← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 149

Sashe 127

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko ance maka hk ake yin so duk da bantabayin soyayyar ba wlh nasan ba hk akeyin so ba ....dan hk Ni mlm ka saurara min kada ka kuma damuna da wani zance sonka nake .
wayanda sukaga zasu iya son naka ,suje suyi tayi ,sunji zasu iya ne Amman banda ni nabeelah salis gulumbe takarasa fadar hkn tana nuna kirjinta da dan yatsanta .

Fesssss ya bude rikitattun idanunshi akanta ya zuba mata yana kare mata kallo hakika ita din daban take ko acikin darurukan mata akan aji ...Bai taba tunanin level dinta da tsaurin zuciyarta ya Kai hk ba ,km har ma yaso yazarta tunaninsa ...
ya taka sannu har inda yakoma ta tsaye tana sakin numafashi mgnr datayi da kyar ..

Ya hadeta da kirjinshi yana fidda numfashi me gyaraye da bacin rai yana jiwo tudun nonuwanta da 'cikin jikinta ya sake ya sake busa mata hucin numfashinsa sannan muryarsa a hargitse yace Ni kike dagawa sautin murya nabeelah.?

Yanzu har munzo wannan stage din ?

kinsa Allah kina sona nabeelah tamkar kiyi hauka amman dakinkancinki yasa kika kasa ganewa ..

tayi masa wani irin kallo bashi da hankali ko mara lfyr , kana tace wlh Ni ba dakikiya bace kullun da'anyi mgn kacewa mutun dakiki alhalin Kai .....sai km tace Ni dai gsky ni ba dakikiya bace ..
sai waye dakiki idan bake ba ?

Oho.. shima dakiki ai yasan kanshi amman wlh ni ba dakiki ba.. ya hade fuskokinsu guri daya yana busa mata hucin numfashinsa me gyaraye da zafin shauki uhm abinda Ni dake bamusaniba wani bakin almari Na shirin faruwa da zuciyoyinmu wanda bamu san ko meyee ba ..

kana ya kamo hannuta duka ya rike Yana mata massaging wani irin abu taji Yana shocking din jikinta yayinda gabadaya tsigar jikinta suka Mike tsaye ..

Muryata a raunane tace wani bakon al'amari ke shirin faruwa da zuciyarka wanda bakasan ko meyye ba.. amman banda tawa zuciyar datake tsarkarka km kubudadace dagareka..
Ya janyota sosai tare da manna bayanta da kirjinshi hannushi km ya maida kan cikinta ta rantse idanunta dan kwata kwata batason tunowa da 'cikin jikinta Yacigaba da shafa 'cikin yana jin motsin da 'cikin ke yi akai akai yanzu sosai fiyye da ko wani lokaci 'cikin hk wayarsa ta dauki kara sautin wakar India me dadi yasoma tafiya daita ajikinshi yaje inda ya zube wayoyinsa ya dauki wayar yana sunan umminsa yagani ya danna wayar yana manneta da kunnenshi tare da yin sallama .

Bangare ummi kuwa bayan tilon dan nata ya dauka suka gaisa da tmbyr nablah yace tana lfy first love alhamdulilllahi daman nace Na sheda maka yanzu jirginmu zai tashi inshallahu ya lumshe idanunsa yana sake shafo tudun 'cikin jikin nablah tare da cewa Ok first love Allah yakawo Ku lfy tace Ameen ya 'cikin jikin nablah Yayi girma sosai ne ?

Ya sake lumshe idanunshi yana sake budewa yace uhm girma kadan nan ne first love to Allah yarabasu lfy shima ya amsa da Ameen,nan sukayi sallama daita tana sheida masa lokacin da jirginsu zai sauka Nigeria.
ahankali yakarasa ya zaunar daita akan Cushing din data taso kijirani har indawo duba wani abu.

