← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 149

Sashe 143

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannu ahankali rayuwa tayi ta tafiyar masu har zuwa lokaci da watan haihuwar nablah tayi 'cikin ya fito sosai yayi tsini har abun ya Daga hankalin deeni da ummi yayinda gabadaya tunda watanta haiguwarta ya tsaya take 'cikin fargaba da tunani kusa zeenat da deeni har ma da ummi suke bata kulawa da nuna mata tsansar soyayya ..wanda kusan yanzu deeni da zeenat kullun suna dakin nablah suna kwantar mata da hankali akan ta kwantar da hankalinta zata haihuwa lfy.
wani lokaci ma har kwana suke a dakin su saka deeni a tsakiyarsu .wanda ita nablah sai dai taja gefe can tayi kwanciyarta tabarsu tana mamakin yadda zeenat gabadaya ta sauya mata yanzu ba kmr da ba .

Yau kmr koda kullun deeni yashigo dakin ya iske tsaye a gaban mirrow tana duban yadda cikinta yayi girma sosai ahankali yakaraso Inda take tsaye yana dubanta tsunganawa yayi agabanta tare da manna kunnenshi kan cikinta a tare suka kalli junansu sakamakon motsin bby suka ji .Ya dage mata gira yana nuna mata 'cikin da yatsansa lumshe shanyayyun idanunta tayi tana Daga kafafunta da kyar Dan son zuwa kan gado ya Mike tsaye jikinshi a sanyaye ya cimmata tare da riko hannuta 'cikin nashi ya zaunar daita akan gadon km har lokacin hannu nablah Na rike 'cikin nashi yana aikin murzawa .
ya tsura mata ido ahankali yana kallonta gabadaya ta sauya takoma wata kalar tausayi Ya saki hannunta .
ya kamo kafafunta ahankali ya maida bisa gado yashiga mammatsa mata sbd wani irin kumburi da sukayi .sosai take jin dadin yadda yake massaging din kafafunta ta Dan yatsuna fuska tana sake lumshe shanyayyun idanunta sorry please.. kiyi hakuri inshallahu lfy zaki haifi abinda ke cikinki dukkanin mu Muna miki addu'ar kema kina ?
Me kike cewa tayi masa banza tamkar bada ita yake ba .jin motsin turo kofa Yasa ya saki ya zame hannunshi Daga abinda yake mata
zeenat ce tashigo tana sheki da daukar hankali ta zauna a gefenshi tana yiwa nablah sannu .
Dan ita kanta yanzu takan tausayawa yarinyar da 'cikin jikinta . Murmushi tayi suka shiga hirar 'cikin jikin nablah .
ita dai nablah shr tayi bata ce dasu komai ba sai dai tana sauraransu ..wlh Allah nake naga yarinyar ta haihuwa kodan sbd mama ta abuja .
Deeni yana jinta yayi mata shr tacigaba kana ji ko my hrt idan yarinyar idan ta haifi mace fateeha za'a saka mata idan km namiji ne sunan fateehu za'a Sa .
ya juya inda take zaune tana yauki ya watsa mata wata uwar harara sbd yagane dalilinta . Nacewa hk Amman ya kanne Yace sbd me zan saka wannan sunan duk da akwai shi 'cikin alqur'ani me girma?
.Ni sunan first love dina zan saka idan macece idan km nmj ne sunan abbana zan saka .
Ta Dan yatsuna fuska tana duban 'cikin jikin nablah kana tace gsky Bai kamata kasawa wannan 'cikin sunan iyayenmu ba.
naga bby din ba daga tsatso me kyau suka fito ba ..tsaki yaja yana mata kallon tababbiya yayi kwanta can kusa da nablah tare da juya mata baya .
Kwanciya tayi itama abayansa ita dai nablah nata idanune kawai domin kusan tafi su matsuwa ta rabu da 'cikin jikinta .
km ko bbu komai tana jin dadi yadda suke bata kulawa sosai .fiyye da da .

