← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 149

Sashe 53

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Ahankali cikin sanyi jiki ya , mike tsaye ya suke hannuwansa duka cikin aljihun wandonsa yasoma zariya Yana zagaye cikin office din.
'sannan ' ya dawo ya zauna a gefen tablet dinsa yana jinjina girman alamarin duk ilahirin jikinsa sunyi masa mugun sanyi .'ahankali ya sake mikewa ya koma kan kujerarsa ya zauna yana son yacigaba da aikinsa idanushi suka sauka akan dan karamin fream din dake ajiye akan table.
ya zubawa umminsa ido kawai yana kallonta shi kansa ya amince tun ba yanzu ba umminsa na matukar son shi da kaunarsa fiyye da komai.
" shima km haka yake matukar sonta tamkar rayuwarsa.
" duk duniya ita kadai gareshi 'ahankali ya kai hannunshi ya dauki karamin fream din yana cigaba da kallon umminsa" yayi matukar kewarta " kusan kwana biyu Keenan rabonshi da sanyata acikin idanunshi wanda km hakan ta faru ne a sanadiyyar Zeenat ,bancin haka yasan zuwa yanzu da tuni umminsa ta nemishi da kanta.

runtse idanushin yayi sosai Yana jin yadda kaunar mahaifiyarsa ke ratsa zuciya da gangar jikinsa "tsawon lokaci idanunshi na runtse sannan ya budesu fes yana sake kallon umminsa tare da sake jin haushi da takaicin Zeenat a ranshi.

Take yaji zuciyarsa tasoma amince masa daya dauki shawarar da manir yabashi Kodan samun natsuwasa da km kuntatawa zuciyar Zeenat din .
sannu 'ahankali ya maida hoton Umminsa ma,ajinsa yacigaba da abinda ke gabansa .

Gabadaya parlour,n big Dady cike yake da manya daga cikin en'uwa na family muhd bello khaliyal.

Big Dady ya kalli gefen da Zeenat take zaune rakube tare da sunkuyar da kanta kasa tana xubda hawaye .
" Yace yanzu Zeenat kin kyauta kennan da abinda kikayi ?
mezakicewa mahalincinki idan kin koma gareshi ' ashe daman karamin tunani gareki bansani ba "Zeenat dai kanta na kasa tana cigaba da zubda hawayen nadama ta kasa cewa komai big Dady ya girgiza kanshi kawai 'sannan Ya maida kallonsa ga deeni .

Kai km kuturu sarkin zuciya" Ai ba a yanke hukunci cikin fushi kwata kwata bamu ji dadin hukuncin da , son ranka da kayi ba .
,domin kuwa har zuwa yanzu a karkashin ikonmu kake, yakamata ace ka kawo maganar gabamu kafin kazarta da komai .

Dan haka muma zamu nuna maka har yanzu kai din a karkashin mu kake km abin ikonmu.

Big dady ya sake juyowa inda Zeenat take " ke... saki nawa ya rubuta miki?
cikin kuka muryata na rawa tace nima ban sani ba .

Ina takardar sakin take 'ahankali ta tura hannuta ta zaro farar takardar daga gefen zaninta ta Mika masa .

Big Daddy ya karba ya bude Yana dubawa yaga ashema saki daya ne ,take yaji wata natsuwa da kwanciyar hankali sun shige shi hamdala yayiwa Allah sannan ya sake duban deeni .
yanzu me yakamata kayi tunda saki daya ne?
Bbu tsoro ko shakka ,deeni Yace bbu wani abu da zanyi da wuce kawai Allah ya hada kowa da rabonsa .

Wlh wlh baka isa ba say kamayar daita sautin muryar inna ta karade dakin .
jikata ba zata zama bazawara ba' byn kagama moremata jiki ba eheeeee.
kaji min yaro da muguwar mugunta da bakar zuciya kmr irin ta firauna.
To ,wlh baka isa ba ,ke km fadeela kina zaune kin yi shr kina jin abinda wannan gatalallen "dan" naki yake fada .