Ta tabe bakinta kawai tana gyada masa kai .

yana fita itama ta Mike tsaye tasoma zagaye office din tana duba koina tare da yabawa da yadda tsarin office din yake .
Sosai komai Na cikinsa yabata shaawa , Daga karshe taje wajen dorawar dake zagaye da makeken table dinsa tana Yan dube dubenta har ta bude wata dirom taga tulin kudi masu yawa da basan iyakarsu ba ,ta dauki dari biyar aciki sbd ita kadaice karama aciki ragowar duk 1k ne ta fice daga office din .
Tasoma tafiya ahankali tana kallon mutane dake Kai kawo hanyar dataga wasu masu yanayi da Yan doko suna faman aiki bi.
", nan ta nufa step tagani me shegen tsawon gaske Yayi secul kmr snake ,tasoma tafiya batare da kowa komai ba 'cikin ranta.
da kyar tasamu ta isa can harabar ma'aikatar byn tafiyar data dingayi tana hutawa .

tana kawo bakin get me gadi ya tashi ya bude mata get yana mata kallon kurilla..
" ta fito gabadaya bakin titin dayake shr da karancin jama'a tana Yan duba dubenta tana kallon masu fice dashige.. wata hanya tabi data hango wata yarinya me saida plantenchirps wacce bata wuce age mate dinta ba .
km daman tunda zasu shigo tagatan taji plantschips din yashiga ranta ta siya ta samu guri daga 'bakin titin ta zauna jimmm can km ta Mike tsaye tashiga tafiya ahankali tana jin dadin yadda isakar gurin ke kadata rabonta da shan iskar waje irin Hk har ta manta ..

Tsaye yake abakin office din nasa "byn ya dawo office be taddata a inda yabarta ba.
" hankalinsa a matukar tashe ya fito yana duban ta inda zai hango bulowarta Dan baiyi tunanin nisa tayi ba .. kowa yaganshi sai ya gaishe shi cike datarin mamaki ganin manage deeni da Sam ganinsa ba'a asamu 'acikin sauki Amman gashi ayau a arha abakin office dinsa .
danna waya kawai yake yana neman layin fk batare daya dago ya kalli tarin masu gaishe dashi ba . Can km wani tunani yazo masa ya koma Office dinsa 'cikin sauri Yana Kiran sunanta tare duba agogon dake daure da tsintsiyar hannushi shr yaji yayi yawa yakara tsayawa for 5 minti .
" 'bakin kofar toilet din yaje yayi nocking still bbu respond kara nouking yayi still no answer ahankali yaji zuciyarsa ta buga ..da sauri Ya bude kofar yashiga Gani Yayi yawam bbu ita bbu alamunta.
wani irin uwar ashar ya saki tare da sake fitowa waje da mugun sauri.yanzu kam yasoma tunanin bata kusa dashi dan jikinshi Bai bashi hkn ba ..

Da maseefa ya isa bakin get da sauri Yana Kiran eze... me gadi da karfi muryasa tamkar zata tar watse da gudun bala'i eze yakaraso daga inda yake zaune yana aikin gadi yace sir am here ..ka budewa wata yarinya get ?

Eze yace sir Yan mata dana budewa get yau suna dayawa bazangane ko wacce yarinya daga ciki kake nufi ba .

deeni ya dauke shi da wani mahaukacin mari guda biyu ajere you are very stupid eze ...wata yarinya me sanye da hijab har kasa ta rufe idanunta da wani 'bakin abu ...

A frigice eze ya amsa masa da yesss yes. sir Na bude mata .... Tun dazu ta fita ..
Kutumar ubanka.
ubanwa yace ka bude mata ?
ya karasa fadar hkn alokaci guda tare da sake nufar eze gadan gadan wani irin gigitaccen mari ya sake sauke masa sannan ya shake masa makoshi Yana sambatu .

