← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 89

Sashe 9

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya kashe wayar, a ranar na kasa bacci ina ta tunani na san dai haramun ne, amma da ya dinga tsara ni da kalaman yaudara, da na barazanar fasa aurena sai na amince, sannu a hankali muka saba da wannan mummunar ɗabi'a, tsakar dare wani lokacin bayan na yi bacci na farka, wataran kuma ba na yin baccin sai na jira shi, zan tashi zaune mu yi ta dirty chat, yanzu na saba da kallon vedion, kuma idan na kalla ina shiga wani yanayi sosai na buƙatuwa, yadda muke yi idan ya turo bayan na gama kalla sai ya ce mu yi sharhi a kan vedion, tun ina jin kunyar cewa komai har na saba na saki jiki, a hankali Sadam yake faɗaɗa min sha'awata, ta kai har na matsu a yi auren.

Daga wannan kuma sai ya fara kwaɗaita kasancewarmu a zahiri, a nan ne dai na tirje duk kuwa ni ma zuwa lokacin ina jin sha'awarsa sosai, duk kalaman yaudara da ya dinga yi mini na ƙi yarda da shi, ya yi fushin ya gama ya dawo duk ban yarda ba, don na san wannan zina ce, ba shi da wasu kalaman da zai yi amfani da su wajen canza kalma, ni kuwa ba na fatan na aikata zina a rayuwata.

Daga baya ya bar yi min zancen, sai dai muna nan tare a waya, aurenmu ya rage wata ɗaya, lokacin har an fitar da anko 'yan'uwa ana ta yi, ya ce Momynsa ta ce na je na gaishe ta, tana so ta gan ni saboda za su haɗa lefe, na ce masa zan tambaya a gida idan za a bar ni, ya ce ba sai na tambaya ba, saboda idan na tambaya za a iya cewa sai na je tare da ƙanwata, ita kuma Momy ba ta son haka, zan yi musu ya dakatar da ni da faɗin"Kin ga Sayyada idan fa ba za ki je ba babu dole, ai mahaifiyata ce dama ban ce ki kalle ta a matsayin uwa ba, sai dai kuma ki sani ba ni da kamar Momy a duniyar nan, duk macen da za ta nuna ba ta ɗauki maganar uwata a bakin komai ba wallahi ban ga amfanin cigaba da mu'amala da ita ba".

Da sauri na ce"Ni fa ba da wata manufar na faÉ—a ba, shikenan yaushe zan je?"

Ya ce"Ko gobe ma".

Na ce"To zan tambayi zuwa gidan Anisa daga can sai na wuce ko?"

Ya ce"Allah Ya kaimu".

Washegari kuwa na je gidan Anisa tun safe, na wuni a can, ana yin sallar la'asar, na tafi, muka haɗu da Sadam a titin unguwar, ya ɗauke a motarsa muka kama hanyar gidansu, babban gida ne sosai, don iyayen shi masu rufin asiri ne, ya shiga da mota cikin gida, muka fito, gidan part biyu ne, na yi zaton babban part ɗin za mu shiga, sai na ga mun nufi ƙaramin, ya buɗe da mukullinsa muka shiga, falo ne madaidaici, sai sai ɗakuna guda uku, na zauna a kujera ina raba ido, gabana yana faɗuwa, saboda zan gana da surukata, ya fita, babu daɗewa ya dawo da drinks da snacks ya ajiye min, ya ce "Sorry babu kowa a gidan fa".

Gabana ya faÉ—i na ce"Kamar ya?"

Ya ce"E yanzu na shiga na ga ba kowa, sai na kira ta take ce mini ta tafi asibiti dubiya, wai ƙawarta aka kwantar, kuma na san za ta iya kaiwa dare ba ta dawo ba".

Na ɗauki jakata na miƙe na ce"To gaskiya tun da hakane kawai zan tafi gida, wani lokacin sai na dawo".

Ya ce"To jira na É—an watsa ruwa sai na kai ki".

Na zauna a tsorace, saboda yadda nake jin salon tantirancin Sadam a waya dole zan ji tsoron keɓewa da shi mu biyu a gida, har ya tafi ya dawo ya ce"Ko za ki taya ni wankan?"

