← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 149

Sashe 63

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummi tace yauwa shine kin iya rubuto?
Sai da Aunty salam tayi murmushi sannan tace ba laifi .
ok bani minti biyu na kira securities din get din.
" za su tambayi sunanki aunty salam tace to ....

Nablah ta zubawa hadadden get din gidan idanunta kawai wanda basan yadda zata iya kwatanta girman sa ba ballanantana tsawonsa .

sai dai zata iya kiran get din da JAMA GET ..wato na gidan bursunan dake garin Lagos KIRIKIRI .

daya daga cikin securities din get din ne ya dan leko ganinsu tsaye ne yasa shi cewa madam can i help you?
who are you, looking 4 duk a tare ya jehowa auty Salmah tamyr dayake itace kusa dashi.
,
the person we are lokin 4 said we should Wait 4 her "inji cewar aunty Salmah mutumin yace or rigth sannan yakoma mazauninsa "

can ya sake lekowa yace are you salmah ?
"auty Salmah ta daga masa kai .
'yace ok you can come in.
tare da bude musu Dan karamin get suka shiga ya nuna masu ,wani gurin yace inter and rigth ur ful name down
,Can u write ya sake tmbyr Aunty Salmah.
tace Eh.
byn sunyi komai har da sign sannan ya sake bude wata kofar yayi gaba yace su biyo shi a baya.

daidai wani katanfarin gida mai dauke da tampal ,wanda duk gidanje wajen kusan haka gininsu yake iri daya Kuma sun kai guda hamsi a jere , banda new buildings da ake sakeyi km kowanne gida da number a jiki,..
no 20 ya nuna musu da yatsansa yace this is the place sannan ya juya.

Ahankali suka isa ga kofar daya nuna batare da bata lokaci ba sukayi nouking, wata mata ce da bata wuce ki mananin shekaru ashirin da takwas zuwa talatin ba tazo ta bude musu kofa hade da yi musu sannu da zuwa.

wani hadaddin falo may maseefar kyau ya kawatu da kayan kwalliya wanda yasha kyau ya gaji da kayan more rayuwar duniya .
, sukashiga hade da yin sallama , ga wani kamshi na musamman dake tashi ta koina a parlour, wani irin sanyi ne ke ratsa musu tsantsar jiki .
take duk wani zafi rana da gajiyar hanyar da suka debo suka nemata suka rasa ...

wata dattijuwar mace ce zaune bisa kujera dake zagaye da parlour ,hannunta rike da waya, duk da ba wai saninta nablah tayi ba Amman take jikinta yabata da ita suka dinga commincating a waya da auntyta .

kallo daya nablah da ummi sukayiwa juna" take gabansu yashiga faduwa a tare zuciyoyinsu ya amsa dummmmmm na minti biya kafin daga baya ya dawo daidai.
,wani bakon al,amari ne , yashige su a tare wanda dukkansu basu san dalilin jin hakan ba. a wannan kallo da nablah tayiwa ummi ne, tagane yadda take jin dadin duniya .
Ga km tsabar jin dadi da hutu na musamman da ya bayyana a jikinta .

Gaban nablah yacigaba da faduwa yayinda Koina na jikinta ya dauki kirma .... musamman zuciyarta da taji tana dokawa da sauri.

Da fara,ar ummi ta tare su ,tana musu , sannu da zuwa tare da nuna musu wajen zama da hannuta zama sukayi suna gaida ummi .

sannuku.. kunsha rana Amman Kuma kunyi sauri wlh ai nayi mamakin da kika ce kuna first get.

aunty salam tayi murmushi sannan tace nima wlh haka nagani .
,yayinda ita km nablah ke zaune abunta Tana raba idanuwa tare da karewa koina na parlour da kallo .

Ajiyar zuciya kawai Ta dinga saki 'ahankali 'ahankali domin , irin gidanje datake gani a TV ne wai yau take zaune acikinsa, km har zata zauna a cikinsa ta cigaba da rayuwata zuwa na wani dan lokaci , .

'Ahankali ta maida shanyayun idanunta inda ummi ke zaune tana sake dubanta da kyau , girgiza kanta kawai Tayi tare da yin zance zuci, cikin haka ta tsinci kanta da yi musu addu'ar hakika wasu sun zo duniya a sa'a, Allah yasa lahirar su tayi kyau 'ahankali ta maida kanta kasa ta sunkuyar tana wasa da Zara zaran yatsun hannuta masu matukar kyawun gaske.

Suna nan zaune a gurin aka shigo musu da abin sha ,ruwa ne may tsanyi da malt sai kayan fruit wanda suka dauki tsanyi suma.

, km duk nablah Tana ganin hakan ne a zahiri aka ajiye agaban su, hjy ta gyara zamanta tare da kiran sunan aunty Salmah .... salmah ko?
Aunty ta dagawa ummi kai kawai .
, wannan ita yarinyar kennan?
murya auty salmah ne ya daki kunne nablah .
eh itace hjy .

'Ahankali ummi ta saki ajiyar zuciya sannan ta dauki wayarta dake gefen kujera takira zeenat .

minti kadan byn kiran wayar da ummi tayi, nablah taga wata kyakkyawan mata ta fito daga wani bedroom wanda da alamun muhalinta kennan itama kana ganinta kasan naira tasamu gidin zama ajikinta tafiya take tamkar bazatayi ba, sai rangwada take tana zuba kamshi jikinta sanye da Riga da sike na a tamfar super exclusive kayan sun zauna ajikinta das.
,Takaraso . ta zauna kusa da ummi batare da tace komai ba ,yayinda fuskarta take a daure bbu wani annuri tana kallon nablah dake zaune a gefen aunty Salmah taji wani abu ya dungule mata a kirji, gabanta yashiga faduwa 'ahankali ta dauke idanunta daga kan nablah ,tana sake jin faduwar gaba.

