← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 149

Sashe 77

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

DEENI zaune a gaban umminsa yayi shr, ya hada uban tagumi kawai yana sauraron maganar ummi ahankali tace na baka iya lokacin da naga zan iya baka akan maganar yarinyar nan Amman har yanzu ka kasa aiwatar da komai muryarta tamkar maishirin zubda kwalla tace ko so kake na mutu batare danaga kwan ka adoron duniya nan ba .
gashi yarinyar nan nablah tana da hankali da natsuwa babban abinda yakara jan hankalina gareta kyakwan tarbiyya da take da ita
ta kwanta min arai matuka fiyye da tunaninka ,dan haka kabari na dangana kaina ga iyayenta kafin mutuwata ta riske Ni .

da sauri DEENI ya zaro idanu yana girgizawa ummi kai. yayinda gumi yashiga ka karyo masa takoina ajikinsa, jin abinda umminsa tace hannuwansa duka ya daura a sama fuskarsa zuciyarsa ta taru ta hade kanta waje daya ji ya ke tamkar jinin da ruwa basa gudana ajikinsa yadda yake so ..

ahankali yaciro hanky daga aljihun gaban rigar jallabiyarsa yana goge gumin dake tsaftsafo masa .

ummi ta sake kiran sunansa DEENI ...ya amsa na'am first love idan kasan bakada abinyi da yarinyar nan kasanar dani na sallameta, taka gabanta.

Tun lokacin da ummi tafara magana deeni yake kallonta har sanda yaji tayi shr da zancenta. Jin abinda tace ne yanzu yasashi danyi murmushin gefen baki ,Wanda yafi kama Dana takaici .

muryasa kasa kasa tamkar may shirin yin rada yace ummi kina nufin auren yarinyar nan zanyi kennan?

Kwarai kuwa saboda nagaji da ganinka haka domin bansan har wani tsawon lokacin zaka dauka kafin burina yacika ba , duk sa'annin aurenka bbu wanda baida "dan" kansa, akwai mai uku mai duhu acikinsu .
tagama fadar haka ta xuba masa ido kawai tana nazarinsa sosai.
yayi shr Bai sake cewa komai ba , Amman kasan tun farko sai daka amince da yadda Na tsara kafin a kawota ?

ya daga mata kai tace to meyasa yanzu kake son min yawo da hankali kodan kaga a bukace nake da son ganin guda jininka shine ka maida zance Na wasa ?

ya hadiye abinda ya tsaya masa a makoshinsa yakamo tafin hannuta 'cikin nasa yace kiyi hakuri first love kin wuce wasa awajena duk duniya banida tamkar ki kece duniyata , na rokeki kada kiyi fushi dani.
,bacin ranki bakaramin babban tashin hankali bane atare dani.
,ya numfasa sannan yacigaba Dan girman Allah kiyi hakuri ki sallameta kawai Dan banji zan iya aurenta yarinyar nan ba.
saboda banasonta ban jin akwai halitar dana tsana kmr ta.tun zuwanta gidan first love narasa natsuwata Ni kaina ban san dalilin dayasa Na amince da zamanta a gidan nan ba.

,ummi ta hade fuska sosai tace sakar min hannu cikin sanyi jiki yasoma sakar mata hannuta kmr yadda tace .

Ummi ta xuba masa ido kawai tana dubansa Dan takaicin abinda yace , numfashi taja ta fitar sannan tace son Na lura so kake ka bata min lokaci, Amman kasan ba dole nayi maka ba tun farko kaine da kanka ka bukaci kara aure.

,km yan aiki nawa aka kawo gidan kafin ita kace basu maka ba.

da kanka ka amince da zaman yarinyar a gidan fa sannan yanzu zakace ga zance Ga mgn .amman bbu komai haka Allah yaso dani daman can bazanga jininka ina raye ba, takarasa mgnr 'tamkar mai shirin zubda sakin kwalla.

muryasa a sanyaye haba first love karkice haka ma akwai hanyoyin da dama daza mubi gurin cimma burinmu ba lallai sai ta hanyar auren yarinyar ba.
,taya za'ace kamata da matsayina da komai Na bige da auren kaskantacciya irinta . Ai da auren wlh nahakura Dana cigaba da zama da Zeenat haka koda bazamu taba haihu ba .

A fusace ummi ta katseshi ta hanyar daga masa hannu sannan tace angaya maka sbd jin dadi ne kawai , nake son kayiwa diyata kishiyar boye ,uhm kasani badan haka bane ,kai kanka kasan dalilina zanyi aikata hakan ne kawai a dalilin farincikin diyarta

Dan haka idan kai zaka iya hakura da kowani irin auren Ni bazan zauna ba ,nan gaba diyarta tashiga tashin hankali akan rashin haihuwa ba .

Ok first love yanzu abinda za'a yi ya, sunkuyar da kansa kasa sosai saboda jin kunyar abinda zai ce. cikin wata irin raunanniyyar murya yace first love me zai hana tacigaba da zama agidan a matsayin mamata kawai batare da an daura aure tsakaninmu ba.

ummi ta tsare shi da idanunta 'tana kallonsa dashi sannan tana mamaki jin furucinsa . tamkar wani mai tabin hankali . Ahankali ta dinga aiyana
kode dan nata yasoma shayeshaye ne batare da sanin ba.

"inda wani ne yatareta da wannan banzan mgnr da deeni yasanar mata da bakinshi ,to wlh da kotu ce zata rabata da duk Wanda ya fada mata hakan. Amman sai gashi, da kansa yake kokarin fayace mata ya gwammaci aikata lafin zina akan , yayi auren sunna da yarinyar .

