← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 149

Sashe 136

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ta girgiza masa Kanta batare da tace komai ba alamun ta amince yauwa diyar albarka nasan daman baki da damuwa ta nan, ko wancen karo ma dakika bijeremin nasan sharrin Salma ne da makircinta Amman nasan ba halin diyata bane ..
sai da mlm salisu ya dasa aya sannan nablah tace baba ... muryarta Na rawa rawa ..Ina neman alfarma guda daya agurinka dan Allah kayi hakuri kabani nan da wata uku , Ina son nakoma gurin aikin nan nawa Dan akwai abinda zan karasa musu wanda ya zama lallai sai nice zanyi da zarar nagama inshallahu zan dawo sai natare....
mlm salisu ya girgiza Kai yana mata wani irin duba kana yace Aa nabeela bazan iya sake barinki zuwa wani guri ba me kike son mutane suce akaina ..?
nazama uban banza kennan agareki koda bbu auren kowa akanki Nablah bazan km yarda da komawarki ba ballanantana yanzu danasan da auren wani akanki .
Me kike tunani mijin naki zaice akai idan yaji labarin kinzo kin koma ?

Muryarta cike da kuka tace Baba tunda yasan banana km Bai San da dawowata ba kawai kada kasanar masa Na dawo .
Aa nabeela kiji mgnta sannan kiyi abinda nake so ko al'amuran ki zasu daidaita arayuwa . gabadaya yanzu kin sauya halayenki dana sanki dasu domin ada kin kasance me biyayya gareni sannan km baki jayyaya ko yi min musu akan duk wani abu danace sabanin yanzu .

Sosai tashiga yiwa mlm salisu magiya da rokonshi tana kuka Amman yace sam Bai yarda ba.
bbu abinda nablah bata fadawa mlm salisu ba akan yabarta ta koma .
bafa zan barki ba nabeelah ki sake komawa ba.
gara ma ki hakura kiyi zaman aurenki shiyafiyye miki alkhari akan wannan aikin .
km inshallahu idan kika bi umarnina zakiga daidai arayuwarki .

Muryarta a shake sbd da kukan da tayi tace shikennan baba Na hakura yayinda km acikin zuciyata ba Haka bane ta dai fadi Haka ne kawai . ta yaya ma zata zauna ta haifi 'cikin shege a gidan ubanta.wazata tace Yayi mata ?
Kai ina...zamanta ma bazai yuwa ba duk da tana son zama 'cikin alhalinta .

Alhamdulilllahi kisoma shirinki daga wannan lokacin zuwa kowani lokacin zaki iya tarewa agidan mijinki....yana karasa fadar hk
ya Mike tsaye tsaye yasoma kokarin cire babbar Rigarsa ya rataye .

Jikinta a sanyaye ta fito Daga dakin mahaifinta

Byn fitarta mlm salisu ya dade zaune yana tunani akan lamarin nablah . gabadaya mlm salisu Yayi deciding akan abinda Yayi mata ko zai amince da bukatar ta ko bbu Nablah me biyayya ce agareshi.
yashiga damuwar sosai akan ganin yanayin diyarsa km abar kaunarsa ahankali ya dinga jin acikin tanaji yanaji babu dadi .
Sannan kwata kwata Bai ji dadin ganinta 'cikin halin damuwa ba. yakasa yin komai ko abincin da aka kawo masa tunani Bai barshi ya iya ci ba ..

Daren ranar nablah Na kwance akan gadon mahaifiyarta juyi kawai takeyi tare da tuhumar kanta akan abinda take son aikatawa kanta.
batasan dalili ba .
Sannan batasan abinda yasa ba Amman ji kawai take zuciyarta Na ingizata ta gudu kawai ta bar gidan ta koma ta haifi abinda ke jikinta tunda tasamu wanda zai amsa km ya fita bukatar abinda ke cikinta . take km ta tsinci kanta 'cikin wata irin faduwar gaba sakamakon tuno deeni da al'amuransa datayi .
Wani irin kewarsa taji ta tsarga mata tare da mamaye zuciyata da gangar jikinta duk ta inda ta motsa sai taji hannushi Na yawo a tsantsar jikinta .sosai ta dinga sauyi atare daita agame dashi .
Ta dinga jinshi har acikin jinin jikinta da gangan jikinta zuciyarta tashiga harbawa ahankali tana aiyana mata abubuwa masu tarin ,yawa akansa.. da kyar nablah ta rentse shanyayyun idanunta tana saka da warwara a zuciyarta akan zamanta gidansu da 'cikin wata bakwai da satinnai ..ajikinta.
tasan muddin mahaifinta yasan da zaman 'cikin jikinta kashinta ne kawai bazai yi ba da duka .akaron banza ma ,zance idan yakamaka kana sai Yayi matun mugun duka tana kallon yadda yake dukan nuratu akan tara samari Ina ga ita me dungurungun ......
Idanunta suka bushe takasa runtsawa 'cikin Haka nuratu tashigo dakin hannuta rike da waya tana chatting ta zauna agefen nablah. sanyayyiyar ajiye zuciya Nablah ta sauke da karfi gaske har nuratu ta juyo 'cikin sanyi jiki tana duban yanayinta kana tace wai ke meke damunki ne duk kin wani takurawa kanki akan maganar baba?
idan baki son auren dayayi miki kigamasa man bawai ki zauna kina damun ruhinki da tunani banza ba .
Itama nablah juyowa tayi sosai tana kallon nuratu takasa ce mata komai ..

