← Book details Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 149

Sashe 132

Auren Sirri Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Har sanda deeni yakaita dakinta kuka nablah take Na fitar hankali sbd gabadaya a tsorace take da ganin yanayin zeenat da ummi.
'cikin natsuwa yakarasa ya zaunar daita akan gadonta hade da janyo karamar stood din dake gefen bedside dinta ya zauna ya kamo hannuwanta dukka'cikin nashi yana murzawa ahankali ahankali tare da tsurawa beauty face dinta rikitattun idanunshi yana kallonta.
zuciyarsa Na masa wani iri tsalle tamkar zata tarwatse ta fasa kirjinsa ta fito.
muryarsa a sarke ya Kira sunanta ,ta dago shanyayyun idanunta ta zuba 'cikin nashi kukan ya isa hk ....Ko wani guri Na miki ciwo ne?

Ta girgiza masa Kanta batare da tace komai ba.
Ok ki natsu yanzu kibar kukan nan hk kinsa bake kadai bace damuwarki zata iya shafar lafiyar bby nah .
still shr tayi taki cewa komai yayinda km aranshi ya dinga jin zafin hasarar da zeenat taso yi masa.

meyasa zeenat bata tausayin takala da rabarsa ?

Meyyasa take kyamar talaka da nisanta kanta Daga gareshi ?

Meyasa girman Kai da kudi ke fusgarta da yawa.. har ta dinga manta kalar tarbiyar da umminsa tabata?
shi yasan Sam wannan ba kalar tarbiyar umminsa bane sannan km ba halin mahaifiyarta ta dauko ba mace me tsananin hakuri da son mutane .
Shi ya rasa Ina tasoma wannan halin nata Na girman Kai da Kin talaka da nuna kowa bakomai bane wanda ko acikin family itace lidar kowa . gabadaya zuwa yanzu halayenta sun sake canzawa fiyye da kowani lokacin Wanda can da Bai santa da hkn ba Amman yasan hakan ma yana da nasara da sababbin kawayen datayi .
Naunauyen ajiyar zuciya ya sauke da karfi yana jin a ranshi komai zai faru sai dai ya faru Amman wlh kan 'cikin jikin nablah sai dai sirrin boye ya fito filli kowa yasan abinda ake ciki .
....Ya kamo fuskarta da hannuwashi duka yana kallon 'cikin kwayar idanunta ya dinga jin aranshi da yana da iko akan kanshi, da dauketa kawai zai yi gabadaya Daga kasar ,zuwa wata kasa daban su cigaba da rayuwarsu hankali kwance 'cikin natsuwa yashiga tunanin rayuwar da sukayi a sabon gidansa ,rayuwa me cike da jin dadi da natsuwa wanda wani lokaci har manta yake da matsalar komai ....
bakinsa ya Kai daidai kan lip's dinta zai tsotsa tayi saurin kawar da fuskantar tana yatsinawa tare da zubawa plate din abincnta data dibo ajiye da niyar ci idanunta ahankali ya maida idanunshi zuwa Inda take kallo din .
ya tashi ya dauko mata plate din abincin ya daura kan tsood din daya tashi ya zauna a gefenta ,kici abinci please...Babu wani westing time tasoma ci dan wani irin yunwa take ji tun tea data Sha agidan glass ne ke cikinta.

Deeni Bai bar dakin ba sai daya tabbatar da nablah taci abinci sosai tasha ruwa sannan ya sata tayi wanka dan taji dadin jikinta ya kwantar daita ya lullubeta da blanket ya duko sosai inda take ya tsotsi lips dinta ya rage mata karfin AC dakin yaje ya kashe fitilar daki kana ya baro dakin tare da kulleta ciki dan gudun bala'i abinda zeenat zata iya mata .

Sosai hankalin ummi ya sake tashi da ganin irin halin tashin hankali da diyar tashiga.
ahankali muryar ummi a sanyaye tasoma rarrashin zeenat tana bata hkr akan abinda deeni Yayi mata sannan ta nuna mata itama nata kuskure akan abinda tayi Bai kamata ba mamana abinda kikeyiwa nablah domin kowane dan Adam yanada nashi baiwar da Allah Yayi masa .
har sanda deeni ya dawo Dining din ummi Na zaune tana faman aikin rarrashin zeenat dabata baki Amman kwata kwata zeenat din bata San abinda ummi ke ce mata ba sbd gabadaya ta dawo tamkar mutum mutumin tsabar mamaki da frigicin abinda deeni Yayi mata a gaban me aikinta.

ganin tahowarsa yasa ummi yin shr da bakinta ta hade ranta tamau tamkar wacce aka aikowa da mutuwa. shima ganin hk Yasa ya hade nashi ran sosai fiyye da tunanin me karantu idan baku manta ba daman kusan halin deeni da shan kamshi maseefa .

Gabadaya kuka zeenat take son yin Amman yaki zuwa mata sbd tsoro da mamakin dake daskare akasan zuciyarta.
Wani irin zafi kirjinta ke mata tamkar ana zuba mata yaji .. gabadaya abun ya girmama tunaninta.
to me hk yake nufi ?
Ta sake tmbyr kanta .