Gumi yakaryowa ummi ta mike tsaye tana furta kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun ...'tana
ta sake kallonshi da jin takaici acikin ranta .

ganin irin kallon da umminsa ke jifanshi dashi ne yasashi shan jinin jikinsa tare da sanin ya tafka babban kuskure daya sake ya fada mata irin wannan mgnr.

Duke kansa yake a kasa yana ladamar abinda ya fadawa ummi Wanda har Ga Allah ba nufinsa shi kennan ba" shi dai yafada ne kawai Dan yarasa yadda zaiyi da ummi .

Tsawon lokaci ,ummi Na tsaye 'tana binsa da kallon mamaki kana tace wlh azim DEENI you really gave me double surprise .
sannan km bani kunya daman can abinda ka ke aikatawa da yaran mutane a gari kennan....bansani ba?

shine Dan rashin tsoron Allah yanzu kake kokarin ka fahimtar dani halin ka na boye.

Da sauri DEENI ya dago yana kallon ummi da rikitattun idanushi dasuka gama rikewa suka dawo jawur tare da matso kusa da ummi sosai, yana may girgiza mata kanshi tamkar wani karamin yaro.

Ummi tasa hannu ta dakatar dashi .. kar ka kuskura kakaraso gareni deeni fatana Allah Ya shirya min kai shirin addinin Muslinci first love Dan Allah kiyi hakuri wlh ba hali bane nida katashi kabar min dakina kawai bana son ganinka a halin yanzu.

ayau naji kunyar kasancewata uwa agareka ,deeni ban dauka haka zuciyarka ta gurbace ba mayagun laifuka ba .
Kullun nake yabonka 'cikin kawayena da dangina .
,dana kimtsasaine kamule may daraja a 'cikin al,umma ashe bansani ba yaudarar zuciyata da mutane kawai nakeyi da kyawawan halinka .

Deeni bai daddara da kashedin umminsa garesa ba .
" yacigaba da karaso inda ummi take yace dan Allah first love ki yarda dani karki min mummunar fahimta wlh bantaba aikata makamanci abinda na fada ba, baya ga mamata ta sunna. Amman Ina neman afuwarki game da abinda nace.

ummi ta sauke ajiyar zuciya Ahankali 'tana godiya ga Allah duk tasan ba halinsa bane .Dan Tasha jin yadda mutane da dama suke yabonsa akan kyawawan halinsa duk .
tasan irin kalar tarbiyar da tabawa "dan" nata.sake sauke ajiyar zuciya Tayi ,Dan tasan ba'a shedar Dan ,yau .

Ya kamo tafin hannuta wannan karon bata hanashi ba ,ya sake cewa Dan girman Allah first kiyi hakuri nayi nadamar fadar haka kinji .Ya fadi hakan yana langwabar da kansa ,alamun Tayi hakuri.

hakan da yayi ne Yasa taji tausayinsa aranta yana sonta baya son ganinta 'cikin fushi da rashin hankali Dan haka ummi tace to Shikenan naji Allah Ya sake Kare min kai .
Take , yaji hankalinsa ya kwanta yayinda jijiyoyin jikinsa da suka tsaya cak suka daina aiki na w wuncin gafi suka cigaba aiki tare da sauke ajiyar zuciya.
Sannan ya numfasa tare da juyowa yasa hannu ya dauki cup coffee ya soma kurba Ahankali ahankali .
muryar ummi yaji yanzu km sai maganar auren ko Dan gaskiya yarinyar 'tana abubuwa masu mahimmanci dazai sa a hada zuri'a daita .

A frigice DEENI yazaro idannu waje coffee daya kurba bai san lokacin daya hadiye da karfi ba.
" ai ko ya sarke shi take yafara Tari kmr ransa zai fita ummi sai faman sannu take jero masa da kyar aka samu tarin ya tsaya ya dago rikitattun idanunshi da suka gama canza kala ya saukesu bisa fuskar umminsa .

yanzu ummi bazata rabashi da zance auren yarinyar nan ba ya fadi haka a kasan ransa yayi shr can kuma yafara magana ahankali yace ummi duk wayannan ababen da kika lisafa akan yarinyar nan nifa ba ko daya da yayi min bawai na kushe zabinki bane " Amman zan aureta da zumar samun ya'ya daga gareta.
Dan a halin yanzu gara na zauna da zeenat kadai na karasa rayuwata daita , yakarasa fadar kmr zai yi kuka .

ummi ta gyra zamanta ta riko hannushi tana sauke numfashi ka amince aje ga iyayenta kennan ?
muryasa a sukwane yace uhm Na amince zan aureta Amman ba Sai kinje da kanki nemar min AUREN SIRRI ba... da kaina zandangana Ga iyayenta tunda oready kina da address din gidansu .

Yacigaba a gsky first love zan dai aureta yarinyar ne kawai badan Ina so ba Sai Dan farincikinki .
km taza zauna matsayin matata sannan ta haifa miki yaran da kike kwadayi samu daga gareta batare da ita kanta tasan da zaman nine mijinta ba Dan sanin nine mijinta zai sa naji some how..'yana gama furta haka yayi Mike yayi waje ranshi a bace zuciyarsa tamkar zata tarwatse tsabar takaici ,ummi tabi bayansa da kallo sarai taji yace a karshe sai dai bata fuskanci inda maganarsa ta dosa ba ta numfasa abinda yake nufi shiyasani damuwarta daya ce ya amince mata da auren yarinyar tunda ya amince ,mgn takare .

MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO
Chapter 77 · 0% Book details