Sashe 1
Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Compiled by Umar Dalha Funtua.
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗
Bismillahirahmanurrahim
Aysha A bagudo
Page 1-2
Lekki Unguwace mai dauke da karancin mutane da suke rayuwa acikinta ,a silent place, saboda bata cika hayaniya mutane ba , dauke da tarin sanyin ni'ima mai dadi sakamakon kusancinsu da ruwan teku" unguwace da tattara kan manya ma'aikata da kusoshin gwanati, hade da manyan masu kudi ,ga tarin yan yahoo boy'z domin mafi yawancisu sunfi sha'awar zama acikinta. rayuwar mutane unguwar abin sha'awa bbu ruwan wani da wani domin suna rayuwasu ne tamkar a kasar waje .
PLASNUW ROWS FAMILY ESTATE
Estate ne mai dauke da tarin dangi acikinta , hadin kai tattare da zaman lfy, Sam bbu hayaniya acikin wannan family kowa kagani cikin nishadi da farinciki zaka gansa ,ga tsantsar fahimtar juna dake tsakanin wannan family. kwakkywan family ne masu matukar kaunar junansu .
Let alh Muhammed bello khaliyal ,haifafen garin Lagos ne ,Amman asalinsa fulanin khaliyal ne dake jahar kebbi. sananne mai kudi ne yayi tashe tun alokacin da duniya ke kwance. sannan kuma take zaman lfy, marigayi Muhammed bello soldier ne daya taka rawar Gani a kasar nan .
ya rike mukamai da dama a wancan lokacin. ya rasu yabar tarin dukiya da da ya'ya da jikoki bila adade.
gabadaya family Muhammed bello bbu talaka aciki domin sun gaji dukiya mai tarin yawa daga mahaifinsu .
kafin rasuwarsa dake shine babba a dakinsu kuma Allah yabashi tarin dukiya da en'uwan , dan ganin ya inganta rayuwar kannensa kafin daga baya ya Gina wannan katanfarin estate din mai mazan kanta.
ya tattara kan yan'uwasa suna zaune a ciki ,yana da mata hudu hjy shema'u wacce aka musu aure tun saurayi da budurwa tana da ya'ya goma Sha biyu, mata takwas maza hudu sai hjy hauwa mai dauke da ya'ya goma maza biyar mata biyar ,sai hajiya rabi mai ya'ya takwas maza biyar mata uku sai hajiya Fatima wacce suke kira da hjy shuwa itama tana da yaya takwas mata bakwai namiji daya .
bbu abinda bbu acikin wannan estate din kama daga makarantar islamiyya wajen wasa buga kwallo wajajen exercise wajen swimming pool library Sannan ga wani katanfarin Holl dake gefe wanda aka shiryashi da kayan kyale kyale zagaye da kujerun zama . an ginashine saboda taron sada zumunci , wanda zasu dinga yi a duk karshen wata .
haka suka taso har zuwa girmansu cike da son junansu .
anan cikin dangi mazan suka zabi matan suma matan suka zaba akayi bikinsu anan cikin estate din suka zauna tare da iyalinsu har zuwa sanda tsufa yacima marigayi Muhammed bello yayi retire.
yayinda ya'yansa da ya'yan en uwa suka cigaba da kula da estate din .
a lokacin aliyu da habib ne kadai suka rage da basuyi aure ba saboda karatu .
Byn rasuwar marigayi bello ne aka raba gado aliyu ya dukufa gurin juya dukiyarsa ,ba abinda yasaka a gaba sai neman kudi wanda acikin kankani lokaci ya gawurta yayi fice yayi suna a duniya, yayiwa sauran yan'uwansa zarra aliyu ya mallaki tarin dukiya da shi kansa bai san iyakarta ba. hade da tarin compenis a Lagos da kudancin Nigeria yana da gidajen saida man petir Bila adadi shine mallakin aliyu airlines yana da hannu jari da dama a compenis na kasashen duniya yana da gidaje a abuja da sauran garuruwa .
tsananin neman kudinsa ne yasa bai ajiye iyali da wuri ba ,burinsa bai wuce ya auri mace mai matukar kyau da tarin illimi ba .
