← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 149

Sashe 24

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari ma sukusuku ta tashi tamkar wace batada lfy ta rame sosai " idanunta a kumbure kallo daya Ummi tayi mata ,ta Gane kuka tayi .
km daman tana lura daita jiya bawani baccin kirki tayi ba .
taji wani irin tausayinta ya tsarga mata har cikin zuciyarta "dan tasan tunda ta kwallafawa ranta auren DEENi , ta hadu da babban aiki .
km sai ta hadu da abinda yafi haka.a addu'a dai zata cigaba dayi musu Allah ya kauda fitana atsakaninsu.

Ahankali Ummi takira sunanta ...ta dago da kumburarun idanunta tana kallon Ummi dasu batare da tace mata komai ba byn gaisuwar datayi mata .
,Ummi tace meke damunki ne zeenat naga duk idanunki duk sun kunbura" sai naga ma kmr kuka kikayi .

Zeenat ta danyi murmushi dole sannan tace kai Ummi bbu komai fa, idanuna kemin ciwo ,km jiya da ciwon kai na kwana .
ta fadi hakan da hankalin Ummi ya kwanta .

Ummi tayi shr kusan minti goma tana kallonta sai da tagama nazarinta tsab sannan ta numfasa tace shikennan Allah ya sawake kinsha magani ?
Zeenat ta girgiza kai kawai.
Ummi tace maza ki tashi kije daki ki dauko magani kisha.
a sanyaye ta mike jikinta babu kwari tace to ...
tare da shigewa kitchen dan bataji zata iya shan wani magani a halin datake ciki yanzu ,dan tasan ko tasha bazai taba yi mata maganin damuwarta.

kusan duk dare sai bacci ya katse mata sakamakon tunanin DEENI da hali ko in kula da yake nuna mata .
, shi sam mutun ne da babu ruwanshi da wani damuwa harakar gabansa kawai yakeyi hankalinsa kwance .

tayi shr cikin zullumi irin zaman da zatayi da DEENi,a zahirin ce tagama duk wani tunani da zatayi akansa ,amman sam bata hango wani jin dadi ko kulawa da za samu aurenta dashi ba .

Sai yanzun take gane manufar Ummi" tana guje mata wahala ne yayinda ita km ta kasa fahimtar hska . gashi yanzu lokaci ya kure mata bata da daman tace ta fasa .

Misalin karfe takwas na dare .
kwance take a parlour kan doguwar kujerar three site .
hannuta rike da wayar Ummi ta juyata idanunta kuru akan TV .zaka dauka ko kallo take .
amman a hakikanin gaskiya kallo daya zaka mata ka gane Gabadaya hankali bai gurin TV .
tana can ta lula cikin duniyar tunani tunani .

, kamshin turarensa ne ya ankarar daita ,take tayi firgigib da dawo duniyar kasa dan tasan tunda Tajiyo kamshinsa yana kusa kennan dan haka ahankali ta dan juyo tsaitin datake jiyo kamshin nasa , ahankali idanunta suka cin karo da kyakkyawan fuskarsa ko kallonta inda take baiyi ba , yakarasa shigowa parlour fuskar nan tashi a daure tamkar zaki .

,take taji zuciyarta ta tsinke tasoma rawa wata irin zazzafar kaunarshi ce ta dinga taso mata tamkar ta tarwatsa mata zuciya , lokacin data daura idanunta kansa.

kamshin turarensa ya addabi hancinta ji take kmr tajita a kusa dashi .
sallama Yayi aciki.
ta amsa tare da sunkuyar da kanta kasa har ya wuceta yasoma taka step bata dago da kanta ba, sai da tabbatar da tadaina jin motsen takunsa" sannan ta dago tana sauke ajiyar zuciya tare dafe kirjinta tace wayoooo Allah kirjina .
dan ita kadai tasan yadda ta dinga ji .
can taji sautin shigowar sako a wayar Ummi " ,sharewa tayi tunaninta ko yan network ne.
Dan haka ta maida hankalinta kan shirin da'ake gabatarwa a TV.
minti biyar tsakani taji wayar ta dauki kara ta dauki wayar tana dubawa .
Wata bakuwar number tagani" yana yawo akan screen din .
Dan haka ta manna wayar a kunneta tare yin sallama .
muryar da tafi so da tsoro ne "ta daki dodon kunneta hakan yasa jikinta ya sake daukar rawa gabanta yashiga faduwa da sauri .

,yace ke dan iskanci da rainin wayo bakiga sako na bane ?
Muryarta A sanyaye tace ban gani ba Amman kayi hakuri dan Allah tsaki yaja tare da kashe wayarsa .
Da sauri tashiga in box din tasoma duba sakon

Kisame ni a dakina yanzu " abinda tagani kennan .

,take gabanta yacigaba da faduwa , duk da tana cikin fargaba hakan bai hanata ,mutunta kanta
da son janyowa kanta martabarta ta Diya mace .
Sai da ta dauki mintina tukun ta mike cikin sanyin jiki ta nufi dakin shi .
tsaye take akan kafafunta a bakin kofar dakinsa zuciyarta na dokawa .
tsoro taji yana shigarta sai ta daura hannuta kan handle din kofar .
sai tacire hannuta da sauri .
,da kyar tasamu tattaro duk wani kuzarin dake jikinta .
,karfin hali tayi wanje murda handle din kofar da iya karfinta tashiga parlour'n da sallamarta .

shr parlour bakajin komai sai karar TV tsayawa tayi tana jirashi kusan 5 minti bata ga alamunsa ba ko jin motsensa batayi ba . dan haka ta yanke shawarar shiga Bedroom dinsa.
tana shiga dakin gabanta ya tsananta faduwa , cikin sanyin murya ta sake yin sallama .ya amsa da kyar km a ciki .

