← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 149

Sashe 142

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahankali yake taka step har yakarasa saukowa zuwa dining area din fuskasa cike da tsansar annuri da zati so fresh dashi ya zauna akan kujerar dinning wanda oready yake a shirye. ummi da zeenat ne zaune suna zaman jiran fitowarsa .
,abinci zeenat ta hada masa da coffee dinsa Na gado yasoma ci yana jin wani irin sanyi har 'cikin zuciyarsa 'cikin sanyi jiki yasoma cin abinci sbd Yadda yaga umminsa tana kallonsa.
Sosai idanun ummi ke yawo a tsantsar jikinshi ,km da zarar sun hada ido da ummi sai yaga tana masa wani irin kallo kmr Na tunhuma kmr Na tambaya wanda shi kwata kwata Bai ganewa manufar hkn ba.
kasancewar shi ba me son mgn bane Yasa yashare ummi kawai Bai ce mata komai ba .
bai km Bai tambayeta dalili ba Amman shi aranshi yana jin kmr an dauke masa wani dutse ne sbd yana jin kanshi so freshi da farinciki byn yakammala da cin abincinsa yake sanarwa ummi zance zuwansa asibiti da nablah zai wuce .
domin yana son ya kaita a duba masa lfyrta.
tun kafin ummi tayi mgn zeenat tace Kai gsky kam my hrt yakamata wlh danni nima Na dade da yin tunani akan hk .
Km tun jiya kayi mgn ai da tare zamu .
Me zai hana yanzu ma kibisu kuje taren ai zaifi tunda kinga ke mace .
Bakamar ba .

Girgiza kanta kawai tayi bari suje kawai ummi wani lokaci maje .
koma Na kaita da kaina ..

Bayan sun isa asbiti aka dubata da lafiyar bby akace za'a yi mata scanning.
fur Nablah taki yarda tasoma kuka dole haka Deeni.
Yana ji yana Gani ya hakura dan ya fuskanci rikici takeji dashi .
Daga hospital din Kai tsaye office dinsa ya wuce da .

Suna shiga ta Mike kan kushin dinsa me kama da bed tayi Kwanciya .
shi km ya kulle office din yasoma abinda yakawoshi ..

Ahankali bacci ya dauketa baita ta tashi ba sai gurin la'asar.
kallonsa tayi kmr zatayi kuka tace deeni kana tsoron Allah kuwa ?
Kalli yadda lokaci bautar Allah Ya wuceni baka tashe ba wai Kai wani irin mutu ne please ?

Murmushi yayi tare da girgiza mata kanshi alamun shima Bai sani ba .
harara ta cilla masa Daga inda take cike da takaicin halinsa.
Sannan mike ahankali zuwa toile din dake office din..

'Bayan ta idar da salolinta tayi addu'a ta shafa ta nike prayer mat din dayabata tayi salla dashi ta matsa ta daura masa saman table dinsa ta koma ta zauna fuskarta a hade Dan jin haushinsa .

Xoki dauki abinci kici yace daita .

Azumi nake tabashi amsa adakile alhalin km babu wani azumin datakeyi .

Bai km mata magana ba Yacigaba da rubuce rubucesa har zuwa karfe shida saura tana zaune shr shi km yanata aikinsa kmr Bai san da mutun ba duk har 'cikin zuciyarsa yaji bbu dadin rashin cin abincin dabatayi ba ..

Ahankali yaga ta Mike tsaye ta nufi kofar fita .

Taji sautin muryarsa 'cikin sanyi wani abu kike son akawo miki ?
yace daita batare daya dago Daga abinda yake ba .
shanyayyun idanunta ta tsura masa wanda Yasa shi dagowa ahankali idanunsu suka sarke 'cikin juna ita tafara janye nata tayi kasa da kanta tana murza hannuwata 'cikin juna .

Sosai tabashi tausayi Dan ya hango gajiya da wunya attare daita .
Bataji motsinsa ba sai hucin numfashinsa taji daf daita a dan razane taja baya ya cilla mata wata uwar harara ,kauda Kai tayi tana mamakin yadda shi kwata kwata abun harara Bai yi masa wuya .

Mutafi ko kin gaji ?

Batare da ta amsa masa ba tasoma tafiya .
shi km yana biye daita abaya.
har suka shiga lift suna fitowa ta barshi tayi gaba ta abinta .
Tsaye ya sameta ajikin motarsa murmushi gefen baki yasakar mata sanda yakaraso Inda take.
Ta yamutsa fuskarta tare da turo masa Dan karamin tsukaken bakinta.
dariya ya kyalkyale dashi sosai yana nunata da key .

Bakinta ta bude Dan mamakin abinda yasakashi dariya har hk .

Nas.. aliyu Muhammad khaliyal ashe rai kanga rai ?
wata matashiyar budurwar ce fara Sol amman daganin ba tmby kasan ankara da cream din bleaching ke cewa deeni hk .
yayinda take karasowa gurinsu bbu ko dar ta rungume deeni ajikinta cike da dokin ganinsa tare da bashi sumba a kirjinsa .