Garin neman kudinsa ne ya hadu da fadila a india tun daga lokacin da aliyu ya daura idanunshi akanta "ya dauki son duniya ya daura mata kasancewarta kyakkywa gaske ga tarin illimi . fadila itace Diya ta biyu a gurin iyayenta su uku ne , ahmed ne babba sai ita sai farida , kin amincewa iyayenta sukayi da auren shi a cewarsu bako ne sannan kuma bakin fata. sai da aka kai ruwa rana dasu sannan suka amince da auren .
koda yazo daita Nigeria ma bata wani sha wuyan zama cikin family dinsa ba .
kasancewarta mace mai tsananin son jama'a da son yara cikin lokaci kadan tashaku da sulaiman da mahamud ya'ya ne ga yayyen aliyu sun shaku matuka da yaran ta daukesu tamkar ya'yan data haifa acikinta .
suma kuma suna maseefar kaunarta dan haka suke kiranta da ummi ,duk abinda suke so itace take musu bata ragesu da komai ba saboda bata da rowa hakan ne yasa ta sake janyo mata soyayya ta daban a gurin iyayensu.
shekarata biyar da aure mutuwar mahaifiyar ta risketa ,zuwan datayi indiya ne dazata dawo tazo da kanwarta fadila ta hada dasu Mahmoud tacigaba da rikonsu .
sai da fadila ta dauki sama da shekara takwas da aure sannan tasamu cikin murna a wajen wannan family bai faduwa .
cikinta na da wata tara cif ta haifi NASURUDEEN daga ita har aliyu suna matukar son DEENI tamkar numfashinsu DEENI yataso cikin gata da kulawar iyayensa, da dangi gabadaya suna nuna masa tsansar gata da soyayya fiyye da tunanin mai karatu .
shiyasa yataso a shagwabe a sangartacce saboda kaf estate din kowa yasan da zaman DEENI babbar matsalar da suka fara fuskanta da deeni , shine rashin magana da bai yi ,da farko fadila ta dauka ko kurma ne sai daga baya tagane tsabar miskilanci ne kawai yayi masa yawa .
duk tarin ya'yan dake cikin wannan estate din DEENI yafita dabam acikinsu, bashida aboki ,.
gabadaya baya yarda da kowa koda yaushe yana tare da umminsa ko farida ko su Mahmoud tun tasowarsa yake da burin son zama soldier yayinda ummi take bashi goyon baya wajen kiransa soja .
Domin wani lokacin zai je yatasa hotonta marigayi kakansa dake manne a falonsu gaba yayi ta kallo yana shafa fuskar tsohon yana murmushin ,Sam shi bashi da fara'a ballanantana sakin fuska koda yaushe fuska nan tashi a hade take tamkar hadari , .DEENI Nada shekara takwas byn yakare primary school aka sai mishi form din shiga makarantar sojoji ba'awani samu wata matsala ba yasamu sakamakon matsayin mahaifinsa da kakansa. sabanin wayanda basu da gata.
domin a wanan lokacin idan dai kai bawani bane ko dan wani ba ko bakada hanya a military school ,sunanka sorry.
Domin kuwa kana ji kana Gani military school zai gareka shiga .
byn wani lokacin farida ta samu miji anan cikin estate din wanda shima yakasance "Da"ne ga marigayi Muhammad bello wato habibu ubansu daya da aliyu mahaifin ga DEENI .
duk da fadila ta nuna rashin amincewarta matuka , da nuna wa er'uwartata illar aurenta da Habib Amman sai taga yarinya ta nuna tana so abunta ,dan haka ta kyaleta kuma da kunya dai ta fito fili tace batason jinin aliyu ,wanda itama kanta tasan hakan ba mai yiwu bane . itama ba wai shi din ne bataso ba ,halinsa ta tsana ,
Amman shi babban ma'aikace gwanati ne, director of land and housing & same na Lagos state gabadaya. yana da mata biyu da yaya bakwai farida ce ta uku .
Ko alokaci daya auri farida takasance mace ce mai tsananin hakuri .
duk da mijin nata Vai kasance mutun mai adalci ga iyalansa ba. Amman bata taba kawo kararshi ga ummi ba domin tasan halin ummi Sam bata son raini .
Shekarar da aka yiwa sulaiman da mahamud aure shekarace Allah yayiwa mijin ummi rasuwa wato alh aliyu Muhammad bello sunji matuwar farar daya , mutuwar tayi matukar gigita ummi dan byn ya dawo daga sallah asuba ne yayi irin kishingide nan yana lazimi koda ummi taji shiru shiru bai sake fitowa ba Sannan bai nemeta ba kmr yadda ya saba , wanda aldarsa ce da zarar gari yayi sha ...yake fitowa ko yakirata a waya Amman taji shr .
tashiga dakin nasa ta tarar dashi kishingide da carbi a hannunsa .
da fari ta dauka ko bacci yakeyi sai tayi nufin ta tasheshi yakoma kan gado.
Ammai sai taga alamun rashin motse atare dashi takai hannuta wajen hancinsa da karjinsa a lokacin daya taji baya numfashi.
take ta zube anan ta sume.
har a kashare zaman makoki ummi batasan a wani hali take ba ,dan bata cikin haiyacinta' koda ta farfado ma sai da akayi ta hadawa da addu'a Sannan aka samu kanta ta dawo daidai , dan mutuwar ta girgiza har ta kusan zarar daita .