← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 149

Sashe 52

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tana gama jin ta mike tsaye Tana jan tsaki mtssss tare da tacigaba da zagin deeni .
Dan ta zubar da cikinka din baza shine zaka mata irin wannan duka , mara mutunci kawai wlh bazan yarda ba ,

Ran deeni ya sake mugun baci " dan haka a hassale Yace da bazaki yarda ba sai kizo ki rama mata tunda dukan dana mata yayi miki ,zafi .

, zubairu kana jina da wanna gantalalan yaro ko.
Wlh koban rama mata ba ,zamu barkar da Allah yayi mata bakar sakayar da bata da magani .

wlh ni karki dameni dan zan iya huce haushina akanki inji cewar deeni .

zaka dake ni nima ta matso gabansa tana zaka dakeni tantirin mara kunya kawai may dan banzar mugun halin tsiya .

Sai da Big dady ya dakawa deeni tsawa sannan yayi shr ya rabu daita ,tana zuba maseefa iri iri.

deeni ya mike da kyar yana kallon big dady miryasa can kasa Yace sai da safe ni zan wuce ganin haka yasa shima fk ya mike yana mara masa baya .

Sai huci inna take maza ka dawo nan ka kawo min takardar sakin jikata dan wlh bazata km cigaba da zama dakai ba mugu azalumi kawai.

Deeni dake shirin barin parlour,Yace tun yaushe aikin gama yagama Ai ko baki ce ba nima bazan km ,zama daita ba.

,ta sake kurma kururuwa ihu yanzu kasar min jika byn kagama moremata jiki to Allah ya isa wlh km sai kaga karshenka .

shi dai Bai km cemata komai ba ya karasa ficewa daga dakin .

Daidai kofar gidan fk suka ja suka tsaya faruk Yace gaskiya aboki banji dadin sakin dakawa Zeenat ba.
dan kasan Ummi zatashiga damuwa ,akan haka fk sakin Zeenat danayi shine yafi alkhari da zaman lfy atsakaninmu ,dana dinga mata ciki Tana zubarwa a rariya gara nabarta kawai .
,fk Yaceto yanzu haka zaka cigaba da ?

,deeni ya daga masa kafada tare cewa uhmmmm zaman haka zai fiyye da dai zama da Zeenat.
nan dai fk yayita bashi shawara akan yayi hakuri ya maidaita tunda saki daya yayi mata , Yace Nagode sosai aboki zan duba maganar idan hakan zai yiwu sai zuwa gobe kennan tare da yiwa junanasu.sallama.

Karfe tara daidai deeni yashiga gidansa ya haura sama ,a sanyaye ya bude kofar dakinsa yashiga yasoma cire shirt din jikinsa da dogon wando ya rage daga shi sai singlet da boxes.
yayi kwanciyasa kan bed dinshi tare da runtse idanushin yana jin zafin da radadin abinda kakar Zeenat tayi masa.

Ga tashin hankali daya baro umminsa ciki yarasa meke masa dadi a rayuwarsa .

Gabadaya komai ya dagule masa waje daya mafuta kawai yake nema.
lokaci may tsawo ya dauka kwance yana tunani abinda yaka mata yayi batare da bacci ya dauke bashi ba .

MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Assalamu alaikum warahmatul Allah wabakatuhu🤝🤝🤝🤝🤝

*Makaranta auren sirri ina may matukar baku hakuri domin zan dakata da novel din auren sirri anan har sai allahu ya kaimu byn sallah inshaallahu zan daura daga inda na tsaya inawa daukacin masoya wannan litattafin nawa murna da shiga wannan watan mai alfarma da albarka Allah yasadamu da rahma da alkharin dake cikin wata ameen ya Allah*

*Tunatarwa Yana da kyau a garemu da muji tsoron Allah mu gyara halayemu mu shiga cikin watan Ramadan ina masu aminta da tasbihi Ga Allah ,lokacin Ramadan Allah na daure shidanu sannan km ana bude kofofin aljanna a kulle nata sbd haka in muna shaidanci to mune shaidanun kanmu sannan yakamata ace mun tsarawa kanmu lokacin ibada acikin wannan wata may zuwa wato watan ramadan zuciyoyinmu suke yaudaramu da kanmu muke yaudarar kanmu Allah ma daukakin sarki yace yaayyullazina amanu,to anan Allah Yana magana ne akan mutane wa,enda kukayi imani da Allah, mu kau da kasala da lalaci mu rage bacci hira banza da surutun da bai dace ba da sauransu, domin mu samu lokacin ibadarmu Sosai duk inda Allah yace yaayyuhan nasu to Allah Yana nufin dukkan mutane walau musulimi ko kafiri azumi ibada ce da Allah kadai yasan ladansa Ga duk wanda yaji tsoronsa ya km yi shi da iklasi azumi ibadace may falala Lada wanda Allah kadai yasani ,to kunga ashe muminai suke bautar Allah da gaskiya idan kinyi sallah da sauran ibadodi domin mutane su Gani suce kinyi to azumi fa na Allah ne shi Yana kallonki inma kinyi ko bakiyi bakiyi duk ibadar da mukeyi don ace muyi ko wani abu mukeyin riya don wasu suce munyi to musani muna afkawa cikin babbar kuskure ne munayi riya bamu da Lada ko kadan riya na daga cikin manya manya kanairai zunaibai don haka mukiyaye muji tsoron Allah karmu bata ayyukanmu na alkhari da da riya .musa hankali da kyau watanni goma shadaya muna cin muna sha ,muna yin duk abinda ran keso ,Sai wata daya ne zai gagaremu mu tsaya mu azumce shi dayin ibadu acikinsa wannan shine watan da akwai daren wanda yake da tarin falala ,mai tarin yawa muyi kokari mu riski wannan dare muna masu kiyamullai, allah yasa mu dace da wannan daren ameen summa ameen*🤝🤝🤝🤝🤝

