Sashe 114
Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Runtse idanunta tayi gammm..... wasu zafafan hawaye Na tsiyaya akan kuncinta karo Na farko data ji wata mummunar qiyayyar wanda yayi mata wannan aika aikan ya shiga zuciyarta daram ya zauna tare da huda duk wasu gabobi da jijiyon dake aiki acikin a sansar aikinta.
,koda kuwa ba halitar bil Adama bane ,wato aljani .. kuka take sosai har dana fitar hankali
Kokarin zamewa take daga gangar jikinsa duk da yadda take jin kanta ajikinshi amman takasa raba kanta dashi dan sake rungumeta deeni yayi tsam ajikinshi yana fidda numfashin ,'cikin wani irin matsanancin kuka tafara mgn da muryarta da soma dashewa ni ka sakar min jiki ...
kabarni nace ...
Kabarni Naji da maseefar data sameni....
Ni nablah ke dauke da 'cikin shege yau ... DEENI yashiga girgirza mata kanshi batare dayasan ya aikata hkn ba ...
Kana jin abinda doctor tace ciki gareni fa har Na tsawon wata hudu amman kake rungume dani ajikinka ...takarasa fadar hkn tare da fashewa da wani sabon kuka me cike da cin rai da girgirza zuciyar ma'aboci sauraro...
ahankali DEENI ya sausauta rungumar da Yayi mata ajikinshi yayinda jikinta ya sake daukar kirrrrrrma sun kusan minti ashirin a haka , kafin daga baya ya dagota cike da kulawa ya tsura mata rikitattun idanunsa ,yana kallonta. da kallon yanayin tashin hankali datake ciki .
,rasa yadda zaiyi da rayuwarsa ,yasashi cigaba da kallon cikin kwaryar idanunta kawai.s sannan ya hadeye abinda yaji ya tsaya masa a makoshinsa .
yayinda doctor saira ke tsaye tana kallonsu tamkar wasu jaruman shirin fillm .gabadaya al'amarin Nasu ya zauta hankalinta tare da girmama tunanita .
"Barinma Yadda taga deeni ya rude da gigicewa akan yarinyar ko shine Wanda Yayi mata 'cikin wa tunaninta iyakacin abinda zai yi kennan..
Ahankali yacigaba da kallon yadda kukan ke galabaitar daita .
"tayi mugun fita haiyacinta.
Ahankali yasa hannushi ya kamo tafin hannuta 'cikin nashi yana shafawa da baya hannushi ahankali 'cikin sarkewar murya yakira sunanta da sanyyayiyar muryasa .
da kyar ta bude shanyayyun idanunta ta xubasu 'cikin nashi batare data amsa masa ba.
,Ya lura gabadaya jikinta a sanyaye yake ko dan yatsanta bata iya motsawa,kokarin son dagota yayi ta zame jikinta daga gareshi..
kabarni DEENI bazan iya tashi ba.... ta sake tsananta kukanta me tsuma zuciya .
Muryarta a sanyaye ta dinga furta kalmar...wayyohhhyyy Allahna.
.
wayyohhhyyy Na shiga uku ..waye Wanda yayi min wannan cikin da bai kasheni gabadaya Na huta daganin wannan ranar me tattare da bakin ciki rayuwa ba?
... wayyo Ni nablah me zancewa mahaifina dayace kada nazo aikatau ..?
Me zancewa yan'uwana da suka tattara dukkan wata yardarsu da amanarsu gareni" tare da amincewa dani ,?
Wayoyyy wayyyyyoo Ni nablah wazan ce yayi min ciki......? Kuka take hade da sambatu iri iri .
,tausayinta ya sake kama doctor saira ya mamaye zuciyata sosai har batasan sanda hawayen tausayin yarinyar yashiga tsiyayo mata ba .
, ahankali ta zare dan siririn medical glass din dake manne da fararen idanunta ta goge Hawayen dake tsiyayo mata tare da maida medical glass dinta tana cigaba da kallonsu , ...
Mikewa nablah tayi da kyar tana layi... yayinda gafe daya km tasoma ganin juwa juya.
batare data juyo ta hankalta da irin kallon tausayin da doctor saira ke mata ba.
" ta fara tafiya cike da damuwa da rudanin rayuwa....