Wata safiyar tafiya gaugawa takama deeni zuwa abuja kwana biyu zai yi ya dawo Bai so tafiyar ba Amman takama sai shi dine zai je da zai tafi tamkar ya wuce da nablah hk yaji ,sai ummi ta nuna bacin ranta sannan ya wuce ..

'cikin bacci nablah taji tamkar an tsunguleta ahankali km ta dinga jin wani irin zazzabi ciwo mara iyaka abayanta da mararrta .
ta bude idanunta wanda da kyar tamkar jira ciwon yake ta farka yace bismilla . Ta sauko Daga kan gado ahankali bata son tayi motsin mai karfi sbd ummi da zeenat su farka .
Dan yanzu tare suke kwana tashiga bayi sbd ji datayi kmr tana jin 'bayan gida

' hk ta dinga shiga toilet yakai Sau goma tana tsugunawa Amman shr yaki fitowa ta dawo ta kwanta tana jin ciwon yana ratsata ta sake jin cikinta ya cure guri tare da wata irin murdawa ta km tashi da kyar takoma toilet Daga ba sai ciwo ya tsananta ba .
Ta sake fitowa ta kifa kanta da gado ta jujjuyawa da cicciza lips hannunta daya dafe da mararta 'cikin ummi ta farka da sauri tace nablah yaya ?
Muryarta da kyar tace ummi marata zan mutu ,ummi ta duro da mugun sauri tare da tashin zeenat itama a rude ta Mike tana duban nablah dake murkususu ciwo ummi ta dafa tare da cewa kiyi addu'a nablah inshallahu bazaki mutu ba abu fa kmr wasa ciwon nakuda yakama nablah yi take cicciza lips dinta tana buga kasa tana kiran mutuwa zanyi ummi ki taimakeni wlh mutuwa zanyi ......

MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Dedicated to
HAUWA A USMAN
JIDDARH

Kainuwa association

Page 98

Ki daina furta kalmar mutuwa nan nablah addu'a kawai shine mafuta .
zeenat wacce gabadaya tagama rudewa sbd ganin halin da nablah take ciki tasoma zariya a dakin tana Kai kawo da furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.
A rude ummi tace kamamin ita zeenat mukaita dakin kasa .

Zeenat dake tsintitin acikin dakin takaraso da sauri .
Takai hannuta jikin nablah ita da ummi zasu kamata.
nablah tayi saurin girgiza kanta tana dukan Tear's da tafin hannunta .
kibari akai ki dakin kasa nablah zai fi sauki akan nan din.

uhmmmm ummi uhmmmm takasa cewa komai sai uhmmmm da murkususu ciwo .
take wani irin gumi me zafi shiga tsaftsafo mata takoina jikinta.
Jikinta ke wani irin kirma Dan azabar radadin ciwo.
ta dinga cizan lip's dinta da karfi tsabar tashin hankali .
kuka take da idanunta tana kokarin kamo hannu ummi 'aiko Allah yabata sa'a ta damke hannun ummi 'cikin nata da karfi tsiya .
nishi take hankali sbd numfashinta dake sizing yana dawo .
zeenat dibo min ruwa a cup kikawo nayi mata addu'a.

hk zeenat ta fita jikinta Na rawa biyu biyu ta dinga taka step taje takawo ummi ruwa acikin cup .

ummi takarba tayi mata addu'a tabawa nablah tasha Amman still ciwon Bai ragu ba .
Sai abunda ya Karu Na naxaba wani irin murdawa cikin nata yayi da karfi aiko ta saki wata irin razananniyar kara wanda Yasa zeenat fashewa da wani irin matsanancin kuka jikinta yacigaba da rawa .
Tana kuka tace ummi Dan girma Allah mukai yarinyar nan asibiti karfa Yar mutane ta mace mana mushiga uku Daga taimako ..

bazata mutu ba inshallahu .

