← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 149

Sashe 28

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Byn yan wasu yan mintina Sai gashi yashigo da sallama ,mutane dake zaune a dakin .
suka fita gabadayansu dan basu waje .
Ahankali yakaraso cikin dakin sosai, ya durkusawa gaban ummi yayi zaman dirshan har da tankwashe kafafunsa. ganin haka yasa itama zeenat tazamo " tayi irin zaman da yayi a gaban ummi" Sai dai ita zuciyarta da gangar jikinta cike suke da rauni.
badan namijin kokarin datakeyi ba da tune zuciyarta ta buga tsabar frigici.
Ummi tayi shr tare da zuba musu idanunta da suka gama canza kala saboda kukan datayi.
Tsawon lokaci tana zaune ta tasa su gaba tana kallonsu kafin daga baya tasoma magana
cikin sanyi muryata ta Kira " sunansa NASURUDEEN...... ahankali ya dago idanunshi yana duban umminsa dasu batare daya amsa ba .
Sai dai yadda takira sunanshi din ya girgiza zuciyarsa domin ya manta when last da yaji takira complete name dinshi haka .
Dan haka ya tattara dukkan hankalinsa da natsuwarsa gareta .
Cikin sanyi murya data sha kuka tace DEENi ga zeenat nan ta sake dawo gareka" a karo na biyu . Sai dai wannan karon yasha bamban da sauran lokuta .
'wanna karon ta dawo gareka ne da matsayi guda biyu ,kawarka km matarka .
zan ji matukar farinciki da kwanciyar hankali idan kuka hada kanku ,kuka zauna lfy.
, zeenat yarinya karama kayi hakuri daita" duk wani abinda ta maka wanda bai yi maka ba , ka sanar min .
Ni Zan fahimtar daita ta hanyar da zata gane .
Ban yarda da duka ko zagi da cin fuska ba .
Kuka zeenat din keyi har lokacin shi kansa ya tsausaya mata matuka
Ga mamakin DEENI Sai ya ga ummi itama ta sauko gabansu hawaye ne ke bin fuskarta wani nabin wani ,a rude deeni yasa hannushi yana share mata hawayen .
Cikin tsananin tashin hankali Yace dan Allah first lov ki daina zubda hawayenki haka , kiyi hakuri "zubda hawayenki bakaramin maseefa bane atattare dani " idan har yanzu bakya son aurena da zeenat ne wlh ashirye nake dana bar miki ita har abada .
Cikin kuka ummi ta girgiza masa kanta ba kukan komai nake ba DEENI facce na tsantsar farinciki .
Farinciki ne yamin yawa har yasani zubda su.
,ta janye garesu byn ta dauke hawayen idanunta.
kama hannun deeni dana zeenat tayi "ta hade su waje guda tare da daura nata hannu saman nasu .

Nagodewa Allah daya nuna min wannan rana may cike tarin farinciki mara misaltuwa , zeenat ga deeni nan nabaki shi amana har abada banida kowa Sai shi.
ki zauna lfy dashi cikin amana "deeni kaima ga amanar zeenat nan naba matukar ka cuceta "ban bazaka ji dadina ba. Dan Allah Ku kula da junanku .
Ku rike min amanar junanku " ku kadai gareni byn Allah banida kowa Sai ku.
abinda tata fada kennan tana sake hade" hannuwansu waje daya .

Duk yadda yaso daurewa zuciyar kasawa yayi sakamakon ,kaunar zeenat din da yake hangowa karara a cikin idanun umminsa.
bai so zeenat din taga kasawarsa " dan haka ya kife kansa kan hannun umminsa ya sumbata cikin dabara ya goge kwallar idanunshi. zuciyarsa ke kwabarsa akan alkawarin da umminsa ke so ya daukar mata " shi kadai yasan abinda ke damun zuciyarsa , aranshi ya dinga ayyana abubuwa masu tarin yawa"anya kuwa zai iya daukar alkawarin nan ....

