← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 149

Sashe 49

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mtssss yaja tsaki may zanyi da jininki Zeenat wlh wlh kinji na rantse bana sha'awar sake zuba Spam din a cikin wannan jikin naki.

ke gubace yanzu a wajena babu wani amfani da zaki min ya sake yin ball daita ta bugi bango dakin ta dawo kasa ta baje tana air....
Air...., Dan sautin kukanta ma kin fitowa yayi Dan azaba .

Kadan kika Gani sauran wancen useless din sumy ko take da suna.

yana gama fadar haka ya juya fuuuuuu a fusace yabar dakin ya nufi nashi.

, gabadaya komai ya taru ya cakudemasa waje daya ji yake tamkar duniya ta tsaya masa cak ta daina jujjuyawa masa yadda yake so.....

jiya da yau duk sun zo masa da abubuwa masu muni da daci da bakanta zuciya .

Cike da bacin rai yasoma shirya jikinsa cikin kayan aikinsa .
Komai nashi ya sake canzawa " hatta da kyakkyawar fuskarsa ta sake daukar sauyi daban fiyye da shekaru 20 da suka wuce wato shekarun kuruciyarsa abubuwa daya suka dinga zuwa masa akan matakin daya kamata ya dauka akan aurensa da Zeenat.
,tunani iri iri ya dinga yi har yagama shirya kansa ya fito tsaf Sai kamshi yake zubawa amman kyakkyawan fuskarsa a daureta take tamau ya kulle koina gidan sannan yakama Gabansa .

Tafi 2hr kwance a gurin daya barta wanda da kyar take iya motsa gangar jikinta .

Tana nan kwance har ta soma jin Kira sallar la'asar daga masallacin dake cikin gidan.

da kyar da bin bango tasamu ta Mike tashiga bayi tana kuka tana girgiza kai shikennan tarasa deeni tarasa cikin jikinta tarasa soyayyasa data kwallafawa rai shikennan tarasa komai nata .
tasan ko Ummi taji abinda tayi zata tsaneta ta juya mata baya.

wayyo ni Zeenat na cuci kaina da kaina na cuci rayuwata wazan kama meye rudeni dayasa nakasa fahimtar komai gashi yau ban kasance cikin jin dadi a gidan mijina ba.... .sharrrrrrrr hawaye yashigo ambaliya a kuncinta.

Kuka take sosai tana nadamar abinda tayiwa kanta .
"tare da addu'ar Allah huci zuciyar mijin nata ,ya sake sauto mata hankalinsa gareta ,ruwa zafi tasamu ta gasa gabobbin jikinta dashi .

Kusan 30 minti ta dauka tana treating din jikinta a bayi
Ba laifi ta Dan ji dama dama ta ragen jin zugin da jikinta ke mata.sai cinyarta inda deeni ya watsa mata ruwan zafi waje yatashi yayi shashin baki baki.
" cikin sanyi jiki ta fito daga bathroom ta tsaya gaban mirrow tana karewa kanta kallon yadda deeni yamaida mata halitar jikinta.
tamkar ba nata ba hawayen masu dumi da ciwo suka sake silalo mata , batayi kokarin maidasu ba ta barsu suna cigaba da bin kuncinta.

ahankali tace Allah sarki sumy a she dai sai kinshiga matsala a sanadiyata duk da kin guji abinda zai faru akaro na biyu , amman duk da haka baki tsira ba Dan nasan deeni bazai barki ba kema .

Doguwar rigar ta sanyawa jikinta tashiga neman wayarta a dakin Dan takira Ummi tazo ta dauketa Amman sama ko kasa ta nema wayarta tarasa.

ta zauna jugun a gefen gadonta tare zuba uban tagumi tana tunanin shikennan ni km kiyamata, ta tsaya kennan a gidan nan tunda har yanzu bbu wanda yasan halin danake ciki a family .

gabadaya zaman gidan ya isheta ya gudireta tamkar tana gidan prison haka ta dinga ji hanyar fita kawai take nema daga gidan domin ta tsira da rayuwata datayi mata saura Amman bbu ta inda ,zata bi ta fice daga gidan .

