← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 149

Sashe 147

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

banda kuka bbu abinda zeenat keyi ita kanta tasan ta cuci kanta da kanta.
Ta ruguza rayuwarsu sbd sakacinta da son zuciyarta ta Mike Daga inda take ahankali tana layi ta rungume ummi ajikinta tana matsanancin kuka.
Ummi kiyi hakuri a rayuwa nasan Na cutar daku Amman ko daidai rana daya ummi baki taba kina ba .
Sai ma sabuwar kulawa da kike bani hakika ke uwace guda har da rabi samun irin Ku ahalin yanzu zai yi wuya ummi kiyi hakuri abida nayi ki ya femin Na cutar dake domin ba irin tarbiyya da kika bani ba kennan ta sake tsanata kukanta.
ummi itama ta rungumeta sosai tana zubda hawayen tausayin diyarta arayuwa ta tsani abinda zai saka zeenat dinta zubd hawaye matukar tana da yadda zatayi.
kasa cewa komai tayi Sai aikin rarrashita datake tana shafa bayanta ..

Ahankali deeni ya dauke idanunsa akansu ya juyo sosai tare da gyaran zamansa yana fuskantar nablah da kyau ya kaskantar da kanshi da muryarsa agabanta yana nuna mata shin din bakomai bane facce me nema agurinta .
a wannan fani har ya mance dako su waye tsaye akansa.
Domin Bai San sanda ya kamo tafin hannunta 'cikin sanyi jiki ba yana kallon 'cikin kwayar idanunta muryarsa cike da rauni zuciya tare da mayyen sonta ya Kira sunanta.. nabeelah ...kiyiwa Allah ki mallaka mana bbys din nan.
badanmu ba Sai saboda Allah ki duba tashin hankali da zanshiga akan yaran nan .
sannan ki duba halin da mahaifiyata da matata zasu shiga ki tausaya nablah ki duba yadda mahaifiyata tagama gayawa duniya akan nida matata muka haifi bbys din nan .Kinsa idan akaji sabanin hk zatashiga tashin hankali da rudin rayuwa ..
nablah nasan kina da saukin Kai da sanyi hali hade da hakuri akan komai Na rayuwa .
Na rokeki da Allah kibarwa zeenat bbys din nan .
Allah zai duba lamarinki ya sake baki wasu da yardarsa ...
a fusace ta fizge hannuta 'cikin sauri Daga nashi tana jin takaicin mgnrsa . ..

Kana ji har mara hankali matarka ta kirani dashi akan ya'yan dani kadai nasan kalar wahalar dana Sha akansu tunda Daga cikinsu har zuwa haihuwarsu.
idan har nabar mata yaran nan wallahi azim Na tabbata mahaukaciyar gaske deeni .
zeenat ta bar jikin ummi tamatso gareta sosai tana kuka tana rokon nablah.

ZUCIYAR deeni tasoma rawa yasoma jin Wani irin ajikinshi hakika ya tausayawa zeenat duk da yasan itace silar rugujewar rayuwarsu da yi musu katangar karfe da burin ransu km farincikinsu Amman fur nablah taki amincewa tare da cewa aunty kiyi hakuri wlh nima Ina son ya'yana.
idan nabaki su ni km yazamanto su kadai ne ya'ya da zan haifa a duniya ni km Sai nayi ya'ya ?

Kiyi hakuri kawai kema Allah zai baki naki da yardarsa Amman zance nabar miki ma su yanzu bbu shi .

kibar min nawa nayi rayuwa dasu , sune duniyata ayanzu bazan iya rayuwa bbu su ba .

deeni ya juyo a tsukwane ya kafe zeenat da idanushi yana kallon yadda ta dawo wata kala abar tausayi bbu wuya tashin hankali ya canza mata kammani .
Ummi takaraso ahankali itama ta zauna kusa da nablah ta dinga bata hakuri da yima dabarunsu irin Na manya da siyasa iri iri Amman fur nablah taki Sai ma fashe musu da sabon kuka datayi ni kibarni Haka Dan Allah Dame zanji .
yanzu zan bar muku gidanku akan na bada yaran nan gara na komai
kan bola Na rayu dasu 'cikin kulawata .

gabadaya deeni yasoma tsorata da yanayinta har yasoma aikawa kwalkwaluwarsa tmbyr Anya kuwa wani abu Bai samu brain dinta ba kuwa gurin haihuwa ?