'Ahankali ummi ta numfasa sannan ta cewa Aunty Salmah kice yarinyar ta Mike tsaye mana .
" tun kafin aunty Salmah ta bawa nablah umarni ,ta Mike tsaye cikin sanyi jiki wanda kusan yanayina kennan akoda yaushe.
Amman wannan karan yafi na kowani lokaci Dan gabadaya ilahirin jikina ya sake yin sanyi
,daganin irin kallon da zeenat ke mata .
dan haka gaban nablah yacigaba dukan uku uku kallon tsaf ummi tayi mata sannan ta lumshe idanunta .
ita kuwa nablah tunda tayiwa ummi da Zeenat kallo daya ta dauke idanunta daga garesu bata sake kallon Ida suke ba , domin hakan yana cikin nasihar da auntyta tayi mata kafin su fito daga gida .

Nablah kina ganin masu kudin nan iyayi ne dasu gashi mafi yawancinsu "basuson shishigi dayawan kallo.
ki zauna lfy da duk mutane gidan, kitsaya a matsayin ki ,abinda ya kai ki shi zakiyi dan Allah nablah karkisa naji kunya a in da zan kai ki kinji Yar kanwata ...

' Ahankali nablah ta dawo daga tunanin data tafi na wucin gadi tare da dago shanyayun idanunta tana sake kallon matar data shigo saboda jin sautin muryarta mai cike da tsabar iyaye wanda dagani har da iskanci aciki .

Ummi kina ganin yarinyar nan kuwa zata iya aikin gidan nan ? Sai naga kmr tayi karama
Amman dai ...sai km tayi shr ta Mike tsaye tare da cewa .
ummi zo muyi wata magana dake.

Ba musu ummi tabi bayanta byn sunshiga wani daki dake cikin dakunan dake kasa ne , Zeenat ta sauke ajiyar zuciya sannan tace
,
,Gsky ummi ni fa kwata kwata yarinyar nan banji ta kwanta min a rai ba haka km tunda ake kawo masu aiki gidan nan, ban taba jin yarinyar da naji tsanarta farar daya a zuciyarta ba kmr ta ,Dan haka ummi kibari suyi tafiyarsu kawai .

Ni asona ma , da abar laraba , kawai ta isa ba sai an karo wata ba ,tunda tana yin komai yadda yakamata.

,ummi ta girgiza kai byn tagama jin Zeenat din tsaf..,ni km kinga Ina ganin yarinyar naji ta kwanta min wlh.
kema kiyi kokarin ta miki tamkar yadda naji araina kinji diyata , ba'a saurin tsanar mutun , km ,da alamun akwai natsuwa a tattare da yarinyar .
Zeenat tayi shr tare da kwabe baki kawai takasa sake furta komai ,.
Har Suka dawo parlour.

tasan tunda yarinyar tayiwa ummi magana takare .

ummi ta zauna tare da sake duban inda nablah da Aunty Salmah ke zaune , sai data numfasa sannan tasoma magana kmr haka gsky yarinyar tayi sai dai Kuma ajira zuwan may gidan muji me zai ce akanta , idan Tayi masa zakiji ni a waya ,idan km akasin haka ya faru ,Shima zakiji .
, nablah ta runtse idanunta kirjinta ya shiga bugawa jin sai wani yaganta sannan za,a dauketa aiki .
bayan duk wannan kallon kurulla da'aka tasa gaba da shi .
,nan gaba km sai an sake kawo mata sabon rainin hankali .
na hada da Kato ya ganita.
, tsuke dan karamin bakinta tayi tana mai jan tsaki acikin xuciyarta .

Aunty Salmah tace bbu komai hjy duk yadda kika yi daidai ne 'ahankali ummi ta sauke ajiyer zuciya .. tare da saki murmushi jin dadi.
, Sannan tace baku ci komai ba.
aunty Salmah tayi murmushi itama sannan tasa hannu ta dauki malt ta bude Tasha kadan ta,ajiye amman ita nablah kasha komai tayi Dan bataji zata iya sakawa cikinta komai ba balle ruwa gabadaya hankalinta a tashe yake da jin furucin ummi na karshe .

sake fuskantar Aunty Salmah da kyau ummi tayi , akwai check up da',ake wa sabbin ma,aikatamu saboda sanin ingancin lafiyar su ,so itama za'a mata da fatan hakan bazai zama da wata damuwa ba.

" Aunty salma tace wannan ba wata matsala bace Dan na yarda da sis na ,💯Kuma ina da tabbacin komai normal zaku gani inshallahu ...km duk aikin dakike so zata miki Dan gwanace gurin iya aiki bbu aikin da zai gagareta ummi tayi murmushi tare da cewa Nagode sosai sannan ta kalli nablah dake zaune a gefe shr sai faman wasa take da yatsun hannuta.

kina jin abinda yaayarki tace ?
,nablah ta dagawa ummi kai alamun taji ,ummi tace A'a nifa bana son kyaliyya ki bude baki kmr yadda na miki ,sannan ta dubi aunty Salmah ko bata magana ne naga tunda kuka zo batace komai ba?.
Chapter 63 · 0% Book details