10 shap yashigo gidan tana zaune cikin damuwa tajiyo motsin. shigowar motarsa ta Mike tsaye 'ahankali tana hangeshi ta Window dakinta hawayen son shi da tausanyi shi ne suka shiga zubo mata.
ita kanta tasan bata kyauta masa ba.
Tasan ta cutar dashi km ta cancanci hukunci fiyye da haka daga gareshi. Har ya fito ya rufe motarsa idanunta nakasan tana kallonsa tana jin yadda kaunarsa ke sake narkar mata da zuciya tare da mamaye mata ruhi da gangar jikinta .

Ganin yasoma kokarin bude kofar shigowa cikin ainihin parlour,n gidan ne yasa tayi saurin barin . jikin window take km jikinta ya dauki zafi da kirma dan sai lokacin taji wani mugun tsoro ya shigeta.
kmr taje ta rufe kofarta taji amman sam tsoro da fargaban abinda zai faru ya hanata motsawa daga inda take , tana nan tsaye har yashigo dakin nata .

Bakinta na rawa rawa da shakakkiyar muryata tashiga yi masa sannu da zuwa.
hood it .....Ya katseta sannu da zuwan ubanki zaki min.
Wlh kika sake min magana wanda bani ne na bukaci hakan ba , say sabauta miki jiki hariznablenimal kawai ,zo.... nan yana mata nuni da yatsansa.
taki motsawa sai ma cigaba da kirma da jikinta yake .

kunneki na ciwo ne baki abinda nace ba
....da kyar take iya daga kafafunta zuwa gareshi kafin ta takaraso ya fizgota da karfi ya watsa mata wasu ta gwayen mari tayi kara amman bbbu murya jiyo sautinta.

Dan ubanki har wani wanka kika samu damar yi da canza kaya ubanwa yace kiyi wanka ya shake mata wuya ,yanzu kam gabadaya muryarta tagama shekewa kwata kwata bbu bakin da muryar bada hakuri sai daya gaji ya hantsilata kan bed sannan yayi kusa daita ya daura kafarsa daya kan abin gadonta dayar kafar na kasa ya zuba mata rikitattun idanushin kawai yana kallonta shi kansa yasan zuwa yanzu ta horo iya horowa amman zai barta ba ko kaita gida ba tukun sai ya tabbatar daya gana mata azaba mafi radadi .

Yace ,oya gayamin full address din wacce Yar iskar abokiyar iskancinki .

Tasoma magana muryata bata fita ya daka mata tsawa ki bude baki kimin magana kafin na kashekeki.
ta diro kasa da sauri ta bude doron din mirrow dinta ta dauki Biro da white paper da sauri tashiga rubuta address din sumy ta miko masa .

a wulakance ya karba yana yatsuna fuska yana gama dubawa yayyaga paper ya watsamata a fuska ya Ciro wayarta daga aljihun bayan wandonsa yashiga gallery inda yaga hotuna wanda bana family dinsu bane..
yace ta nuna masa wace samy ta karbi wayar jikinta na rawa tare da fashewa da kuka .tashiga
ta dubo masa hoton tare da ta Mika masa wayar .
ya masa yana duba pis din daman km ita din yafi zargi tsarki yaja sannan yabar dakin.

Yau kmr jiya tana kwance a dakinta tana bacci ta kamkame jikinta guri daya " sbd tsoron abinda zai faru.
taji an take mata kafafunta da karfi tsiya wani azababen zafi taji wanda yasa pent dinta ya jike da danshin fitsari sannan ya watsa mata ruwa may mugun tsanyi a jikinta. Da sauri ta mike zaune tana kukan azaba tare da rike masa kafafunsa yayinda hawayen tausayin kanta , yacigaba da zuba daga idanunta, takasa ce masa komai ,sai kallonsa da ta dinga yi da kumburarun idanunta dake cike da hawaye tunda ya hanata yimishi magana .