DEENI ya zabura ya Mike tsaye ya biyo bayanta da sauri yana Kiran sunanta tare da kokarin dawo daita amman taki sauraronsa ,sai ma fizge jikinta datayi daga nashi tacigaba da "Daga kafafunta da kyar ..
tafiya daya biyu zuwa uku tayi DEENI yayi nasarar sake damkota gareshi Ina zaki a hk...?
Ki natsu man musan abinda yakamata a yi duk wannan kukan naki bashi ba sulotion atare dake .....
zubewa tayi ajikinsa tare da sakin wani irin gigitaccen kuka.
ahankali tasa hannuta ta dafe daidai tsaitin zuciyarta datake jin yana mata zafi tamkar zata tarwatse..
" ta manne ajikinshi tana sakin numfashi da kyar tare da lumshe shanyayyun idanunta hawayenta Na tsananta zubowa, yayinda zuciyarta ke dada karyewa sbd mummunar halin data tsinci kanta ciki ..
Ahankali ta bude shanyayyun idanunta data lumshe ,tasoma ganin dakin Na jujjuyawa daita ...juwa take Gani sosai Domin zuwa lokacin bata ganin komai dake 'cikin dakin hatta bakin dake cikin idanunta yasoma yin sama da kasa alamun juyewa .
DEENI ya dake rungume daita a jikinshi yana kallon yadda idanunta ke son kakkafewa Yayi saurin yin kasa daita , kafin ya ankare tuni ta saki wata irin naunauyen ajiyar zuciya me karfi gaske .
Yayi saurin saka hannunshi duka yana jijiga fuskarta da iyakacin katfinsa tare da Kiran sunata a rude na..bee..lah.. na..bee..lah dan girman Allah Kada ki min Haka please.... ki natsu musan abin yi tukun yana cigaba da girgirzata Can yaji gabadaya takarasa sakewa ajikinshi .....ya tsayawa cak ..... yana dubanta da rikitattun idanunsa....
Gani Yayi bata numfashi ya dago fuskarta da sauri yana dubanta sannan a rude yasa byn hannushi a hancinta .
Amman kwata kwata bai ji wata alamun
numfashi a atare daita ba .
'Cikin wani irin tashin hankali da matsanancin fargaba ya Mike tsaye daita.
Yayinda , jikinshi ya dauki wani rawa yana Kiran sunnan doctor .......
kai tsaye kan dan madaidaicin gadon marasa lfy ya nufa ya kwantar daita yana sake Kiran sunan Doctor.
,yayinda doctor saira itama tazagayo daga inda take tsaye.
da mugun saurinta tare da kallon abin mamaki yadda DEENI ke sake ya rudewa akan wannan yarinyar dabata gama Sanin kowacece gareshi ba .
da dan hanzarinta takaraso inda nablah ke kwance tamkar wata matacciyar gawa dan bbu inda ke motsi a sansar jikinta..
Cike da natsuwa doctor saira tasoma dubata suma tayi doctor saira ta fadi hk tana duban Inda DEENI ke tsaye rike da hannun nablah yana mammatsawa ko zata dawo haiyacinta..
suma ... DEENI ya furta hkn da karfi jikinshi Na sake daukar rawa duk jikinshi bbu inda baya tsatsafowa da ruwa gumi tsabar tension din dake zariya a gabobin jikinsa.
,Ok please doctor taimaka min kibata taimakon gaugauta please.
Abinda nake kokarin son yi kennan ..
DEENI ya saki yatsun Hannu nablah da kyar .
ya shiga zariya acikin makeken office din yana furta duk wata addu'a dayasani Dan neman sausauci a gurin Allah.
da taimakon Allah dana doctor saira aka samu numfashi nablah ya dawo daidai yasoma sauka ahankali ..
doctor saira ta sauke ajiyar zuciya ganin numfashin nablah ya dawo daidai ,shima DEENI sai lokacin hankalinsa ya dan kwanta ..
Doctor tace muje mr DEENI Ina son magana da kai, ya gyada mata kanshi kawai batare yace mata komai ba sai ma zuwa yayi ya zauna kan kujera yana furzar da huci me gauraye da tashin hankali.
