← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 149

Sashe 13

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga inda Zeenat ke tsaye tana jin komai" take jikinta ya dauki yacigaba wara har wani zazzabi zazzabi taji yana neman rufeta , kafafunta suka Gaza daukarta sakamakon kirmar da suke , nan ta sulale kasa tana jin yadda gabanta yashiga faduwa da sauri da sauri , tarasa dalilin ummin nakin aurenta da yaya DEENi .
alhalin tasan yana sonta har haka .
,to hakan na nufin ummi tafison yaya yaje waje ya aure wata , sabanin ita kennan .
kawai batayi aune ba taji saukar hawaye nabin kuncinta .
Da sauri tasa Hannuta ta dangwalo hawayen dake bin fuskarta, tana kallo ta girgiza kai kawai tana jin tamkar an diga mata dalma ne zuciya ,.
Ta runtse idanunta ahankali muryarta cike da rauni tace meyasa ...
Meyasa ummi kike son ki ruguzamin rayuwa please ummi ki amince na auri yaya DEENi , Ina sonshi har bansan iya kar kaunarsa a zuciyata ba " bazan iya rayuwa in bashi ba

Fk ya fahimci abinda ummi take nufi shiyasa yace ma DEENi ya dinga kiran yarinyar suna hira. ko km yajata ajikinsa . Ta hakan ne komai zai zo da sauki , fuskasa dauke da murmushi yace ummi idan dan wannan ne ,karki damu , duk wannan me sauki ne zamu tuntubi yarinyar muji , idan bata amince ba Shikenan .

Ummi tace da dai yafiye muku" ba ku tsaya girman kai ba, fk ya sake yin dariya yana girgiza kai yayi mata godiya ya mike .

Jin da Zeenat tayi fk yayiwa ummi sallama ne yasa tayi hanzari mikewa da sauri tashige bathroom din parlour din dake manne da falon nan ta fashe da wani irin kuka ita kam zuwa yanzu tafara jin haushin ummu .

Fk na fita yakira deeni bugu biyu ya dauki wayar , fk yace friend kafara da bani goron albishir ,cikin yanayi na ko in kula deeni yace kada kace min first lov ta saurareka ?

Fk yace ta saurareni km inshallahu zamuyi nasara da alamun ummi ta amince ,.
duk yayi masa bayanin yadda suka yi da ummi ,
yakarasa zance da ummu ta nuna tanason asamu yarinyar a nemi amincewarta .....
DEENi yayi shr sannan yace to ai wannan shine mai wahalar dan bazan taba iyawa ba , fk yace wai kai tsorota kake jine ko yaya ?
,ai take deeni ya hassala a fusace ya aiko masa da wata irin uwar ashariya " wanda yasa fk yayi sauri cire wayar daga kunnenshi ,ya dan duba sai daya tabbatar daya yana kan layi. sannan ya mayar yacigaba magana" haba friend meyasa kake saurin daukar zafi akan abinda bai yakawo ba .

bance dole sai kasameta da kankaba ,ni dakaina zanyi komai.
sai Kuma ya sausauta yana jan numfashi yace ai kai ne da wani zancen baza.
naji tsorota akan me ,raini ne kawai banaso , yanzun dai kai kaje kasameta kuyi magana da in ni nakirata bafa ra'ayinta zanjira ba. umarni kawai zan bata fk yace Shikenan sai na nemeka .

Zeenat zaune gaban TV dake manne a parlour su ta hada uban tagumi ,hade da zubawa TV idanun . Kallo daya zaka mata , kasan kwata kwata hankalinta bai kan shirin da'ake gabatarwa .
gabadaya tunaninta ya kashi gida biyu .

ga tashin hankali ummi taki amince wa da aurenta da yaya DEENi. ga kamil da yasako, gaba da zance yanason kai maganarsu gurin big dady, .
hankalinta a matukar tashe yake .
har ummi takaraso inda take zaune taba tasani ba".
ummi ta zuba mata idanu kawai tana nazarinta sannan ta numfasa sai data kira sunanta tukun , Zeenat tayi saurin juyo a frigice tayi firgigib tana duban ummi .
idanunta ta zubawa ummi kmr wata mara gaskiya " ummi tace wai ke wace irin sakarriyar yarinyar ce" da kwata kwata baki san ciwon kanki ba "kalli ummi ta nuna jikin Zeenat da dan yatsanta , dube yadda kika dawo ,duk kinbi kin sakama kanki tunanin banza ji yadda kika koma duk kin tsotse kin rame dan jarabar tsiya ,anason a karemiki mutuncinki ,kinki natsuwa, kisan haka .
sai kiyi tayi ai.

cikin haka fk yayi sallama yashigo ya zauna akan kujerar one site yana gaida ummi
Ta amsa masa fuskarta a gimtse da tasan kwanan zance " Zeenat ma ta gaisheshi tsam mike taje takawo masa abin sha .

,ummi ta tabe baki tana hararata dan takaici sannan ta sake kai dubanta ga fk din" tace DEENI fa yana dakinsa .
Fk yayi murmushi yace ai ba gurinsa nazo ba ,jin haka yasa ummi tashare , ta cigaba da kallonta , gabadaya parlour ya dauki shr tamkar babu mutane a cikinsa baka jin motsen komai sai karar TV .
Zeenat kam kamewa tayi tashiga hankalita dan motsi kadan , ummi zatace tafiye rawar kai .
ganin shr yayi yawa yasa ummi ta mike tabar gurin ta nufi dakinta . Parlour ya saura daga Zeenat sai fk .

yana Ganin ummi tashiga dakinta yasa ya juyo yana fuskantar Zeenat yace sister wajenki nazo fa . tace to Allah yasa dai lfy yace lafiya nasan zakiyi mamakin zuwa na ?