Kimin shr banason sake jin motsin kukanki waya baki damar yin bacci Ai kin gama bacci acikin gidan ,tunda baki nemi zaman lfy dani ba .

kuka ta saki sosai tana girgiza masa kanta sai daya gaji dan kansa sannan ya daga mata kafafunta wanda taji tamkar ammata garafa ne km kitashi kije ki hada min breakfast .

Sallah Ta fara yi sannan taje ta hada masa breakfast dan yanzu tsoransa ya sake nunkuwa a zuciyarta fiyye da da.

Kwantar da hankalinta tayi ta shirya masa abinci a natse takai masa ,sai da taga yasoma ci sannan ta samu natsuwa a zuciyarta .

Wasa wasa sai da deeni ya dauki sama da kwana biyar yana ganawa Zeenat azaba iri iri km kullum da kalar azabar dayake tashinta dashi .

Iya azabtuwa Zeenat ta shashi a gurin oga deeni dan kallo daya zaka mata taba mugun tausayi tayi baki ta rame gabadaya ta fita haiyacinta ko Matsin shi taji gabanta Yashiga faduwa kennan har sai yazo ya gana mata azaba ,take samun natsuwa .ita kanta sai data Rena kanta da irin muguwar ramar datayi ko kallon mirrow bata son yi .

Deeni ya baza yaransa wanda suma sojoji ne wajen neman sumy km Allah ya basu sa'a Dan basu sha wani wahala gurin kamota ba saboda pics dinta da oga yabasu .

Dan suna shiga unguwar daita suka fara cin karo tayowa wata kawarta rakiya" gurin dawowarta ne suka cafki shegiya suka danna a mota.

Kai tsaye inda oga deeni ya umarcesu dasu kaita sukayi .
"tun a cikin motar daya daga cikin yaran deeni may suna tope yakirasa a waya .

Byn Deeni ya daukar wayar ne " tope yagaida shi wannan yace sir gatafa mun kamota.

Deeni dake zaune office Yace ok ku karasata kawai ganin nan zuwa anjima amman ku soma ladabtar min daita kafin nazo tope ya amsa da ok sir angama .

MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Page 51

Deeni dake zaune a office dinshi Yace ok ku karasa daita kawai Gani nan zuwa anjima amman ku soma ladabtar min daita kafin nazo tope ya amsa da ok sir .

Rikecewa sumy tayi Hankalinta yayi matukar mugun tashi .
dajin wayar da wanda taji ankira da tope yayi.
Dan duk taji abinda Suka Tautauna a wayar .
Dan a handsfree tope ya sata "wanda tarasa kowaye wanda Yace a wuce daita gashi nan zuwa .

Haka kawai taji gabanta ya daki uku uku ya fadi rassss.

jikinta yasoma rawa rawa lokaci daya wani irin matsanancin tsoro yashigeta.
" wanda tunda take iya tsawon rayuwarta bata taba tsintar kanta cikin yanayi tsoro haka ba .

Sosai tasoma kuka tana tunanin laifinta Ga wa en nan bayin Allah .

Ade dake ta gefenta ya Ciro Yar karamar bindigarsa pistu ya mannata a daidai gefen cikinta .

muryasa kwasashe Yace u better keep ur mouth short before I skater u into pieces .

Cak kukanta ya tsaya amman gabadaya jikinta bai daina kirma ba .

Har Suka kawo omole new side kuka take shape shape bbu sauti .

Daidai wani dankareren tsararen gida may matukar kyau da tsari wanda kallo daya zaka masa kasan anyi barin kudi akansa , sukaja Suka tsaya tare da yin hon.
Chapter 49 · 0% Book details