Sosai Ya xuba uban tagumi tare da jefa Dan karamin yatsansa 'cikin bakinsa yana cizawa da karfi yana kallonta yana nazarin reaction dinta ..
sosai ya jima yana kallonta kafin Daga bisani yace first love barta kawai akawo mata abinci yaci da alamun tana jin yunwa tun da muka shigo gidan nayi nayi daita taci abinci taki ci a she rigima take ji shiyasa.
jikin ummi a matukar sanyaye tace zeenat goge Hawayenki ki natsu kada mutane su gane Muna 'cikin damuwa da matsala.
muje maza ki kawo mata abinci ni zan Dan tsaya saboda kauda idanun mutane akanmu.

Tare suka fita .
ummi Na sake rarrashinta akan ta kwantar da hankalinta ..

Suna fita deeni ya juyo gareta ya hade da jikinshi ya rungumeta zuciyarsa Na harbawa da sauri da sauri .
tare sa sakin naunauyen ajiyar zuciya bakinsa yakai daidai saitin kunneta sosai.
Yace Na yaba da jarumtarki Na yaba miki da yadda kike son baby's dinmu .
daman Haka yakamata duk wata uwa tayi akan yayanta .
km hakan da kika yi ya sa naji kin birgeni sosai. Sai dai me zai hana ki tausaya kibarwa zeenat dina baby's din please zata kular miki dasu ..ki tuna sanda kike kuka kike rokona akan azubar da ciki Na hana batare da saninki ba .
ki tuna irin taimakon dana miki akan ni zan karbi 'cikin da bansan wanda Yayi miki ba domin gujewa kunyar duniya
Da karfina da dukiyata duk sa sadaukar akan Na inganta 'cikin jikinki da rayuwarki .
Amman kirasa abinda zaki sakayyar min dashi .
Sai hanani bbyn dana gama wahala akansu.
Meyasa zaki min hk ? Yakarasa mgnr da
Ki bar mata sake of me please nablah zanji dadi idan har zaki iya min hk .kina jin yadda zuciyarata ke bugawa da karfi akanki .
,akanki zan iya yin komai ciki har da fallasa sirrin dake boye wanda hakan bazaiwa first love dadi ba.
please nablah sake of me jikinta Sai kirma yake tana zubda ruwan hawayen tausayinsa muryarta a dashe tace nasani deeni kataimaka min a rayuwa km zan iya yi maka komai a rayuwa Amman bazan iya kyautar yaran nan Ga kowa ba ciki kuwa har da kai ..
Ni kaina Haka kawai Na tsinci zuciyata da matsanancin kaunarsu tunda Na daura idanuna akansu .kasa samun natsuwa .
Ya zanyi nabaku kennan ni zauna hk ?
Byn tarin wahalar dana Sha akansu .
ahankali ya sausauta rungumar da Yayi mata ya ciro hanky Daga gaban aljihun rigarsa yashiga goge mata hawayen dake tsiyaya akan kuncinta .
bakinsa ya Kai kan lips dinta ya tsotsa yana kallon 'cikin idanunta .
Lumshe shanyayyun idanunta tayi tasoma kokari cire bakinta Daga nashi .
Jikinsa a sanyaye ya xuba mata rikitattun idanunshi kawai yana kallonta yana imagine dinta.
har sanda zeenat ta dawo dakin hannuta rike da cool food flasks da flasks din ruwan zafi da plate ..

