da bansanar miki da abinda tamin ba ,kafin na zartar da hukuncina akanta . amman ki gaya min me yakamata nayi byn na kamata dumu dumu da laifin zubar min da ciki har Sau biyu tare da shan maganin hana daukar ciki Sau ba iyaka .

Cikin zafin rai ya Kamo lips dinsa na kasa yasoma cizawa da karfi sakamakon hawayen dayaji yana kokarin son zubo masa.
" wani irin nauyin zuciyarsa tayi "yana ji yadda kirjinsa ke masa zafi da ciwo tamkar an daura masa dutse may shege nauyi a sama kirjinsa , .

, Da kyar yasamu yacigaba da magana. mutane na gudun tsautsayi amman ni na zauna da nawa tsautsayin batare dana sani ba 'bana da miradin danayi gida biyu amman nayi tunani indai tsautsayi ne ya hau kaina "to itama dole tsautsayi ya hau kanta .

,ni muradina gida daya ne kawai nake da bukata amman tunda itama ta cin nawa zuciya gobarar datayi sanadiyyar tarwatsa min zuciyarta tarabani da abinda nafi so a rayuwata ... to tabbas nima say na nemo may kashe min wannan wutar .
ta hanyar musguna mata .

Kada ka taba karya zuciyar mace kada ka taba ruguza iyali domin cika muradinki first lov NASURULDEENI dinki babu abinda bayawa Zeenat na jin dadin rayuwar aure "tare da sanyata cikin farinciki mara misaltuwa.

burina na kyautata mata.
' ta yadda zan samar da murmurshi da farinciki a fuskarta amman firt lov ki duba kiga da irin abinda ta saka min dashi.
gata nan tsaye ki tmbyeta ban kasance may adalci agareta ba A dan ,zaman da mukayi daita .'
ahankali ya mike tsaye hawaye dake makale a idanushi sukayi nasara zubowa batare daya shiryawa hakan ba.

shin na zalinceta ko daidai da rana daya ne.
ki tmbyeta first lov amman duk da haka idan kina ganin banyi daidai ba akan dukan danayi mata to zaki iya rama mata ki hukunta ni ta duk yadda kike so.

kece kikayi sanadiyyar kawo ni duniyar nan...
ko mayar dani lahira kike son yi "ahalin yanzu ba zance miki komai ba.

wlh Deeni dinki bazai taba cewa komai ba. Hawaye yacigaba da bin fuskarta .

km ba,zan miki wata jayayya ba abisa Ga hukunta ni da zakiyi ....

,jikin Ummi yayi maseefar sanyi dangane da jin Dukabinda dan nata ya zaiyana.

,jikinta a sanyaye takaraso kusa da tillon "Dan" nata tana kuka itama tare da dora hannuwanta duka ta riko fuskarsa dashi tana kallonsa.
wani irin matsanancin tausayi tattare da kaunar "Dan' nata ne taji Ya sake nunkuwa acikin zuciyata .
Yayinda kuka mai karfi ya kufce mata" from no where kawai ta rungumeshi ajikinta tana cigaba da kuka shima kukan yake ,yarona kayi hakuri.
" kukan ya isa haka kabar kuka kayiwa umminka uziri bisa Ga zarginta gareka.
Chapter 54 · 0% Book details