← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 149

Sashe 135

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da wani irin mugun sauri ya dago da rikitattun idanunsa ya zubawa ummi sosai yana mata wani irin kallo me tsoratarwa sannan da mamakin mgnrta saman fuskarshi .

Eh deeni bazakataba Gane hakan ba sai lokacin Yayi .
Amman ka rigada ka fada son yarinyar nan tunda har ka iya marin zeenat agabana akanta batare ko shakkata ba .
km ka rungumi matarka agabana deeni ka kwantar daita akan kirjinka hkn ya tabbatar min da bakaramin so kake yiwa nablah ba.

ni dai koda zamanku zai daure daita fatana dan Allah dan annabi kayiwa diyata zeenat adalci karkaga wannan itace uwar ya'yanka itace me haihuwa sannan ka wulakanta min zeenat ko byn raina banason ka wulakanta min ita .
dan hk ka natsu ka kwantar da hankalinka da kyau akan 'cikin jikin nablah Allah ne yabaka 'cikin jikinta km shine me tsare bayinsa .
" inshallahu da kariyarsa nablah zata haifamaka abinda ke 'cikin ta.

A hassale muryarsa Na rawa yace ni duk ba wannan ba tunda nace kartaje ba sai a hakura ba idan lokaci hk Yayi da kaina zan kaita uhmmmm sannu ubanta mlm salisu .......

yau wata nawa rabon yarinyar nan da iyayenta kada ka mata ita kanta nablah bazataso zama tare da iyayenta ba a halin datake ciki .
Km ma Muyi daita yau din nan zata dawo .... zuciyarsa a hassale km muryarsa can kasa kasa yace first love nidai gsky banso tafiyarta ba. sannan km mgnr wai Ina son yarinyar nan komai komai.... shima ba hk bane first love domin ni nasan zuciyata nasan abinda take so da wanda bata so . banasonta yarinya idan har. Na afka sonta ta yaya bazan gane ba yakarasa fadar mgnr tare da juyawa fuuuuuu yasoma tafiya ranshi abace ya bar gidan ummi tayi murmushi irin Nasu Na manya deeni kennan ne rikicin gangan Allah Yayi maka albarka tare da sanyaya maka zuciyarka ..

Hayaniyace ta kure 'cikin gidan mlm salisu da murna da kururuwar ganin nablah gabadaya duk wanda ya kalli fuskokin ahalin gidan murna suke da farincikin ganinta ..

Mama tashiga nan nan da diyarta kanneta zagaye daita kowannesu Na murna ganinta hatta aunty Salma tazo da murnata wace ummi ce tasanar mata da zuwan Nablah din . gabadayansu ,suka saka nablah a tsakiyar su .suna murna da jin dadi ganinta .
nuratu ta kalli nablah da kyau .
Kai Alhamdulilllahi yau dai zamu huta da shan zagi gurin baba.
Na aunty Salma ta tsiyar masa da "ya" nablah tayi murmushi wanda ke karawa fuskarta kyau da annuri tare da cewa banana kennan.
nayi kewarsa nima sosai fiyye da tunaninku ..

uhm kalli yadda kika dawo Nablah kinyi kyau dake kikayi fresh sosai gadabaya fatar jikinki ta sauya wlh gurin nan ya amsheki inji cewar nuratu ..
Allah ko nablah tace hk tana murmushi sannan tacigaba duk wannan kyawun da fresh din danayi wlh nafi son gidanmu koda kuwa za'a kwana bamu ci ba Amman dai zan koma sbd wani dalili nawa .. aunty Salma tayi saurin cewa wlh bada hannuna ba 'cikin komawarki .
Ni dai tunda kin dawo Na auna arziki Na huta da fadan baba wlh har fargaba zuwa gidan nan nake .
Tun tafiyarki nake 'cikin tashin hankali boye miki kawai nakeyi sbd kwanciyar naki hankalin Amman mgnr gsky Na tsorata da al'amarin baba.. nan nuratu tashiga zaiyanewa nablah labarin duk abinda ya faru da yadda aunty Salma ke shiri idan zatazo gida .
aiko gabadayansu suka kwashe da wata mahaukaciyar dariya .

