← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 149

Sashe 65

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Ahankali ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun hannunta wanda kusan rashin abinyi ne kesata yin haka.

,haske taga ya garwaye parlour gabadaya 'koina ya dauki haske tamkar rana ce ba dare ba.
wani irin kamshi ne mai azababen dadi yake kusantota ,har inda take zaune ,yayinda mamallakin turaren ke tukarowa parlour zuwa indasuke haka shima kamshin ke kai kawo acikin hancin nablah .
har zuwa sanda mamallakin kamshin ya karasa yashigowa, gabadaya parlour ya canza wani irin cent na daban", take gabanta yashiga dukan uku uku gashi tana san dagowa ta kalli kowaye mamallakin wannan azababen kamshi Amman takasa dago idanunta,dan ko kwakkwaran motse kasawa tayi ballanantana tasan kowaye mamallakin wannan turaren mace ko namiji ne sakamakon kanta dake Duke akasa har lokacin.
Ta kafe teas din parlour da ido ".

Ta kasan idanunta ta hango wando jeans. wanda hakan ya tabbatar mata da mammallakin kamshi turaren nan namiji ne .
"duk da bataga komai nashi , baya ga Zara zaran yatsun kafafuwansa da kowani ke kwance da gargasan gashi.
'ahankali yake takowa zuwa inda ummi take zaune .

Muryar ummi taji tana cewa ka fito son ?
tun da zu muke Jira ... matarka tace wanka kake yi ,'ahankali ya juyo ga mahaifiyarsa yana kallonta sannan yadanyi murmushi gefen baki .
hannunsa yasa ya dauki remut ya canza channel zuwa ta kallon Ball sannan ya Mike kwance kan three site hade da cewa gani first lov anything for you my beautiful mum...
Ummi ta saki murmushi sakamakon jin dadi abinda yace sannan tace kai ko Allah ya shirya min kai ...tare da kai hannuta kai kan tilon dan nata ta shafa tautausar sumar kansa tana jin wani irin sanyi a ranta .

Muryata A dake takira sunansa ' deeni.....
Ya dago rikitattun idanushi yana kallon ummi batare da yace komai ba ...
"maganar mai aiki da mukayi dakai za'a kawo ,to orready ma she's here.. ta iso sauran muji meyye ra:ayinka nidai na amince daita hundred percent ..

kasa kasa yayi da muryasa wanda daman can haka yanayin maganarsa take ..
Kuma yadda yayi magana ummi ce kawai zata iya jin meyace ..

tana ina .......?

abinda kunne nablah ya ji kennan.
gata can ummi ta fada tare da nuna inda nablah take zaune ...

'ahankali ya juyo tare da kallon inda ummi tayi mishi nuni da hannuta. idanunshi ya runtse gam sannan cikin sanyayyayiyar muryasa mai kashi jikin duk wanda tsautsayi yasa ya fada kunne shi " yace first lov... kice ta Mike naganta ..

tsoro da fargaba tare da frigice ne suka taru suka kaiwa zuciyar nablah farmaki" tashi daya taji jikinta yakama rawa gabanta yashiga faduwa da sauri, tasoma tunanin abinda ya kawota wannan gida mai cike da abun tsoro da abubuwan ban mamaki ...

sai kawai ta tsinci kanta da ambato sunnan Allah a kasan ranta da karanto duk addu'ar datazo bakinta Dan rage jin tsoro " take taji wata natsuwa tazota mata aboye ta dinga sauke ajiyar zuciya .

'Ahankali ummi takira sunata nablah Mike tsaye man ya ganki , batare da wata gardama ba,ko bata lokaci ta Mike tsaye kmr yadda ummi tace .Amman still jikinta Bai bar kirma ba haka ma hannuwata suna sarkafe da juna tana cigaba da wasa dasu " yayinda ta cikin hijab dinta kuwa uhmmmm tashin hankali kennan 'dan kuwa jikinta sharkaf yake da gumi tsabar frigici datake ciki ,duk da tsanyi AC dake aiki a parlour hakan bai hana gumi tsassafowa ilahirin jikinta ba .

idanunshi da Suke a runtse ya kafeta dasu yana kallonta ,jin shr,n da yayi yawa ne yasa nablah dago fararen idanunta dan satar kallon mutumin dataji an Kira da suna DEENI . take zuciyoyinsu suka buga a lokaci daya .......

Yayinda jikin nablah ya dauki kirma... zuciyarta ta sake amsawa daf..daf..daf.. 'da sauri tayi kasa da idanunta ahankali ta furta wayyo Allah na.. a kasan ranta.. mutun ko aljani nake Gani yau .

, tsabar kyauwu halitta da Allah yayi masa .tunda take a rayuwarta bata taba ganin mai tsananin kyau halitta da kwar jinin irin mutumin da take gabansa tsaye a halin yanzu haka ba .

kusan tsawon minti 5 ya dauka yana kallonta batare daya bude Idanunshi ba" sannan 'ahankali ya dauke idanunsa daga gareta yakoma ya kwanta sosai acikin kujerar dayake "ummi tace ya'akayi ne DEENI naji kayi shr... ....

Tayi.....
.
abinda kawai nablah ta iya ji kennan daga bakinsa , Dan gabadaya ma jitayi kunneta ya daina jin magana tsabar tsoro da rikici hakan km sai lokacin hankalinta ya dawo gangar jikinta daga mummunar damuwar data tsinci kai ciki ...
Amman fa duk da Haka a tsorace take da mutumin dake kwance a gabanta .