Duk wani taimakon da ummi tasan anayiwa me nakuda tayiwa nablah shi Amman Sam bbu wata alamun zuwan bby wanda hkn ya nuna ummi cewa doguwar nakuda gareta.
Daman km dayawa anasamun hk wani zaga alokacin rainon ciki basashan wahala sai gurin haihuwa wasu km tun gurin daukar 'cikin suke shan wahala har zuwa haihuwa wasu ma kwata kwata basu San da wannan matsalar ba zasuyi renon ciki lafiya Haka ma haihuwar 'cikin sauki zasuyi ta .

kuka nablah keyi tana kiran mutuwa zatayi itama zeenat kuka take tana cewa ummi kinga abinda nake gudu da jin tsoro ko........
ummi kalli yadda yarinyar mutane ke shan wahala kalli yadda numfashinta keyi ni dai wlh tsoro nake ji wani abu yasameta 'cikin wani irin kuka zeenat takarashe zancenta da wallahi ummi bazan iya haihuwa ba ban zan iya ba wallahi Na hakura da haihuwar gabadaya .

'Cikin fushi ummi ta buga mata tsawa Dan Allah kiyiwa mutane shr duk kinbi kin cikawa mutane kunne ba'a haihuwa ke uwarki ta haifeki.
zakizo ki ishi mutane da surutan banza da wofi shasha kawai 'aiko kowace da yadda haihuwa take zuwa mata kamamin ita ni mukaita kasa .. .

Haka suka kama nablah zuwa dakin kasa ummi ta kwantar daita tunda tun dazu a tsugunne take a sama har garin Allah yawaye ciwo yaki ci yaki cinyewa banda murkususu ciwo bbu abinda nablah keyi da ikin kiran sunan mamata da mutuwa zatayi .
Wani daren yashigo nablah Na kan abu daya , tayi firifiri daita tayi mugun fita haiyacinta iya jigatuwa tayi shi har tasoma gajiya tana janyo numfashi da kyar tana fitawar da kyar km still ummi da zeenat Na tsaye akanta Amman haihuwa shr.
Gashi km sosai nablah ke jin wata irin azababen azaba har tasoma fezgar gashin kanta ....
ta daina gane suwaye akanta ta dawo bbu karfin komai ajikinta bakinta ya bushe sannan Yayi fari fat.. idanunta suka bushe .
hawayen dake idanunta suka kafe suka bar xuba bakinta ne kawai ke motsin ahankali tana karanto duk wata addu'ar tada iya ji taje da zata iya data fizge 'cikin jikinta ta huta da radadin azabar ciwon datake ji ...

Daren ranar bbu shiri ummi ta da zeenat suka cucibi nablah tamkar wata Yar bby suka sakata abayan mota batare da sanin kowa ummi ta zauna baya tare da nablah zeenat ta shiga gaban mota ta tayiwa motar key sai wani asibiti kudi me zaman kanshi da shegen kyau.

suna xuwa hospital doctor yana dubata yace haihuwa ce Amman km da saura Dan yanzu ma tasoma nakudar domin har lokacin jikin nablah Bai bude.
ba jin Haka Yasa zeenat sadaukarwa da mutuwa zatayi duk wannan azabar data kwana tana Sha .
Ace km yanzu taka fara nukuda ita kam tunda take arayuwarta bata taba ganin irin ciwon nan ba.
shi Yasa tasawa ranta ta nablah takare ..

Tun daren jiya jikin mahaifiyar nablah yake a tashe takasa runtsawa sakamakon gabanta daketa aikin faduwa tamkar ana buga mata guduma wanda batasan dalilin faruwar Hakan ba Dan Haka ta Mike jikinta a sanyaye Daga kwanciyar datayi tazo ta dauki buta tayi alwala tashiga jero nafiloli da addu'oi neman tsari .
Chapter 143 · 0% Book details