Ita dai Ummi shr kawai tayi Tana kallon tsaitin da deeni 'ke zaune dan batasan abinda zatace ba ,km koma tana da abin cewa bazata iya da jarabar inna ba .

Inna tacigaba ko baka maidaita jikata ba zata samu wanda yafi kyau da kudi da komai "amman wlh tunda kagama moremata jiki Sai ka maidaita gidanka.
ban da ma kaddarar aure mai jikata zatayi da kai tsami gaye da kai da tsayi awa bishiya .

abin dariya abin takaici a wulakanci deeni ya dinga kallon inna Yana jin wani irin zafi a kirjinsa tamkar zuciyarsa zata buga.

a zafafe Yace to baza'a maidaita ba say kiyi duk abinda zakiyi.

,ni kake cewa bazaka maidaita ba , zubairu kana jinshi ko to wlh bada ni kake ba da wannan ta zaune kake tashiga nuna Ummi da hannu ,mara kunya yaro kawai may dan karan taurin kai awa na mutane farko .

Deeni ya bude baki big dady ya katse shi ta hanyar buga masa tsawa.
" mahaifiyar tamu kake kokarin yin sa,insa daita ,kar ka sake na sake jin bakin ka kaji dai nagaya maka .

Dan Allah inna kiyi hakuri Ya isa haka "

Inna tace bai isa ba zubairu , nace bai isa ba kai ya kalli tsabar idanunka ya gayamaka haka ko yagawa uwarsa haka ,say ni daya raina ko dan haka ko yamayar daita ko km wlh koto ce zata rabamu dashi tare da fashewa da wani mugun kuka ,wlh Allah yaisa tsakaninmu dakai deeni bamu taba yafe maka ba .fk yatashi ya mike dan takaici inna ya bar parlour,n .

Da kyar big Dady yasamu ya rarrashi inna . ranshi a bace Yace yanzu yanzu ka maida matarka inji cewar big dady .

deeni Yayi shr Yana kallonsa Yana huci .
inna tace bakaji magana ake maka ba" kinbabbe kawai Sai faman huci kake kmr ,zaka hadiye mutane.
" deeni ya tsareta da rikitattun idanushin kawai zafi zuciyarsa da kirjinsa suke masa .haushi da takaicin inna suka taru suka mamaye masa zuciya.

inna tace daina kallona da wayan nan mugayen idanun naka masu kama dana mage , munafiki kawai.

Zeenat ce Sai Sai ta koma gidanka ko kaki ko kaso uhmmmm.
zeenat dai kanta na kasa Sai risgar kuka take tana addu'ar aranta kar Allah Yasa deeni Yace ya maidata.
duk da tsananin son da take masa bazata iya juri zama dashi ba cikin wannan situation din ba.
yayinda hawaye ke cigaba da bin kuncinta .

Wai wasa ake dakai ne ka tsai da mutane kana bata mana lokacin kowaye sa,anka anan inji wani kanin mahaifin deeni.
shi kuwa big dady tunda yayi maganar karshe bai sake cewa komai ba Sai idanu daya zuwaba deeni Yana kallonsa ko kifta ido baiyi .

'Ahankali deeni yake kallon duk ilahirin wayan dake zaune a parlour kaf dinsu iyayensa ne idan aka dauke fk wanda shima sako yashigo kawowa ya iske ana maganar ,'ahankali yacigaba da kallonsu idanunshi suka fada cikin na umminsa wacce gabadaya tazamo kalar tausayi, wasu abubuwa yake hangowa daga cikin idannun umminsa masu kama da rarrashi da ban hakuri .wanda suke nine a bukace take da son ya aikata abinda akace masa Yayi.

,ahakali ya mai da idanunshi kasa tare da sauke ajiyar zuciya. muryasa can kasa kasa Yace na ...mai daita...