Deeni ya janyo wata Yar karamar stood tsakiyarsu ya bude cool da zeenat tashigo dashi.
miyar dayafi tsana arayuwarsa yasoma cin karo dashi wato miyar kuka wace Tasha naman kaza da kayan kamshi makewa Yayi ya ciro karamar ta sama ya ajiye yacigaba da bude cool yaga tuwan samiviter ne aciki Whit lailon ya ciro tuwon yasaka akan plate ita km zeenat jiki Na rawa ta hada mata tea me kauri ta mikowa deeni.
" ya karba ya ajiye a gefen plet din.
abin zeenat nabashi mamakin sannan km yana jinjina girma al'amarin.
lallai sanadin wayan nan baby's din Yasa zeenat dinsa tasoma sauya halinta wanda yajima yanasonta dashi .

Muryarsa a matukar sanyaye yace Bismillah nablah kici abinci .
taki ci ta xubawa masa idanunta ya Mika mata cup din tea shima taki karba.
Yayi shr ya tsura mata rikitattun idanunshi bazaki ci abinci ba ?
Ta girgiza masa kanta alamun eh saboda kina tunani zamuyi poison naki ko ?
Tayi saurin sake girgiza kanta to meyasa bazaki ci ba alhalin nasan kina jin yunwa ?

Muryarta a shagwabe tace nifa bance zakuyi min wani abu ba .. zeenat kawo min spoon.
.
Zeenat ta juya da sauri taje takawo masa spoon ta Mika masa .
mamaki ne yakama zeenat Ganin deeni yasoma tura tuwon samiviter da miyar kuka abakinsa the most abincin dayafi tsana kennan arayuwarsa ballanantana dai miyar kuka wanda ko sunan miyar akafada agabansa Sai ya yatsuna fuska tsabar baya sonta .
Amman yau shine zaune yana ci hankali kwance dago rikitattun idanunshi Yayi masu tsantsar cike da tashin hankali ya daura akan nablah dake zaune tamkar an dasata tare da yi mata alama da spoon din hannunshi .
, zeenat tasoma itama sosai ta tsoma hannuta sbd ganowa datayi lallai nablah bata yarda dasu ba.
tasoma ci Sai da nablah ta tabbatar dayaci sosai hk ma zeenat sannan ta tsoma hannuta ciki tare da yin bismillah tasoma ci ahankali aranta tace idan ma mutuwarce ba zan mutu ni kadai ba Sai dai abarwa ummi baby's din .
ko tea din ma kin Sha tayi Sai da zeenat Tasha deeni yasha sannan Tasha itama .
deeni ya kalleta yana tabe baki girgiza Kai .
sbd muraran km azahirance nablah ke nuna kuruciyarta a filli . Idan har wani abu zasuyi mata .
Ai tayi kadan ta kare kanta .

number wayar ummi deeni yakira .
Byn kmr minti goma Sai gata tashigo dakin first love yakama ayiwa yarinyar wanka hk fa da duk abinda yadace.
ko bakace ba deeni duk za'a yi mata daman wannan tashin hankali ne Yasa nakasa samun natsuwa nayi mata ai nablah tamkar diyar cikina Na dauketa .

Da zai fita ya janyo hannu zeenat ya nufi dakinsa daita ya rungumeta tsam tsam ajikinshi zeenat yakira sunanta Ina so ki tattaro natsuwa ki sanyawa gangar jikinki sannan ki kwantar da hankalinki da sannu zan shawo kanta 'cikin sauki batare da wani hargitse ba har ta amince .
domin wannan harbin iskar da kike da tashin hankalin ba zai saka tabada ya'ya 'cikin sauki ba .
as far as tasan wahalar daukar ciki da radadin haihuwa kema kinsa bazai yiwu a karbi yaran 'cikin sauki ba.
ki dinga lallabata ta yadda taza yarda ta amince da ba cutar daita da yaranta zakiyi ba ..
Chapter 147 · 0% Book details