Maman da tun sanda suka fara hirasu da nuratu da Salma ba tsoma musu baki ba sai yanzu tace uhmmmm nablah bana jin babanki zai yarda ki sake barin gidan nan ballanantana har ki koma wani aiki.
ni kaina wlh yanzu banaso komarwaki .
dan hk bbu inda zaki ki zauna kema 'cikin yan'uwanki zan fi samun kwanciyar hankali .
Aunty Salmah tace wlh zanceki gaskiya ne mama Amman kubari baban yazo tukun nasan da zarar yasanar mata da abinda ya zartar akanta zata natsu ... ko babu wannan dalilin bazata koma koina ba inji cewar mama .
murmushi takaici nablah tayi tare da cewa Mama kennan Allah Ni dai zan koma wlh Amman Na da wata uku zan dawo gabadaya gareku.
mama dan Allah kada kice a'a ta karasa mgnr tana marairaice muryar .
uhmmmm mama ta sauke ajiyar zuciya to shikennan Amman kibari babanki yazo kiji me zaice.
Take sukar bar zance suka shiga wata hirar daban .
karfe hudu daidai sai Ga direban ummi ya dawo daukar nablah Amman nablah ta fita da kanta tace ba yau zata koma ba sai zuwa jibi ko gata. da zai wuce aunty Salma ta bishi Dan ya rage mata hanya .

Da daddare byn sallar isha'i mlm salisu yashigo gidan da sallama a bakinsa hannushi rike da wata bakar leda yana shiga dogon parlour gidan.
idanunshi suka sauka kan diyarsa nablah dake sanye da hijab ajikinta wanda tun safe datazo gidan bataci re ba tana kwakume dashi abinda Yasa ma mama bata mata maganar ta cire ba sbd tasan tun asali hk take mayar hijabi ce ita ko bacci zatayi bata cirewa ..

Ahankali mlm salisu yakarasa shigowa ciki tare da cewa wanake ganin hk kmr nablah agidan nan ?

Nuratu ta tashi da sauri jikinta a sanyaye ta karbi ledar hannushi ta ajiye a gefe tana mishi sannu da zuwa .
Bai kulata ba sbd hankalinsa dake kan nablah ..tsam itama nablah tayi da ranta tare da shan jinin jikinta sbd ganin irin kallon da mahaifin nata ke jifanta dashi .
jikinta a matukar sanyaye ta bude bakinta da kyar gurin cewa sannu da zuwa baba ..

uhmmmm yauwa Yan neman abun duniya da fatan dai kin samo masu yawa ?
Nablah tayi tsit ta sake sha jinin jikinta ai nasan duk inda kika je zaki dawo , indai nine ubanki ba shegiya bace ke.....
yakarasa mgnr yana nunata da yatsa hannushi haba haba baban Salma tun...ke ...nasakaki cikin maganata ? Ya katse mama Yacigaba da mgnrsa .
Da "yata" nabeelah nake mgn ba da saratu ba .
dan hk banason jin bakinki cikin manta .
,ai duk da hadin bakinki yaran nan suke yi duk isakanci da sukaga dama.
basu dauke ni abakin komai ba km wlh duk lalacewata ni nan nine ubansu dole km akirasu da sunana sai dai mutun ya gudu bazan fasa mgn ba da cin uwar yarinya tsit kake jin gurin tamkar babu wasu halittu acikin parlour ..mlm salisu yacigaba har ni ubanki zance miki banason abu kice sai kinyi dole .

Ni talakane me wadatar zuci banida karfin daukar nauyin karatunki Amman kice dole sai kinyi .
Yanzu Ina kudin da kika samo a yawon duniyar da kike je dan nasan ba aiki kikaje ba?
duba Ga yanayin sauywar da jikinki Yayi Amman bbu komai hkn ma daidai ne a gurina kinyi son ranki nima nayi son zuciyarta akanki yakarasa fadar Haka tare da shigewa 'cikin dakinsa Bai sake cewa komai ba.

jikin mama Na rawa tace kungani ko.
Kunga irin abinda nake gudar muku kennan Amman bakwa jin magana..