Zaune taganshi yana operating system sanye cikon wando three counter da pure whit singlet , ahankali take takowa har inda yake yayinda kanta ke sunkuye .
tsugunnawa tayi a gabansa muryata na rawa tace Gani Yaya .

GA TSARABARKU TA KANO BA YAWA KUYI MANAGE 😃😃😃

MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Page 25- 26

Bai ko kalli inda take ba hasali ma operating din system dinsa yacigaba dayi.
" tayi kusan minti goma tsugunne a gabansa batare daya dago idanunshi ya kalleta ba .

Shr Tayi tare da" sunkuyar da kanta kasa .
Yayinda zuciyarta ke tsananta bugawa .

cikin daddaden muryarsa may cike da dadin sauraro "fiyye da komai datafi kauna .

Yace tun yaushe kike tare da wance sakaran Dana ganku shekaranjiya ?

Batasan sanda ta zauna ba ,dan tsabar frigice da tsoron daya shigeta na lokaci guda .

,zuciyarta ce tasoma rawa...rawa tare dokawa .tarasa yadda me za tace.
cikin ya'n sakanni nan hankalinta yayi matukar mugun tashi. kwakwaluwarta "tashiga tariyo mata abinda ya faru a shekaranjiya din .

gabadaya tagama
frigita da tmbyr daya jiho mata, tunaninta ya ta'alaka ne akan ya manta da abinda yagani din .
dan ganin ya share Bai nuna koda a fuskarsa ba .
da kyar ta iya bude bakita tare da son nuna masa , itama batasan inda zancesa ya nufa ba.
, muryarta cike da rudani tace wa kenan ?

Sai Lokacin ne ya dago rikitattun idanunshi ya dubeta dasu .
,tare da zabgamata wata uwar harara .
cikin sanyayyayiyar muryarsa, ta isa ya sake yin magana Yace wawa ..... .ni zaki waskewa ya nuna kirjinsa da yatsansa
bakaramin laifi zaki karawa kanki wajen nuna min bakisan abinda nake nufi ba .

Domin bana bukatar
rainin hankali ko karyata min abinda idanuna suka gane me .

Amsa tmbyta kawai nake da bukata .

take muryarta tasoma rawa alamun kuka keson kufce mata.
,ahankali ya daura yatsan hannunshi akan lip's dinshi " shiiiiiiiiiii....... karki kuskura naga Tear's dinki ko rawar murya .
dan banida bukatar su .
I said tun yaushe kuke tare , that's ol ....
A boye ya dinga sauke ajiyar zuciya sannan ya"
yacigaba ko duk dadewarku bakisan tun lokacin da kuke tare ba ?

Lokacin daya taji maganarsa na neman birkita mata Brain dinta. to up side down" wani irin rudewa da gigicewa ta sake yi .

Ba bakinta kadai ke rawa ba ,yanzu kam har gangar jikinta rawa yake .

Ta dawo tamkar wata zautacciya Da kyar tasamu ta iya hadeye abinda taji ya tsaya mata a makoshi .
tare da zubda hawayen da suka taru a idanunta, cikin rawar murya tace shekara biyu kennan.
Tana gama fadar haka
, tayi saurin sunkuyar da kanta kasa dan gudun jin saukar mari .

yayinda hawayen tausayin kanta suka cigaba da bin kuncinta.

a hankali ya dinga girgiza kanshi shekara biyu kennan ya sake maimaitawa kansa.
Cikin sanyi ya maida jikinsa" ya kwanta rigingine ya Kuma cigaba da operating din system dinsa batare da ya sake ce mata komai ba .
,Take yaji zuciyarsa ya dauki beating ,wanda yarasa dalilin jin haka .

Kusan minti shabiyar kennan idanunshi na kan system dinshi yana cigaba da aikinsa .
, wanda mutun zai iya dauka aikin ne kawai a gabansa"
amman a zahirin gaskiya hankalinsa ya rabu gida biyu ne . kan aikinsa da nazarinta yanayinta " maganarta ba iya kunnenshi kadai ta tsaya ba " har gangar jikinsa takaiwa farmaki . ahankali ya dinga furzar da iskar mai zafi daga bakinsa . gashi dai magana yake son yi amman taki fitowa sakamakon zuciyarsa dake bugawa .
,da kyar yasamu iya bude bakinsa .
yace kina nufin shima sonki yake yi kennan ?

Tsoro da faduwar gaba ne suka taru suka mamaye zuciyarta.
cikin in..inna ..tace wai wai haka yace "amman , dan Allah kayi hakuri .

da sauri DEENi dake rigingine ya mike zaune cikin daga murya yace mene ? Nayi hakuri ubanki "
Da sadakin nawa akanki idan da kuna kula juna ,I don't care .
Amman yanzu iskanci ne yasa kika, cigaba sauraran wancen sakaran dan tsabar kin raina min hankali.

Bakinta na rawa tace Ai shima yasani" shiyasa ma yace ya hakura dani .
, ok da shi m...
sai km yayi shr yakoma ya kwanta . hade da runtse idanunshi . Lips dinshi na kasa yakamo yana cizawa a hankali ahankali " cikin zafin rai da kunar zuciya ya nuna mata kofa da yatsansa alamun ta bar masa dakin .

,kasa Mikewa tayi tsabar tsoro gabanta yacigaba da faduwa ,muryarta na rawa" ta sake yunkurin bashi hakuri dan Allah yaya kayi hakuri wlh mun rabu dashi tun ba ya...
Chapter 24 · 0% Book details