,ummi kuwa ta furta kalmar alhamdulilllahi yafi Sau dari kafin daga baya ta kalli nablah a tsanake sannan tace jeki nabla ma hadu gobe kinji ..

,muryarta nablah a sarke tace to ... sai da safenku sannan ta juya cikin tsanyi jiki ahankali take tafiya yayinda itama ummi ta juyo tana sake bin bayan nablah din da kallo har tabar parlour zuciyarta na karanto mata abubuwa dayawa game da yarinyar ga wani irin tausayin yarinyar daya mamaye zuciya ...

Bangaren deeni kuwa gabadaya ji yayi tamkar am masa wanka ne da ruwan sanyi , jikinsa ya mutu murus tamkar mara lfy haka ya dinga ji ajikinsa tun sanda yabi hannu ummi da ido .

kwarai yaso ya bude idanunshi yakarewa yanayinta kallo Amman sam yakasa aitawatar da hakan , sai ma tsintar kansa da yayi da mummunar faduwar gaba a lokacin da yake kallonta .
, wanda har yanzu dayake kwance a wajen bai daina jin yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri ba ..

'ahankali yasake runtse idanunshi gam ko zai daina jin abinda yake ji ajikinsa ,amman kwata kwata sabanin haka Ya dinga ji .
Sai ma zuciyarsa da tacigaba da harbawa da sauri da sauri .

abinda bai taba ji atare dashi ba kennan tun iya tsawon rayuwarsa wai faduwar gaba akan mace ....
Macce ma , mai matsayin mai aiki ...

ahankali ya furta sunan da yaji umminsa takira yarinyar dashi nab....lah... Yadda ba mai jinsa ....

muryar matarsa yaji tana cewa ummi ai wannan yarinyar bakaramin daga tuta tayi ba , tunda har my hrt yace tayi.

ummi tace al,amarin Allah kennan nima gsky naji dadi matuka da tamasa saboda daganin yanayin yarinyar ba tmby akwai natsuwa atare daita .
kema kiyi kokarin ki sota a ranki " ba mamaki wata rana tayi miki amfani .

" dagani bazamu samu matsalar daita ba ", zeenat tayi murmushin karfin hali tare da kwabe baki Dan ita kwata kwata bata ji son yarinyar aranta ba . tanaji a zuciyarta tamkar ta sallameta daga gidan ne yanzu yanzu ....

Muryata Cike da takaici tace wani amfani km ummi .Allah yakiyaye wannan yarinyar tayi min amfani .
ni wlh Dan bani da iko ne.
tunda kince ta kwanta miki a rai .
wlh da tuni korarta zanyi. Dan Haka kawai nake jin tsanar yarinyar har cikin raina .

deeni dake kwance ya ja tsaki mai tsawo..Dan takaicin maganar Zeenat din sannan ya Dan juyo ya tsareta da rikitattun idanunshi masu sata natsuwa a duk lokacin daya watsa mata su.

take tayi shr ta hadiye maganar ta ,sannan yace I don't want to hear anything stupid here.
A Zafafe yacigaba magana haba kin cikamin kunne da shirme banzan ki .

sannan ya dan sausauta murya tunowa da yayi ummi natare dasu ,cikin sanyi jiki ya juyo suka hada Ido da ummi . itama shi ta zubawa idanunta kawai .
Cikin sanyi ya kamo hannun ummi cikin nasa yana mai karkada mata kai 'ahankali yace am sorry...my first lov .

take ummi taji wani irin sanyi a ranta , gashi bata iya fushi da tilon dan nata, Kuma bata son damuwarsa ,gara ace duk abinda zai same shi ya tsaya a kanta.

" hannuta tasa ta dungure masa kai dashi " tace kai dai kacika maseefa wlh ai barewa batayi gudu ba danta yakasa rarrafe like father like son ai lokacin aliy ..... ganin ummi zata soma tabo labarin dad dinsa yasa yakatseta da hanzari muryarsa cike da shagwaba yace please first lov ya nuna mata yatsansa alamu tabashi 1 minti sannan ya juya inda zeenat ke zaune ta kasa kunne, kallo daya yayi mata wanda yasa ta gane abinda yake nufi tun kafin yayi magana ta Mike tsaye 'ahankali tabar gun.

hade da cewa maseefafe banza kawai akasan ranta in maseefarka ta motso kowa yashiga uku acikin gida.

sai da ya tabbatar da Zeenat tabar part din gabadaya sannan yace ok continue first lov ummi ta tabe bakinta sannan tace anki ayi continue din.
dan saboda za'a yi maganar dad dinka shine ka koranmu yarinya.

A shagwabe yace haba first lov a gabanta zakirinka jistin din abinda dad dina yayi ya girgiza kai impossible.... Ai zaki sa ta raina ni .
Ummi Tasaki murmushi ganin yadda ya hade rai kmr mai shirin kai gumurzu sannun gyenbo sarkin son girma aiki DEENI ya yamutsa fuska jin abinda ummi tace murmushi tayi nan dai suka cigaba da hira su ta tsakanin uwa da "da" .....

Koda nablah ta koma dakin daaka sauketa ciki ,key tayiwa kofar saboda tsaro ,sannan ta cire hijab din jikinta ta tsaya tana bin jikinta da kallo yadda take ajike jagab da gumi tana tsiyaya ,dariya ce ta kufce mata, ai kuwa tashiga yiwa kanta dariya ,sosai tayi dariya har da rike ciki saboda tuno yadda ta koma kallar tausayi dazu a parlour.
,a hankali ta zare kayan jikinta dayake doguwar riga ce "ta daura zaninta data zo dashi tashiga bathroom..
Chapter 65 · 0% Book details