← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 149

Sashe 40

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Momy fervor tace Aa ai hjy tabani zeenat tace kar ki damu ki karba kawai ta amsa tana risinawa da godiya . saannan ta sake cewa su moris dan Allah su maida hankali suyi duk abinda yakawosu da duk abinda yakamata ta Mike tana yi musu sallah .

Say Washegari da safe deeni yaga masu aikin duk bawani kwanta masa sukayi ba ,dan haka ya kira doctor din dake kula da lfyr zeenat.
yace tazo ta kai su moris a musu gwajin jinin sbd sanin cikakkiyar lfyrsu.
,hakance ta kasance anmusu gwajin komai normal zeenat tayi musu bayanin duk aikin daza su dinga yi mata .

Ke moris girki zaki dinga yi ke km rahma gyaran sama da kasa ,suka amsa mata da to.

Zeenat makale da kudinrin tana Allah Allah taji kiran sumy dan sam bata zata iya hakura da zaman cikin ba .

Thursday kmr yadda Sumy ta shida mata dawowar nurse .

Ta shirya suka je km sun sameta a gida ,byn Sumy tayiwa nurse titi bayanin abinda ke tafe dasu .

Nurse titi tace badamuwa su sameta a office hakance takasance .

byn sun sameta nurse titia office dibta ta dubi Sumy tace how many month cikin ,Sumy tace going to 4 month .

Nurse titi ta dubi zeenat tace ke meyasa zaki zubar da ciki? Sumy tayi saurin cewa wlh wani saurayinta ne yayi mata cikin ...so km karatu suke shiyasa take son zubawa . zeenat na tana jin yadda sumy ke zuba karya ,wel ita dai ba wannan ne matsalar ta .

,Nurse titi tace ok yanzu abinda za'a yi duk cikin wata daya muna cireshi dubu goma .

Kinga kudinta yakama 40k kennan.
kudi badamuwarmu bane mudai ayi komai agama lfy.
zeenat ta kirga 40k ta ajiyesu nan kan tablet din nurse .

Nurse titi ta Mike yasoma harhada aluran kala kala taja su a sirinji tare da nuna zeenat wani guri dake kewaye da labule .

Zeenat ta Mike cikin sanyi jiki tashiga gurin nurse titi tayiwa mata injection guda biyu "tare da bata tablet shima guda biyu tace idan taje gida tasha daya ta tura daya a gabanta da kyau .
"Ta kwanta sbd maganin zaifi aiki sosai ajikinta .
Sannan km idan taga jini karta kuskura tasha ruwan sanyi sai hot water .

Da sauri suka Mike suka bar office din nurse titi saboda lokaci yasoma wucewa kai tsaye inda sumy tayi parking din motarta suka nufa .
suka bude kowanne su yashiga ya zauna .
"sumy tayiwa motar key ta fige motar da gudu ta fita.
,ko acikin motar ma sumy sake jaddawa zeenat take dan Allah kartayi kuskure da wani abu zai faru ,dan duk abinda yaje ya dawo say a nemenita .
kinga Kinsani cikin bala'i.

Zeenat taja numfashi karki damu kawas bbu abinda zai faru say alkhari , addu'a ta a yanzu naganni agida .

Daidai jakonde first get sumy ta sauketa tace to Allah yakiyaye say muyi waya takarasa barin jection din da sauri dan gudun kar mugun ido yaganta .

Da kyar zeenat ke daga kafafunta har ta iso bakin get dinsu securities nata masa sannu da zuwa ,bata tsaya tabi takansu ba .
Burinta bai wuce ta ganta a cikin part dinta ba.

Tana shiga part dinta ta dan tsaya a parlour'n kasa tana sanarwa moris abinda zata daura dan kusan dowarta suke Jira .

Tana shiga dakinta bayi tashiga ta dauro alwala tazo tagabatar da sallar la'asar ta balli table din da nurse titi Tasha sannan ta tura dayan akasanta kmr yadda Ta umarceta.sai da tabbatar da ta tura tablet din akasanta da kyau sannan ta nemi guri ta Mike akan bed dinta tana Jiran abinda zai faru.

Kusan 2 hours ta dauka kwance Amman bata ji wani alamu ya canza ajikinta .dan haka ta Mike tashiga bayi ta duba sam bbu wani abu datagani wanda ya danganci jini sai ainihin ruwan jikinta .

Hankalinka ya tashi ta dauki waya ta Kira nurse titi tasanar mata .itafa bata Ga komai ba .
Tace kibari zuwa can dare mugani dan alluran dana miki duk masu karfi ne da wannan table din nasan kafin safiya cikin zai yi kasa .

Deeni yana shigowa estate din ya dinga Gabansa na cigaba da faduwa da sauri , addu'a yasoma karantowa .da haka ya dan samu natsuwa ,dan kwata kwata yarasa dalilin dayasa yake jin haka da farko ya danganta hakan da rashin lafiyar zeenat byn yakira zeenat din ya tabbatar da lfyrta km still yana jin gabansa na dokawa sam bay taba tsintar kanshi cikin wannan yanayin masallaci cikin gidan ya nufa byn yayi magrib da isha'i yayi addu'a Sosai akan duk ma abinda zai sameshi yazo masa da sauki .

Bai tsaya wani bata time ba ya fito shida fk suna gaisawa sama sama fk na kokarin kowa masa wani zance yace sauri yake kasan madam dina sai a slow . Yayi gaba ya bar fk.

Fk ya dinga masa tsiya wai yanzu yazama mijin hjy sai rawa kai kake akanta ko juyowa DEENI bai yi ba yacigaba da tafiyarsa tare da cewa kai ka sani dan sa ido kawai.