Maza maza ki tashi kibishi dakinsa ki bashi hakuri ..

Jikin nablah a matukar sanyaya ta Mike tsaye ta karasa 'bakin kofar dakinsa ta dan yaye labulen dakin babanta.

Ta hangoshi zaune shr yasa hannushi daya ya tallabe habarsa dashi tashigo ahankali ta durkusa da kyar tayi neldwon 'agabanshi muryarta Na rawa tace dan girman Allah babana kayi hakuri Allah bazan sake ba km wlh tsakani da Allah aiki naje baba ba yawon duniya ba .
Duk da nasamu abinda Na fita nema Amman banida natsuwar zuciya sakamakon bijirewa mgnrka danayi .
Amman kayi hakuri baba takarasa mgnrta hawaye Na bin kuncinta ..

Mlm salisu ya sauke naunauyen ajiyar zuciya yana duban nablah diyarsa wacce yafi so da kauna duk a 'cikin ya'yansa komai nashi ta dauko basu da bambanci komai sai dai kasacewarta macce muryara a sanyaye byn Yayi gyaran murya yace shikennan nablah Allah kyauta km alhamdulilllahi tunda Allah Ya dawo min dake lfy bbu abinda ya sameki ai Na auna arziki.
kukan nablah ya tsananta yayinda a ranta km tace wayyyyyoo babana akwai abinda yasameni har Yayi min nakasu a rayuwata ..

kibar kukan hk Na hakura km na yafe miki Allah Yayi miki albarka sai dai wani hanzari ba gudu ba nima nayi miki abinda bazaki ji dadinsa ba ..
Domin kuwa byn tafiyar ki bbu dadewa wani mutumin kirki yazo neman aurenki nan dai mlm salisu yayiwa nablah bayanin abinda ya faru byn tafiyarta tun daga farko har karshe ..

Nablah Ta dago shanyayyun idanunta afrigice tana kallon mahaifinta dasu .
Shima ya dago yana nazarinta tare da daga mata kanshi alamun gaskiya ya sanar mata .
Ya numfasa kana yacigaba haushin abinda kika min da kaicinsa da km kimar mutumin Yasa Na aikata Haka ..
nablah wannan mutumin dana aura miki mutumin kirki ne me mutunci da girmama babba. bakiga yadda yake hidima damu ba ke kanki kinsan rayuwar gidan Na tausaya da al'amuran cikinsa gabadaya .
yanzu Hk shine ya hanani wanki hular da nakeyi ada ya samomin aiki me daraja acikin apapa..

bbu abinda zancewa wannan mutumin sai Allah Yayi masa albarka km ya albarkaci aurenki dashi ..
yanzu tunda kin dawo zan nemeshi nasanar masa ya turo iyayensa gareni domin nasan nasabarsa da inda yake zaune ..
sosai nablah ke resgar kukanta har da shesheka tana jin wanin irin zafi 'cikin ranta meyasa abubuwa suke zuwa mata hk?
daga wannan sai wannan tasan shikennan shirin karatunta ya rushe kennan har abada tarasa burin zuciyarta da farincikin rayuwarta .
yau tazo mata da abubuwa iri iri masu daci da muni.
rasa karatunta 'cikin jikinta ...auren da babanta ya daura mata batare da amincewarta ba ..

nabeelah mlm salisu yakira sunanta kinyi shr kina kuka bakice min komai ba.
ko zaki butulcewa zabin dana miki ne?

Ta sinkuyar da kanta kasa sosai tana sake fashewa da wani sabon kukan me cin rai da taba zuciya tare da girgiza masa kanta ...

Kin amince da auren dana daura miki ?
Chapter 135 · 0% Book details