Nablah ....nuratu takira sunanta .
muryata a sanyaye ta amsa da Na'am. Ta amsa muryarta Na rawa .

meyasa. kike son komawa gidan aikin nan byn kinsamu abinda
yakai ki ?

Kuma wani abu ne zai sake maida ke ?

,aganina ki hakura kawai da duk ma abinda zakiyi ki zauna acikin mu wlh lokacin da baki nan nasha mafarki dake kina 'cikin wani halin tashin hankali shiyasa ni yanzu a gaskiya bana son ki sake yin nisa damu .
duk da jikinki ya nuna baki 'cikin damuwa da wahala Amman wlh hankalina Bai kwanta da wannan aikin naki ba.

, Nablah ta fara kwalla idanunta suka cicciko taf da ruwan hawaye xuciyarta na sake karyewa .
muryarta a sanyaye km cike da raunin hawaye tace aunty nuratu bazaki gane abinda zai maidani gurin aikin nan ba kona gaya miki .
sannan km batun mafarkinki gaskiya ne domin Ina 'cikin tashin hankali da garare rayuwa wanda Yasa bana jin zan iya cigaba da zama a tsakaninku acikin wannan yanayi .
,dan hk Na yanke shawarar gobe zan yi tafiyata Amman dan Allah kada ma ki gayawa kowa dan bama zan koma gidan aikin ba .
A frigice nuratu ta ajiye wayar hannuta tana fuskarta nablah dake kwance tana matso ruwan hawaye idanunta.
kina nufi duniya zaki shiga ko me ?

Niidai kiyi min addu'a kawai domin rayuwata tana 'cikin tasko wanda bansa ranar dazan fita ciki ba Nablah takarasa mgnr hawaye nabin gefen idanunta.

Me Yayi zafi hk indai akan auren da baba ya daura miki ne Ai gara kiyi zamanki idan yaso kice masa
baki so .
Amman zance guduwa ma kada ki farashi domin sunanki zaki bata .
Uhmmmm aunty nuratu wlh ba a dalilin auren da baba Yayi min bane .
Kawai dai akwai wani sirri dake tattare dani ne.
Km shi zai hanani zama tare daku a halin danake ciki .
wani sirri ne wannan da har da bazaki iya gaya min shi ba Ina matsayin yaruwarki ?

Nablah tayi shr zuciyarta Na wani irin bugawa km tana son sanarwa yayarta zance cikin jikinta Amman bakinta Yayi mata nauyi takasa cewa mata komai.

Uhm Ina jinki nablah ki sanar min da abinda ke damunki ko zan iya taimaka miki idan km har abun yafi karfina sai mu sanarwa da aunty Salma. still shr nablah tayi taki cewa komai duk yadda nuratu taso nablah ta sanar mata da damuwarta Amman taki. Dan hk nuratu ta hakura tace shawarata takarshe da zan baki kada ki kuskura ki gudu kije koina ki zauna duk rintsi km komai Yayi tsananin sauki Na zuwa da izinin Allah .sannan
Ta Mike ta fice Daga dakin ..

byn fitar nuratu nablah ta sake afkawa 'cikin duniyar tunani iri iri a game da rayuwarta shekarata, ta 'cikin Sha takwas kennan Amman tension din dake idanunta Yayi mata yawa. zuciyarta banda zafi bbu abinda take mata ,tana murna tazo gida gashi tazo ta tadda wani sabon tashin hankali dayafi na 'cikin jikinta.
Wai babanta ya daura mata aure da mutumin da ko shi kansa Bai San kowaye ba .abu kmr a film..
Yadda nablah batasamu runtsawa ba hk ce takasance da deeni shima.
Dan kwata kwata ko kwanciya kasawa Yayi atsaye yake yana ta faman aikin zariyar a dakinsa .
Da tunanin abinda zai biyo baya domin ake uku yayiwa Kule direban ummi zuwa unguwar su nablah ya daukota Amman taki biyo shi wai ba yanzu zata dawo ba har yakira ummi 'cikin tashin hankali fisrt love kin Gani ko.
kinga abinda yasa kikaji naki yarda da zuwan yarinyar nan ko... yanzu meyye solution ?

nifa zanje kai tsaye komai ma zai faru sai dai....naji Amman kabari zuwa gobe mugani ummi ta katse shi ta hanyar ce masa hk.
Ni San yarinyar nan bazata iya zaman gidansu. Da 'cikin jikinta ba .
Jin ummi kawai yake Amman gabadaya hankalinsa a mutukar tashe yake.
zariya yake sosai hannuwansa duka rungume da kirjinshi ...yana Allah Allah gari yawaye.
Chapter 136 · 0% Book details