Takasa kuka ta kasa hauka ta kasa komai sbd abin ya girmi momery dinta zaune kawai take tana jin sautin muryar ummi sama sama batare da tana fahimci inda maganganunta suka dosa ba ..
yau Deeni mijinta ne ya mareta akan wata watan ma me aikinta kennan hkn Na nufin ya daina tsanar yarinya yanzu ko me ?
Idan kuwa hk ta faru a 'cikin gidanta da kuwa ta shiga ukunta ..

Deeni Yayi tamkar babu abinda ya dameshi ya zuba tuwan da kanshi hankalinsa kwance yasoma yaci batare da wata damuwa ba yana zuba santin tuwan acikin zuciyarsa .
wani irin dadi tuwan yake ji Yayi masa
ko kallon inda zeenat ke zaune bai yi ba ballanantana yasan damuwarta .
"yayinda hkn kuwa ya sake taba zuciyar ummi sosai to me wannan salon nasa yake nufi?

kardai gadar zaren data shirya diyarta ce ke shirin ruftawa ciki ?

Jiki a sanyaye ummi ta Mike tsaye tare da duban Inda deeni yake wanda oready tuni ita tagama tsakurar tuwanta .
muryata tamkar zata zubda kwala tace deeni muje Ina nemanka a daki.
shi kanshi yadda yaji muryar umminsa da yadda yake kallon yanayinta yasan ranta a bace yake matuka akan abinda Yayiwa zeenat yanzu dan hk shima muryasa can kasa kasa yace Ok sannan ummi ta nufi daki..

Byn kmr minti Gona sai gashi yashigo dakin yana ciccin magani sannan km fuskar nan tashi a daure still ya zauna a kujerar dake facing din umminsa .
ummi har lokacin jikinta a sanyaye yake .sai data numfasa kana tace yanzu deeni Kai kana ganin abinda kayi ya dace kennan? A gabana deeni ka mari zeenat kan matarka dan tsabar ka rainani takarasa fadar hkn tana nuna kirjinta wlh kabani mamaki .km ka tsinka min zuciya .idan wani yace min a gabana zaka aikata hk wlh zance karya ne ..

Sosai ummi tashiga yi masa fada ta inda take shiga bata nan take fita ba.. kafin km daga baya ta dawo yi masa nasiha me ratsa jiki da zuciya.. yanzu abinda kayiwa zeenat akan wannan yarinyar Yayi kennan ?
Nice fa tamkar mahaifiya Ga zeenat.
Zeenat bata da kowa acikin duniyar sama dani da mahaifinta sai Kai mijinta , Amman dan cin fuska agabana ka zage ka mararmin yarinya dan rashin mutunci.

kai kanka kasan banason aurenka da zeenat.
duk duniya bbu abinda zancewa zeenat banaso Amman ta kafe ita taji tagani tana sonka km taji tagani zata iya zama da baudaden hali irin naka.
ka tuna rayuwarku deeni ka tuna..bbu abinda banyi ba zeenat akan rashin son aurenku ta rufe idanunta tace ita Laila tana sonka.
ka tuna abubuwan da tayiwa kannen mahaifinta agabanka deeni ka tuna wulakanci dakayiwa kakarta inna mahaifiyar mahainfinta agabanta Amman ta Danni zuciyarta tacigaba da zama da kai, duk dan sbd son da take maka.
ka tuna irin dukan mutuwar da kayi mata. zeenat bata taba jin ta tsaneka ba ko tana kyamatar Halinka ba.

km duk tsiya dai zeenat uwar gidanka ce bata cancanci wannan wulakancin da kaskancin a gurinka ba.
yakama maza Ku dinga daraja uwargidanku ,Ku mutuntasu akan komai Na rayuwa ,domin kuwa sune wayanda suka fara bawa rayuwarku farkon farincikin mara misaltuwa. Dan hk wlh azim yadda ka kuntata mata Daga dawowarta to ka tabbatar kaje kabata hakuri tare da sanyata 'cikin farinciki.
gabadaya jikin deeni Yayi matsanancin tsanyin akan abinda ya'aikata muryarsa a kasalance yace first love kiyi hakuri Amman itama tayi kuskure abinda taso aikatawa yarinya nan .
yanzu idan wani abu ya samu 'cikin jikinta mezamu ce ?
yakarasa fadar mgn tamkar zai yi kuka Amman duk da hk nasan nayi kuskure nima kiyi hakuri ..Ya tashi daga inda yake ya matso sosai kusa da ummi yana sake bata hkrn abinda Yayi ..bbu komai amman ka tabbatar kabata hakuri naji first love zan bata ..Allah Yayi muku albarka ya amsa da Ameen tare da Mikewa tsaye Yayi mata sallama ya bar dakin.

Ahankali yaji jikinsa Yayi masa sanyi sosai ya dinga jin har a 'cikin zuciyarsa Bai kyautawa zeenat ba sosai zuciyarsa tayi regretting din abinda Yayi mata . tabbas bbu karya 'cikin maganganu ummi zeenat tana tsantsar son shi da kaunarshi Bai kamata ya mareta agaban nablah ba.
dan hk Kai tsaye dakinta ya nufa..
Chapter 132 · 0% Book details