jikinsa yayi masa nauyi tausayin ummin ya sake mamaye zuciyarsa. muryasa a sanyaye yace ummi ki kwantar da hankalinki inshallahu bbu abinda zai faru zan riketa amana yayinda a cikin zuciyarsa yake sauya kudirin ,ma,anar na karba dan kada Allah ya tuhumeshi gobe kiyama.
Yayinda ta kasa km hannuta dake cikin nashi yake ta murzawa ahankali cikin wani irin salo da yake sa tsagar jikinta tashi .
saboda nata hannu na kife ne cikin nashi tafin hannun.
gabadaya jikinta yayi tsanyi yasoma rawa rawa "dan samun saukin hanyar tsira da son cire hannuta cikin nashi" yasa tayi saurin cewa na karba alkwarin ummi inshallahu ni dai addu'arki kawai nafi bukata "
.cikin sanyi ya sakar mata hannu ..
Allah sarki ummi wani irin farinciki ne gyaraye da tsantsar kaunar ya mamaye zuciyarta . murmushin jin dadi ta dinga yi .sannan ta mikar da zeenat din tsaye ta rungume ajikinta . Tace Mamana ina miki addu'ar km bazan gushe wajen yi muku addu'a ba Allah ya muku albarka ,ya azurtaku da ya'ya masu albarka.

Da kyar su aunty zahra suka rikota sakamakon rukunkume ummi da zeenat din tayi .

sun fito tsakar gidan dake cike da mutane .
Wanda ,Yawancin duk en'uwa ummi ne da kawayenta.

Kai tsaye gidan mahaifinta aka kaita shima nasiha may tsara jiki yayi mata sosai da nuna mata tayi hakuri ta kula da mijinta , tamkar yadda mahaifiyarta tayi. yace naji dadi kwarai da deeni yakasance miji agareki,ina muku fatan alkhari .
Ina da yakini deeni zai rike min ke da amana .'
da baki duk wata kulawar da ta dace.
Ahankali take cigaba da kukanta.. aranta kuwa cewa tayi uhmmmm.
abba bakasan asalin halin deeni bane .
shiya ka fadi haka.
,halinshi na zahiri kawai kasani bakasan na baniba.
yace ta daina kuka duk abinda take da bukata karta zamo may rokon miji ta tmbye shi zai mata .

,har gidan big dady Sai da aka kaita agurguje suka dawo gidan kafin motar daukar amarya tazo.
may gyaran amarya ce ta sake mata sabon gyara na musamman zeenat din ta sake fitowa fes abinta .
Sai sheki take zubawa ga wani irin kamshi na musamman dake tashi ajikinta .

Duk da cikin estate din zata zauna hakan bai hana motocin abokan deeni dana fk cika kofar gidan ummi ba .
Dan daukar amare .

Shemah aka soma saukewa , sannan zeenat aunty zahra ,ke rike da hannuta fuskarta rufe cikin mayafi" har cikin gidan ta umarceta da tashiga da kafar" dama tare da yin Bismillah " tayi kmr yadda aunty'n tace.
sannu ahankali har suka iso dakinta ta zaunar daita akan gado.
nan da nan mutane suka cika gidan dan ganin dakin amarya .

ahankali zeenat ta dan bude idanunta da suke rufe " tana kallon irin dukiyar da Ummi ta narka mata a daki wanda take jin ko mahaifiyarta ce a raye .
bazata iya mata kwatankwacin haka ba , dan ma tsayawa bada labarin irin kayan da Ummi ta zuba mata a dakin ma bata lokaci ne ..

Zaune dake a gefen laulausar zanin gadonta ta cure waje daya sakamakon tsaron daya cika . Ahankali ta kai idanunta kan agogon dake manne da bangon dakin" Karfe goma shada ta buga daidai"atsorace ta saki ajiyar zuciya saboda wani sabon tsoro dataji yana kawo mata ziyara.
A ranta tace kar dai deeni barinni zaiyi in kwana ni kadai.
aiko idan haka ta kasance da nashiga uku dan a gaskiya bazan iya kwanta ni daya acikin gidan ba .