Inna taja tsaki tare da Mikewa tsaye munafiki kawai ' daman can kana sonta iskanci ne kawai irin na mai shayi ya tsaida uwarsa ya tsai fatan shayi , tsami gaye kawai ..
Deeni ya dago rikitattun idanushin suka hada ido da Ummi tayi masa gargadi da idanunta alamun kar ya sake Yace Komai

Bye bye bye until after sallah missing u guys

MMN SUDAIS CE
[6/29, 7:51 AM] 0mmer Farouk: 💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

*Assalamu alaikum warahmatul Allah inawa dinbin masoya wannan littafin barka da sallah da fatan kunyi sallah lfy Allah ya karbi Ibadunmu da mukayu cikin Ramadan Allah Yasa muna cikin bayin da Allah ya, enta daga wuta zuwa jannatul firdaus Ameen ,kmr yadda nace zan cigaba da type din wannan labarin nawa byn sallah, to a yau ne alkawari Allah yacika Allah ya nuna mana lokaci ,hakika may hankali da tunani ne kadai zai Gane yadda duniya ke gudu, Allah Yasa mudace yabamu ikon cikawa da kyau da imani ,km Allah yabamu ikon aikata ayyukan alkhari*

Page 54

'Ahankali Deeni ya dauke rikitattun idanushin daga cikin idanun umminsa ya maidasu kan inna dake tsaye tana fama , babatu da sambatu iri iri 'km duk cikin taron mutane dake zaune a parlour bbu wanda yayi yunkurin dakatar daita daga maganganu da take .

zuciyar Deeni cinkushe da haushi hade da takaicin inna" bakinciki ganinta ke sake nunkuwa a kasan ransa yayinda yashiga da zuciyarsa wani irin zafi da suya zuciyarsa ke yi.
" so yake ya murje idanunshi Tare da cire kunyar jamar dake zaune a gurin, sannan ya zage kunjinsa ya zabga mata rashin mutunci fiyye da irin wanda ta iya .
,amman Ina...tuni idanun umminsa dake yawo a kansa" yasa ya kasa aiwatar da komai sakamakon gargadin dinsa datake ta hanyar kwayar idanunta .

dan haka daya rasa yadda zaiyi ya fanshe tarin wulakancin inna gareshi,sai kawai ya shiga aikawa inna da wani irin mugun Kallo may hade da harara .

Wanda yasa ,ita kanta inna dake tsaye har lokacin sake jin haushin DEENI da takaicin irin kallon kaskancin da wulakancin dayake aiko mata dashi .

"Km hakan yayi sanadiyyar kara hassalata , dan haka a tsawace Tace ni daina kallona ,ka wani tsareni da wa'yan nan mugayen idanun naka masu kama dana mage , kana aikomin da kallon wulakancin to bada ni kake da wannan uwartaka ta zaune kake... ehee.. takarasa fadar haka tana may jan mugun tsaki a fili tare da soma kokari kamo hannun Zeenat .

Ke tashi mu tafi , can sashina ko kya samu ki maida jikinki ki murmure daga wannan bakar ramar da kikayi " inna tasoma kokarin mikar daita Zeenat tsaye .
Yayinda Zeenat din km taki mikewa Sai ma sake cure jikinta da tayi gurin guda alamun babu inda zata .

,au bazaki mike mu tafi can gurina ba ,kinfi son ki zauna inda za'a dinga miki izaya da tsotse miki jinin jiki.
Dan zama da wannan mugun azalumin kadai ya,isa yasa jinin jikinki ya kafe batare kowa yasani ba "ni tashi mutafi .

,juyin duniya nan inna tayi da Zeenat kan ta tashi su tafi can part dinta " amman kememe Zeenat taki tashi .
ganin haka yasa inna sake tunzura, ta cigaba da tsayuwarta tare da surfa masu maseefa iri iri km har lokacin bbu wanda yaiya cewa komai

big dady ne "ya dan dago idanushi yana duban sashin da inna ke tsaye Tana surfa maseefa ,ya xuba mata kawai domin shi kansa big Dady rasa me zai cewa inna yayi...
Chapter 53 · 0% Book details