Page 53

A ranar sam deeni kasa bacci yayi saboda tsantsar fargaba da tunanin da yake ciki akan hukuncin da umminsa zata zarta akansa.
" dan Bai san abinda zai faru ba akan sakin da yayiwa Zeenat. farinciki ko akasin haka.

ganin kwata kwata bacci yaki samuwa agareshi ne Yasa ya mike 'ahankali ya tashi tsaye yashige bathroom , yayi alwala yazo yasoma jero nafiloli yana may kaiwa Allah kukansa .
, koda ya idar sallah ma guri yasamu yayi kwanciyasa.
' Sai daf da sallar asuba yasamu bacci ya daukeshi kwata kwata bacci daya samu baifi na awa daya ba ya sake mikewa yayi alwalar sallar asuba yana zaune yana lazami har garin Allah yawaye .

Misalin karfe bakwai daidai yayi wanka sbd yana son fita da wuri sbd matsalar hoidop din da ake fama dashi acikin garin Lagos sakamakon gyare gyaren titi da ake .

yana tsaye agaban mirrow yana shirin zuwa office amman gabadaya tunani umminsa ya addabe zuciyarsa duk da ruhinsa .
"ranshi a dagule yake shirya jikinsa sbd yasan umminsa nacan na fushi dashi Yana wannan tunanin har yagama shirinsa tsab .

Zaune yake a cikin tafkeken office dinsa may zagaye da makeken tablet cike da tarin file files da takardu.

system din dake gabanshi yana aikin tura sakwanni ne" ya dan ture gefe tare da afkawa cikin duniyar tunani abinda Zeenat tayi masa .

hakika Bai san yadda zaiyi da damuwar data kunsa masa ba.
, Sam yakasa hakura da abinda tayi masa Sosai yake jin zafinta har cikin zuciyarsa tsawon lokaci Yana zaune yayi zurfi cikin tunanin .

Wani abokin aikinsa manir ne yayi kundin balar shigowa cikin office din" byn nouking din da yayi tayi yaji shr ba respond .

Zaune manir ya samu deeni yayi shr yana duniyar tunani' kusan Kira biyu yayi masa" amman ko daya deeni bai san yana yi ba Sai ana uku ne yayi firgigib ya ankara '
da an shigo office din.

A wayance ya waske . Naunauyen ajiyar zuciya ya saki tare maida hankalisa sosai kan manir .

'Ahankali manir yasamu gurin ya zauna akan daya daga cikin kujeru guda 2 dake ajiye dan zaman baki .
Shr shima Yayi ya zubawa deeni ido kawai yana kallonsa tare da nazarinsa "tsawon lokaci suna kallon junansu batare da kowannesu Yayi tunanin yacewa dan'uwansa komai ba .

Har Sai da manir yayi karfin halin cewa .

wato har yanzu dai matsalar Zeenat din ce taki ci taki ciyenwa?

dayake yasan komai game da abinda ya faru.

a ganina zuwa yanzu yakamata ace kasawa ranka salama akan maganar yarinyar nan . kayi hakuri kabarwa Allah komai .

deeni da Yayi shr kawai tare da kamo lip's dinshi na kasa yana cizawa 'ahankali'ahankali shi kadai yasan yadda yake jin zuciyarsa da gangar jikinsa 'ahankali muryarsa a sanyaye yace uhmmmm duk maganarta na damuna.
" amman nafi tunanin halin da first lov zata shiga ne kasan yadda Zeenat din take a gurinta .

Manir yayi shr ya jima yana jinjina girman alamarin sannan ya numfasa yace deeni Ina kan hanyata yanzu ta zuwa Ilorin daman sallama nazo muyi .

bbu wani hanzari dazan iya maka akan maganar ka matarka daya wuce..
Sai km ya dan mike daga kan kujerar dayake zaune ya rankwafa gefen deeni tare da kai bakinsa daidai tsaitin kunnen deeni, zo kaji wata magana.
,kusan minti biyu manir yayi Yana tsarawa deeni zance sannan ya dauke bakinsa yakoma gurin zamansa.
" a razanane deeni yake bin manir din da wani irin matsanancin kallon tare da mamakin abinda Yace.
manir yacigaba abinda kawai zakayi kennan karaba kanka da wannan damuwar dake damunka kada zuciyarka ta samu matsala .

'Ahankali deeni ya shiga girgiza kansa yana kallon manir batare da ya iya ce masa komai ba .

haka kawai shine maganin matsalarka Amman ka zauna kayi tunanin shawarata da kyau inji cewar manir .

Da kyar deeni ya iya bude bakinsa da Yayi masa nauyi Yace anya kuwa manir zan iya abinda ka bukaceni da nayi kuwa?
" manir Yace zaka iya mana Sai dai idan baka gadama ba.
deeni ya sake girgiza kansa ,kai bazan iya ba wlh ....

Manir ya mike tsaye yana mikowa deeni hannunsa ' bbu dole fa cikin shawarata kaduba kagani idan zaka iya kawai kayi "ni zan wuce Sai na dawo , jikin deeni a sanyaye shima ya mikowa manir hannu sukayi musabaha .

manir ya wuce Yana cewa malam katashi tsaye kawai kayi abinda ya dace ba kullum tunani ba .

Deeni ya jima zaune yana saka da warwara akan zance da manir yayi masa wanda gaf maganar take da tarwatsa masa zuciya.
Chapter 52 · 0% Book details