Yan kawota basu minti goma da tafiya ba.
taji saukar yayyafi sama sama wanda ya hadasawa yanayin garin yin tsanyi hade da kamshin kasa.
" ruwa bai yi yawa ba haka nan yayyenfin bai tsaya ba.
Kusan tun lokacin da suka tafi suka barta anan take zaune bata ko motsa ba Sai yanzu datayi tunanin deeni na iya barinta ta kwana ita kada . Hakan yasa ta Mike cikin tsoro ta kulle kofarta ta dawo ta zauna ,zamanta ke da wuya .

Tasoma jiyo Hayaniyar muryoyin maza daban daban" a cika gidan hakan yasa taji tsinkewar zuciya .Tare da faduwar gaba da .
hankali ta runtse idanunta tana jin yadda zuciyarta ke dukan uku uku kmr zatayi tsalle ta fito waje .

Deeni tsaye a parlour'n yayi babbake tare da dakatar da abonkansa .
yace to to....Nagode sosai da kulawarku.
rakiyar ta tsaya iya nan..
ba Sai kunshiga ba.

fahad ne yayi murmushi sannan Yace ko baka fada ba ma anan zamu tsaya.
,muma bashiga zamuyi ba .
,dan an dade da daina wannan .
Shr tayi tare da kamkame jikinta waje daya tsoro ne ke sake kawo mata ziyara .
tun tana jiyo hayaniryasu sama sama har tadaina taji dif...alamun basa cikin gidan sun fice .

Juyawa suka sake yi tare ya raka su , fahad na ta mishi tsiya iri iri
Cikin sauri sauri "gudu gudu yashigo parlour sbd ruwan daya sake yin karfi duk ya jike masa farin yadin dake jikinsa .
Ya tsaya kulle koina .

Ahankali ya murda handle din kofar dakinta yajita a kulle .
Ganin alaum murda kofa yasa ta sake mikewa tayi taje ta bude masa .
Tana may sunkuyar da kanta kasa .
.cikin sanyi jiki ya shigo dakin tare da rungumeta tsam tsam ajikinsa da hannushi daya "sannan ya ajiye tarin ledodin dake hannushi kamshin dake dakin kawai ya isa yasa kagane rana ce ta musamman....

MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Page 31-32

Wani irin shock taji ajikinta " lokacin da shaki mayataccen kamshi turarensa , take jikinta ya dauki kirma.
Zuciyarta ta tsaya cak ta daina aiki wani lokacin kafin daga baya tacigaba da bugawa da sauri da sauri "mamaki da fargaba ne suka taru suka lullube ta ,wai itace yau rungume akirjin Yaya DEENI" abinda ta dade tana mafarkin samu kennan.
dan haka ta sake lafewa ajikinsa' tare da kai hancinta tsaitin dayafi kamshi ajikinsa . muryata a sanyaye tayi masa sannu da zuwa tare da lumshe idanunta.
, sake rungumeta yayi ajikinsa tsam tamkar wacce za'a kwace masa ita, sannan ya amsa da yauwa tana makale a jikinsa ya kulle dakin.
Taba zaci zai amsa mata ba dan ta sake narke masa .

Ahankali yasoma takowa zuwa kan lullausar center rough dinsu .
ya zauna daita yana sauke ajiyar zuciya sosai take mamakin hali irin nashi
"tamkar ba shi ne wannan maseefaffen mutumin da kallo daya idan yayi maka" ya isa ya tarwatsa zuciyar duk wanda akawa shi.
,hannushi duka yasa ya cire mayafin dake lullube da jikinta "tare da zuba mata sexy eyez dinshi.
,kamshin jikinta da wanda ke gyaraye da dakin ke sake tsuma zuciyarsa.
,duk da bai tsananin sonta , Amman hakan bai hana shi jin mutuwar da ilahirin jikinsa yayi ba .
gabadaya jikinsa bbu inda bai dauki sauyi na musamman ba .
Chapter 28 · 0% Book details