Doctor saira ta zagaya ta zauna tana dubansa Na wasu Yan dakiku sannan ta saki numfashi kana tace .
"yanzu Mr DEENI yakake ganin za'a bulowa Lamarin yarinyar, kaga dai yadda ta daga hankalinta akan 'cikin jikinta ?
Jikinsa a matukar sanyaye yayinda gabadaya yanayinsa ya sauya 'cikin lokaci daya da kyar ya iya bude bakinsa gurin cewa ki barni daita kawai zansan yadda zanyi handover din koma ta yadda komai zaizo da sauki .
Wlh yarinyar tayi matukar tabani tausayi sosai yanzu kowaye mutumin da Yayi mata 'cikin ?
Nima abinda nake son sani kennan DEENI yabata amsa da hkn.
A gsky idan ba,zaka damu ba zanso nashiga 'cikin lamarin binciken Wanda Yayi mata 'cikin jikinta ...Wannan ba damuwarki bane ba km hurunmin ki bane da son sani Wanda Yayi mata ciki DEENI ya katseta ta hanyar ce mata hk ...
A dan kausashe yacigaba da kaina zan nemo duk Wanda Yayi mata hkn sannan Na zartar da hukuncina akansa ..
Ok hk ma Yayi
Amman kasoma da rarrashin ita yarinyar firstly ko zata tuna Wanda Yayi mata haka kafin ka zartar da komai.
Yace uhm alamun yaji ....
Cike da natsuwa Ta tsura masa ido kawai tana sake dubansa da nazarinsa sosai kana tace dan Allah in maka wata tambaya Inda bazaka damu ba ....
Ya dago rikitattun idanunsa ya zuba 'cikin nata kana ya sake ce mata uhmmmm...
Ina son sanin matsayin yarinyar nan a gurinka? ..Yayi tsaida da ranshi tare da yin shr yana nazarin abinda zai ,daga karshe da yace mata cousin's muke daita . Ok shiyasa naga duk hankalinka ya tashi to Allah kiyaye gaba .. doctor saira nagama fadar hk ta Mike tsaye tana gyara farar rigar jikinta ta nufi kofar fita Domin son zuwa duba peticent dinta ..
Kusan awa daya da fitar doctor saira sannan nablah ta farka ... da wani matsanancin kuka har da shesheka deeni dake tsaye akanta ya matso sosai kusa daita ..yana shafa sumar dake baje a kanta.
Ahankali ya dinga jero mata sunnu babu kwaukwautawa.
, shr kawai tayi tana kukanta batare datace masa komai ba.
Yasa hannunshi ya dagota tare da jinginar daita .sannan ya zauna kusa daita ganin yadda ranta ke a jagule da bacin ran halin datake ciki.
yasashi Mikewa tsaye 'cikin tsanyi jiki Ya nufi dan karamin fridge din doctor saira ya dauko ruwa mai tsanyi ya zuba mata a cup ya kara mata cup din a daidai lip's dinta, yashiga bata ruwan da kanshi .
Sai dai kadan Tasha ruwan ta cire bakin daga cup din tare da jan naunauyen ajiyar zuciya.. DEENI ya ajiye cup din a gefe daya , ya tsura mata idanunshi yana kallonta ji yake tamkar ya rungume ajikinshi ya rarrashita ,hk yaji ..'cikin muryarsa kasa kasa yakira sunanta tare ,
Da kamo tafin hannuta 'cikin nashi yana shafa byn hanunta da nashi hannun ahankali ..
bata amsa masa ba ,sai numfashi da take saki akai akai .
muryasa a kasalance ya sake Kiran sunanta nabeelah kallonsa tayi da shanyayyun idanunta.
ido cikin ido suke kallon junansu , gabanta yashiga faduwa da sauri Wanda Shima sai dayaji hkn atare dashi ..
wai garin Yaya hk ta faru dake ne ?
Shr tayi bbu amsa dan gabadaya wata irin kunyarsa ce ta rufeta ta kasa cewa komai sai kallon 'cikin idanunshi da take ..sai da suka dauki sama da minti goma a hakan suna kallon juna ko wannensu ya kasa dauke idanunshi daga kallon dan uwansa , km kowannesu da abinda zuciyarsa ke sakawa ...