Tace bawani mamaki killa akwai abinda kake son nayi maka ne .
yace ba wannan bane nazo ne dan nasanar miki da wani abun alkhari koda yake bansan yadda zaki dauki abun ba.
tsab Zeenat tagane abinda yakawo shi gabanta taji ya tsananta faduwa ,.

fk yace deeni ya duba duk cikin en'mata dake cikin family din nan.
yaga bbu wacce tayi masa km tadace dashi sai ke .
Zeenat ta zaro idanu waje kmr da gaske ta nuna kanta tace ni fa kace yana so...

Fk yace bawani abin mamaki bane , Dami kika tsinta a kala ,a ranta tace maganar ka gaskiya.
fk yace yanzu me kika gani idan kin amince , magana zata wuce gurin big dady kai tsaye batare da bata lokacin ba .
ta tabe bakinta kmr batayi murna dajin zance ba , sannan tace gaskiya kagaya masa kawai yayi hakuri dan ni narigada na tsaida wanda zan aura ,.

fk yace waye shi km a ina yake km kin kai maganar wajen big dady ne ? Duk alokaci yajero mata tambayar ,tace Ko daya muna dai shirin yin haka fk yace yace shi din wanene tace wani ne acikin family dinmu yake humm yace inbaki shawara ta daga masa kanta" zan so ki dakatar da koma waye.
dan kowa zaki aura ina tabbatar miki ba zai taba kai kmr DEENI ba .

ke kanki kinsa samun irin su DEENi sai an tona. zakiyi alfahari samun mijin kmr sa "mata dayawa suna ,sonshi ban sani ba kodan sun fahimci qualities dinsa ne .
sai km yace amman bazan takura miki ba in kinga bakison shi Shikenan .
ta kalleshi a shashance hade da wani irin salo sannan tace nifa bance maka bana son shi ba na dai kawai kace masa na tsaida wanda zan aura .
Kaga yanzu idan na canza raayina da sauri haka shi saurayin nawa bazai dadi ba .
ka dai bashi hakuri Allah ya hada kowa da rabonsa na alkhari .

fk yayi shiru yana cizan yatsa hankalinsa yasoma tashi "karfa yarinyar nan ta kwafsa masa yazaci yana mata zance zata amsa da murna ya fadi haka a kasan ranshi.
can km yace to ni yanzu mekike son nace masa ?

Ta sake tabe baki yace Kafada masa gaskiya kawai , yace ba za kiyi tunani akai ba kafin ki yanke hukunci ,ko km kuje kisamu wanda kika san kin amince mata km tasan deeni din sosai tabaki shawara akai, Zeenat tace naji zanyi tunanin .

Fk Yace Shikenan zan sake nemeki zuwa gobe naji abinda kika yanke akai , tace badamuwa .

Byn ya tafi, ne tashiga dakin ummi tana murna cike da farincikin burinta yakusan cika ,fitowar ummi kennan daga bathroom aiko tana ganin yanayinta da alamun tace musu ta amince ,take ta sake daure fuskarta , ta rufeta ta fada, ai gashi nan saboda baisan darajarki ,da kimarki ba sannan bai dauke ki da mahimmanci ba ,yakasa zuwa da kansa sai abokinsa ya turo miki nasan jikinki na rawa kika amincewa ko ?.

Zeenat taaba fuska tamkar zata saki kuka tace nifa ba wani rawar jikin danayi .
ummi tace wlh kiyiwa kanki fada, akan sakarcin da kikeyi ke kmr ba macce ba .
sam bawani jan aji irin na sauran mata .
Zeenat ta sake bata rai sosai .
ummi tace gaki nan ga deeni ,inda shine nabarki dashi ya isheki wando da riga .

A waya DEENi yaji duk yadda sukayi ya dinga mamaki wai wannan yar yarinyar ce zata ce sai tayi shawara to dawa zatayi ? Km ita ce wa ?

Fk yace itace mace deeni yace dan Allah malam imin shiru shiya sa fa kaga bazan iya kai kaina gareta da sunan Ina sonta ba bare tamin salo . Nan km yau zazzagawa fk maseefa yana Ai shi yaja masa duk wulakancin da'aka masa fk yace kwanta da hankalinka kavarni daita kawai nasan zata yarda ma kawai dai itama so take ta nuna mana itama macce .
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

Page 19-20

Shiyasa kaga bazan iya kai" kaina gareta ba da sunan Ina sonta , bare tamin salo .

Nan km yayi ta zazzagawa Fk maseefa hade da cewa ai shi yaja masa duk wulakancin da'aka masa .

Fk yace kwantar da hankalinka kabarni daita kawai ,nasan zata yarda ma ,.
kawai dai itama so take ta nuna mana ,itama macece , nasan jan aji ne kawai na mata Amman ita din wa dazatace bata sonka ,Ina rai inshallahu zamuyi nasara.

Cikin fushi da jin haushi deeni Yace in taki yarda ka kyaleta kawai , yarinya sai kace wata gold sai wani yawo akamin da hankali akanta, yaja tsaki hade da kashe wayar batare daya sake jin abinda fk zai ce ba .

Kwana deeni yayi da tunanin hade da zullumi halin da zai tsinci kansa idan yarinyar nan taki yarda dashi, duk shi Gani yake ba sonta yake ba. zai dai yi aure ne kawai saboda umarnin umminsa, bugu da Kari ma, bazai iya kaskantar da kansa wajen mace ba ballanantana har ya kai shi ga furta kalmar so.
Chapter 13 · 0% Book details