Kwance take akan gadonta ta bude idanunta byn taji shigowarsa ta Mike zaune tare da yaye bargon data lullube jikinta dashi.

Idanunta tsaye akansa tana kallon fine man dinta , tamkar wanda ake sake canza masa halitta da kara masa kyawu .
Kokarin tashi take amman ya dakatar daita da hannushi .yana may karasowa gareta.

'Ahankali ya janyota jikinsa ya rungumeta tsam tsam yana shinshina wuyanta bby ya jiki ta narke masa ajiki.da sauki say day bb'ynka na ban wahala .
Sorry karki damu duk randa ya fito. zan zane miki shi I promise .tayi murmushi tana sake shigewa jikinsa .
Cikinta ta dan ya murda mata ,tasa hannu ta dafe mararta tare yatsuna fuska ,ya kalleta yace lfy ta girgiza masa kai kawai alamun bbu komai.

Yace bari naje showerl daman nazo naga lfyr bby'na ya kwantar daita tare da tmbyrta ko tayi sallar isha'i tace eh sannan ya wuce dakinsa .

Wanka yayi ya dawo dakinta byn ya hadawa kanshi coffee yasha dan kwata kwata bazai iya cin abinci masu aiki ba .

Zuwa lokacin ta kokarta ta Mike tayo wanka tare da sanya kayan bacci tayiwa kanta wanka da turare dan tasan mijinta mayye kamshi ne.

A gaban mirrow ya isketa tsaye yakaraso gareta yazagaye hannushi a kungunta yana kaiwa wuyanta sumba ya amshi kwalbar turaren ya ajiye.

Ya janyota hannuta muje kiji wani labari mai dadi duk ta dago abinda yake so tana rungume ajikinsa har dakinsa.yajata suka zube kan bed yasoma aika mata da wasannisa masu saurin dagulamata lisafi da birkita mata Brain.gabanta say faduwa yake 'ahankali yayi kololuwar tashi dan alokaci bbu abinda ta tsana kmr yace zai yi sex daita.
Romancing dinta yasha yi amman sam taki yarda ta mayar masa martani cikin sanyi yadakata da abinda yake ya zuba mata idanushi,cikin kwayar idanunta yake hango wasu abubuwa wanda yakasa fassara su ,tsawon lokaci ya dauka yana kallonta ganin haka yasa ta wayance ta shige jikinsa tare kamo hannushi ta daura daidai kasan mararta my hrt cikina ke ciwo.
A take 'ya frigice cikinki ke ciwo shine baki sanar min ba say yanzu tashi tashi muje hospital ta zaro idanu waje tana datasanin cewa haka.
Ta sake narke masa Ai naji sauki uhm ke dai kibari muje kawai banason sakaci fa shine first hope dina idan wani abu ya sameshi zanji ba dadi I will blame my self tasa hannu ta dago fuskarsa karka damu bbu abinda zai samu bbynmu ya lumshe idanushi tare da cewa Ameen a zuciyata km tana canza mafar addurta datayi.

Kwantar daita yayi ya rungumeta tsam ya fasa yin abinda ke rashin dan gudun kar wani abu ya samu bby'n.

Basu wani dade ba bacci yayi awon gaba dasu .

Cikin bacci ta dinga ji tamkar ana mintsininta can km taji wani azababen ciwon ciki hannuta dafe da mararta tana murkususu taki tayardashi dan kar Yace suje hospital say cizan lip's dinta take tana yarfe hannu duk sanyi AC dakin hakan bai hana gumi tsatsafo mata ba .

Ta Mike tana layi tayi cikin bathroom din dakinsa tasoma kokarin cire pent dinta abinda tagani ne ya frigita..

MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Page 44

Jini tagani har da gudaji gudaji a pent dinta. Wanda hakan yayi sanadin tsugunwarta kasa da sauri .

tsugunwarta keda wuya taji tamkar ankara mata wani ciwon ne akan wanda take ji.

kmr Jira jini yake ta tsugunna yashiga zubowa " Ga wani irin azababen ciwon data ke ji a kasan mararta kmr zata mutu.

murkususu take sosai tana yarfe hannu.
ta dinga nishi sama sama duk iya duriyar da take dan kar DEENI ya farka ,bai hana Hawaye silalowa daga idanunta ba .

Da azaba tayi azaba kawai say tasa kuka.

Cikin bacci deeni ya dinga jin sautin kukanta 'ahankali 'yashiga lalubar inda take kwance da hannushi .yayinda idanunshi ke rufe ,yaji bai ji alamunta ba ya sake motsowa gaba still bbu ita da sauri ya mike zaune yana bin takin da kallo" km har zuwa lokacin baidana jin gujin kukanta ba.

Hankalinsa ya tashe ya zabura ya mike tsaye yayi hanyar bathroom din dan tanan kunnenshi ke jiyomishi sautin kukanta .

say day yana daura hannushi akan handle din kofar yaji kofar gam a garkame .
ga km alamun Tana cikin bathroom din dan lokacin yana jiyo sautin kukanta Sosai.

A razane deeni ya hau buga fakor da karfi yana kiran sunanta zeenat...... Zeenat.. amman shr taki amsawa sai kuka take .

meke damunki zeenat ki taimaka bude min kofar please ... Duk yabi ya rude ya gigice yacigaba da buga fakor yana kokarin ballata .

Ganin irin azabar da take sha wacce ita tajanyowa kanta gashi idanunta har sun soma rufewa shi km yana cigaba da jijiga kofar hade da kiran sunanta yasa ta rarrafa da kyar ta bude masa yana ganinta haka ya gigice ya shiga tmbyrta
Chapter 40 · 0% Book details