Ubawan yace ka bude mata get nace ?

ya fadi Hk Yana girgizashi wallahi idan banganta ba ,sai Na batar dakaima anemeka anrasa.......kafin kace tunin gurin ya fara cika da jama'a duk Wanda yazo yaga manage ne sai yakama gabansa 'cikin hk fk yakaraso gurin da sauri tare da riko deeni yanason kwace makoshin a eze hannushi kar Yayi kisan Kai .
Wai meyye hk deeni ?

Meye ya hadaka dashi ?

Ka sake ba girmanka bane ,a fusace yace girman shegiya me zanyi da irin wannan girman still hannushi Na rike da eze wanda ya kusan shekawa lahira tamkar deeni zai yi kuka yace eze ka cuceni kagama da rayuwata tunda ka bude mata get .
Wai kan wata yarinya kake mgn ?
Anya kuwa wani abu Bai taba brain dinka ba..deeni yayi wurgi da eze Yana sakin numafashi gabadaya ya rude yashiga tashin wani irin duba yake wa fk wanda yasa yaja baya kadan ..muryasa a fusace yace Kai ne mahaukaci bani ba domin ni sanan abinda nake ..wa ma yakiraki nan ?
Bar nan kafin Na sauke maka naka yanzu yana nuna masa hanyar da yatsunsa shi kam eze tunda yaji deeni ya saki wayarsa yashiga furta sorry sir am sorry sir bbu abinda eze ke aikin fada rike da wuyansa Yana rawar jiki .
deeni ya dawo tamkar wani zautaccen mahaukaci sabon kamu
,hankalinsa a tashe yashiga Kiran Ugo Sunday Kingsley Hk ya dinga Kiran escort dinsa dake zagaye dashi oready Yana me sake nufar 'cikin company .

securities din 'bakin get da escort dinsa kafin kace me tunin sun iso gareshi Suma hankalinsu atashe domin yadda yanayin boss dinsa ya sauya, sun San babu lfy .. umarni yashiga basu da kwantancen nablah da irin yanayin shigarta dake jikinta.

can km ya tuna da CCTV camera din dake zagaye da ma'aikatan ya juya da mugun sauri yakoma office din da securities masu kula da gurin suke tamkar zai tashi sama.

'Cikin sauri suka soma yin rewaning CCTV camera yana tsaye jikin bango rungume da hannuwanshi duka a saman fadadden kirjinsa sai dai gabadaya hankalinsa da idanunsa sun tattara ne akan CCTV shi kadai yasan irin halin tashin hankali dayake ciki ahankali aka fara tariyo masa tundaga shige da ficen mutane dake 'cikin company har zuwa sanda yashigo tare daita da fitarta da hanyar da tabi ai bai San sanda ya fito a gigice ba fk Na kokarin janyoshi da tmbyrsa wace yarinya wannan ya tada hankalinsa akan Amman Ina kwata kwata hankalinsa Bai jikinsa ballanantana ya tsaya sauraronsa a 'bakin titi yake yana wage wage ta inda zai ganta amman Ina bbu ita bbu alamunta securities da escort dinsa kuwa tuni sun bazu gurin nemanta ..

MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

Page 91

Wani irin kallo Fk yake yi masa na mamaki, mai d'auke da alamomin tambaya iri iri ,acikin ransa yake ayyana abubuwa da dama, shi dai yasan ko akan Zeenart matarsa bazaiyi wannan haukan haka ba, kuma a iya saninsa da tunaninsa bai san shi da wata mace ba byn matarsa zeenat, kuma gashi ya gani da idonsa a CCTV tare suka shigo, to wacece wannan yarinyar? tambayar da yayiwa kanshi kennan ganin bamai bashi amsa idan ba Oga Deeni ba, yasa shi nufar shi gadan-gadan.

Babu wani alamun tsoro a tare dashi ya kalli Deeni yace " wai kai Malam akan wacce banzar yarinya ka tada hankalinka haka?
, ka wani gigice ka fita daga hayyacink.......
Chapter 127 · 0% Book details