Wayyohhhyyy zuciyar nablah tayi wani irin matsanancin harbawa da karfi , sannan takoma ta dinga bugawa da sauri da sauri .
sai data saki kara a can kasan makoshinta wanda ita kadai taji sautin abinta .
Banda dokawa bbu abinda ZUCIYAR nablah keyi Dan ganin wannan tashin hankali ganin matar nan taki raba jikinta danashi.
Taji wani irin tutukin haushi ya tsaya mata akirji .
Yasa a fusace ta janyo matar tayi cilli daita gefe tare da dauketa da wasu mahaukan mari . muryarta a sarke tace ke wacce irin jaka ce ki dinga kula da jikin mazan mutane .
Dan gabadaya zaki iya fadawa tarkon sharia ..tana nunata da yatsanta . sororo deeni yayi yana aika mata da kallon mamaki ..
Uhmmmm su nablah kennan .
ta juya ahankali ta jingina da jikin motar .

Hannayeshi zube duka 'cikin aljihun wandonsa yabita da kallo fuskasa dauke da wani irin matsanancin murmushi farinciki .

Nas aliyu wacce wannan wawiyar yarinyar har ta iya taba lafiyar jikina agabanka kana kallo ?
Wani irin mugun kallo ya sauke mata wanda Yasa tayi saurin ja da baya bashiri tafiya yasoma yi Dan isa idan take da hanzari Tasha gabansa yanzu Nas aliyu kana kallo aka wulakantani Amman ka kasa daukar mataki alhalin rabonmu da ganin juna over 12 year kennan Ina ta nemanka sai yau Allah yabani sa'a gashi nazo taka Nas Dan Kai Amman da alamun ko murna haduwarmu da juna bakayi ba.
haba Dan Allah duk me yakawo hk ?

A kufuke ya Daga mata hannu kibarni naji da riginar da kika cazamin akan wanda nake ciki jidda Dan wulakanci ma ki rasa irin tarbar dazaki min sai ta runguma 'cikin bayyanar jama'a .
Ai Ni wlh nablah tayi min daidai data dauke min ke da mari shasha kawai yasoma kokarin bude motarsa .kamoshi tayi cike da fitsari nablah dake tsaye still tana facing dinsu ta runtse idanunta gam.
karar saukar wasu irin mahaukatan maruka taji deeni ya sauke mata masu kyau d lfy . Ta sake runtse idanunta.
Banson shirme da shiriritanki Na iskanci leave me alone ..ya fada a fusace tun abaya banyi irin hk dake ba sai yanzu ne danake da lafiyayayun mata har guda biyu .....Ya nuna mata yatsunsa biyu
take gabanta ya fadi tagane wacce yarinyar data mareta yanzu matarsa ce .. wani irin kallon rainin hankali nablah da bude idanunta ke masa jin ya ambaci mata biyu ..

Yana gama fadar hkn ya bude motarsa yace ke.....shiga muje.
Nablah tayi masa banza taki motsawa ballanantana tashiga kmr yadda yabata umarni.
Bai wani tsaya westing time ba sai ji tayi an dauke ahankali byn ya bude mota side din baya ya sakata ya rufe shima yashiga.
Direbansa ya tada motar .

'Bayan motarsa ta bi da kallo cike da mamaki da takaicin tallabe da fuskanta .
Wato sai har yanzu shi yana tamkar yadda tasanshi bai canzawa . atunani ganin yadda ya fito Daga cikin companies dinsa yana murmushi .
Ya canza Daga wance Nas aliyu din data sani zuwa wani daban.
tana kallonsa har sanda securities dinsa suka saka motarsa a tsakiya suna kokari barin haravar ma'aikatan sannan ta nufi motarta a guje ta fige motar tazo ta wuce shi .
Tabe bakinsa yayi yayinda azuciyarsa yace fitinanniyar banza kawai bbu abinda ta iya sai shashanci .
ban saurareki ba acan baya sai yanxu .
shasha mara aji kawai mtsssssss ya furta a bayyane ..

Har suka Kai gida bbu wanda Yayi dan'uwansa mgn Daga nablah har deeni .
sai da motar ta tsaya ne nablah ta yunkura tana shirin fitowa taji .
an janyota an maidota ahankali tare da juyo daita suna fuskantar junansu .
cikin kwayar idanunta yake kallo yana hango tsagwaron sonshi da kishinsa tattare da tashin hankali iri iri a 'cikin su .
Muryarsa a kausashe yace as from today Karki kara yi min wannan stupid thing din da kikayi yau .
Wato marin wata akaina .Dan Banga abinda ya dameki dani ba ,da km rungumar datayi min .
Ko kina sona dazaki haushi ?
Tayi shr tare da tsurawa 'cikin idanushi nata kwayar idanun.
Dan iskanci har dayi abu kmr wata matata ko zeenat datake matata bazata yi min abinda kikayi ba.
Muryarta cike da rauni tace ..Amman ta ya'ya Dan tana Yar isaka zata rungumeka a.... shiiiiii gara ma nata akan Na wasu take tagane hannuka me sanda yayi mata idanunta suka cicciko zatayi kuka ..
muryarsa a sanyaye yacigaba da mgn km wlh kinci darajar 'cikin jikinki ne if not ni kadai bansan abinda zan miki ba .wawiya kawai idan ance kina son mutun kice a'a .

dama kince kina sona ko na dan taimaka Na aureki ko Dan dararjar kyautar bby da kika min .

taja tsarki tare da bude kofar motar da karfi ta fice ta barshi nan zaune . murmushi yayi kawai yana shafa sumar kanshi ahankali ahankali yarinyar kin makaro fa domin Na dinga kunna wutar kauna kennan acikin zuciyarki .

Wata irin kulawa da tarairaya ta musamman Deeni yake bawa Nablah ita kuwa saidai ta Bishi da shanyayyun idanunta akan duk abinda zai mata domin kwata kwata batajin hidamarsa gareta yana birgeta.
Chapter 142 · 0% Book details