← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 149

Sashe 2

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Byn wani lokacin su sulaiman suka cigaba da tallafawa ummi da DEENI a lokacin farida na dauke da tsohon ciki duk da itama ta dan jima bata haihuwa ba, kuma har lokacin ummi bata san er'uwarta tana cikin matsala ba ,sai byn data haihu" lokacin ne ummi taga komai bbu alhalin ga tarin dukiya kmr zai kashe habibu , gashi yasake kara wani sabon auren matansa sun cike hudu cif .
ummi tayi kuka kmr may gashi tana cikin danginsu da suke tamkar tsiya madauri daya.
ba daman tace zata dauki wani mataki akan haka .
dan tasan yadda kansu yake a hade .
dan haka taci kukanta takoshi ita da er uwarta ahankali take furta kalmar shiyasa tun farko naki amincewa da auren nan naki da habibu ,ba dan komai ba sai dan irin haka Amman kika nace ,ga irin abinda nake gudar miki kennan Amman kika kiji , sai kuma ta tsagaita da kukanta ahankali tace ba yadda zamuyi da ikon Allah ,sannan ga rabo a tsakani.
Amman duk da haka sai da ummi tayi masa tatas saboda daman ita bawani sakar masa fuska take ba kuma yana shakkata.
kullum ummi acan take wuni har ranar suna yarinya tace sunan mahaifiyarsu ummi wato muzeenat , shima habibu yayi hakan ne saboda ya wanke kansa a wajen ummi,kuma yayi nasara domin hakan da yayi yasa ummi taji dadi Sosai aranta har ta dan rage jin zafinsa .
sannan bakaramin kudi ummi takashewa bby ba. haka ma ranar suna ummi Tayi rawar Gani sosai .
byn anyi suna ne ummi tasamu habibu akan dan Allah ya dinga kula da farida dan ita kadai gareta bata da kowa duk fadin Nigeria sai ita, idan ma bazai damu ba, zata bashi Rabin dukiyarta yakara akan nashi da duk wani abinda yake so, ita dai burinta kawai ya kular mata da er,uwa ,yayi murmushi kawai hade da ce mata yaji .

Byn wani lokacin farida ta kuma samun wani ciki wanda tun yana karami take fama da laulayi tun lokacin ummi tadawo da zeenat wajenta ,
a kwana a tashi bbu wuya a gurin Allah har cikin farida ya isa haihuwa gurin haihuwar ne taji jiki sosai .
koda ta haifi yaron ma bbu rai sannan itama tace ga garinku .
mutuwar ta shigi habibu matuka yayi kuka tamkar ransa zai fita ,dan shi kansa yasan yayi babbar rashin da ba zai taba maida irinsa ba.
yayi rashin mata mai tsananin kirki da hakuri da sanin darajar miji . Allah sarki ummi kusan har tafi habibu jin mutuwar tilon er'uwarta ta ,.
a wannan Lokacin ne rikon zeenat ya dawo dindindin gurin ummi ta dauki soyayyar duniya ta daurawa zeenat tana mugun ji da Yarinyar tamkar ranta kwata kwata bata son abinda zai rabata da zeenat Sannan kuma tana debe mata kewar er'uwarta .
lokacin shi DEENI na ss1 a NMS, Nigeria military school dake zariya.
yayinda DEENI Sam ba halinsu daya da ummi ba koda yaushe kagansa fuskar nan tasa a daure a cunkushi bbu wani fara'a ga shegen miskilanci tsiya sai dai mugun kyakkyawa ne na karshe . ajin farko, wato first class ,gashi da maseefar iya sa kaya kallo daya zaka masa ya gigitaka kaji yashiga ranka farar daya saboda tsabar kyawunsa sai shegen shiga ran mutane domin kusan yan'mata cikin estate din suna maseefar son sa yayinda yake girma kyawunsa na sake bayyana hade da miskilancinsa .

Tunda zeenat ta dawo gidan magana bata taba hadasu ba ko gaisheshi Tayi baya amsawa in dai bayaga idanun ummi ba yana da matsanancin tsafta wanda kusan a wajen ummi yagada .
Cikin haka ya kammala karatunsa na secondary school ya wuce NDA burinsa kennan nason zama cikakken soja itama ummi kuwa nasake karfafamasa gwiwa da bashi goyon baya yana karantar science ne ,wato likitan soja .
bansan yadda zan kwatanta muka halinsa ba Amman yakasance mutun ne shi mai bambanci ra,ayi.
byn yakare karatunsa ya fito da mukami second lieutenant star biyu kennan .

Zaune zeenat take a falo tana kallon wani serisfilm a zeeword my let home Tayi zurfi cikin kallon film din gabadaya attention dinta naga kallon ita kadai ce ummi tashiga cikin estate din yin barka taji karar Bell wanda shine kusan karo na hudu da taji ana dannawa. cikin jin haushi ta mike dan bata son abinda zai dagata daga kallon datakeyi , tana bude door din bata tsaya ganin kowaye ba ta juya abinta takoma mazauninta sallama taji hade da shigowa ta dago kanta kennan da niyar amsa sallama sai taga mutun tsaye kikam sanye da sabon kayansu na sojoji gabadaya zeenat ta gigice hade da rikicewa tsabar tsoro dan ita Allah yayita da maseefar jin tsoron soja take cikinta ya dauki kugi Amman still idanunta na kansa ta tsaresa da kallo .
in ina tasoma yi wa..wa.. waalai....ya dakatar daita da hannushi, yana zabga mata wata uwar harara muryasa a kwasashe yace yau ne kika fara ganina da har zaki wani tsareni da idanu Kona canza miki ne ?da sauri tasoma girgiza masa kai. Kai tsaye dakin ummi ya nufa tunda bai ganta a parlour ba yasan tana dakinta tana kallonsa ta kasa dauke idanunta daga garesa har sanda ya dawo fuskar nan tasa a hade yace ke.....dan iskanci kina kallon mutune bazaki iya cewa ummi bata nan ba kin wani tsare mutun da idanuwa tamkar na maciji ,dayake bawani manyan idanu gareta , da sauri bakinta na rawa tace dan Allah kayi hakuri mantawa nayi ko kallonta bai sake yi ba yaja tsarki yayi hanyar dakinsa ta tabe baki hade dacewa jarababbe kawai ai yadawo kennan, itama taja tsaki ta juya tacigaba da kallonta ..

MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

Aysha A bagudo

Page 3-4
Chapter 2 · 0% Book details