Da sauri na ce"A'a, don Allah ka yi sauri kar Mama ta ga na daÉ—e".

Ya yi murmushi ya ce"Amma ai za ki taya ni shafa mai ko?"

Na sunkuyar da kai ban ce komai ba, zuciyata tana ta bugu, ya shiga ɗaya daga cikin ɗakunan dake falon, don tsoro ko ruwa kasa sha na yi, saboda zarginsa kawai nake yi, kar ya zuba mini wani abu a ciki na sha ya cim ma buƙatarsa a kaina, sannan na fara tunanin karya yake yi dama ya san Momyn ba ta nan, so yake kawai ya yaudare ni.

Ina nan zaune da zulumi na ji yana ƙwala min kira daga cikin ɗakin, na daga murya na amsa, ya ce"Zo mana".

Gabana ya faÉ—i, na ce"Na'am me ka ce?"

Ya ce"Zo ki ga wani abu".

Na ce"Don Allah ka zo ka mayar da ni gida, bai kamata na shiga É—akinka ba fa".

Na ji motsin buɗe ƙofar ɗakin, ina juyawa na gan shi daga shi sai boxer, ya nufo ni, kafin ya ƙaraso na tashi na ɗauki jakata ina cewa"Ni zan tafi kawai sauri nake yi".

Ya ƙaraso ya riƙe hannuna, da irin muryar nan ta cikin waya ya ce"Babyna, kenan da kike cewa kina kewar kasancewa da ni duk na ƙarya ne? Tun da ga ni yanzu mun samu dama me zai hana mu farantawa junanmu?"

Ƙwalla ta kawo idona na ce"A'a don Allah, mu bar wannan har sai mun yi aure".

Nan ya tisa ni a gaba da zantukan yaudara da daɗin baki yana nuna min ba komai ba ne wannan, wanda ba su da tabbacin za su auri juna ma suna yi ballantana mu da kwanaki ya rage aurenmu, bai ƙyale ni ba har sai da na amince na shiga ɗakin, ya yi yadda ya so da jikina, sai da ya nemi wuce gona da iri sannan na lura ni ma na shagala da yawa, na farga na taka masa burki, bai yi fushi ba sai ma godiya da yake ta min yana nuna min kulawa da soyayya, ya saka na yi wanka shi ma ya sake yi, sannan ya mayar da ni gida, jikina duk a sanyaye ina ta tsarguwa, gani nake kamar duk wanda ya kalle ni zai ga abin da na aikata liƙe a goshina.

08028966015
[27/09, 7:35 pm] Sadiya Abdulrazak: A sanyaye na shiga gida da siyayyar da ya yi mini a hanya, na miƙawa Mama kamar yadda na saba na ce inji shi, ta ce"A ina kuka haɗu? Ko shi ya kai ki gidan dama?"

Na ce"A'a, yanzu zan shigo gida na gan shi, sai na ce masa kaina ciwo yake, shi ne ya ba ni ya tafi".

Ta ce"To ciwon kai kuma? Ki ci abinci ki sha magani, kar dai ki kwanta sai kin yi sallah, ya Anisan take?"

Na ce"Lafiya lau, tana gaishe ku".

Na shiga ɗaki na kwanta, gabana sai faɗuwa yake yi, ina ta hango yadda kasancewarmu ta faru, na rasa ma me nake ji, Allah Ya sa ni ba da son raina ba ne, sai da aka fara kiran sallah na fita na yi alwala na yi sallah, na kasa cin abincin ma, ballantana magani dama lafiyata ƙalau babu ciwon kan, na kwanta lamo a katifa ina ta tunani, fatana dai Allah Ya sa kar Sadam ya sake neman mu aikata wannan abun, da daddaren mun yi waya da shi, amma na ce masa ba ni da lafiya, don haka ba mu yi irin chart ɗin da muka saba ba.

Amma washegari muka ɗora daga inda muka tsaya, har ma yana yi min sharhin kasancewarmu, ni ma kuma a hankali sai nake jin daɗi idan na tuna yanayin, don haka a tare muke yin sharhin, kuma har ma ina jin ina ma mu ƙara kasancewa haka, amma fa idan mun yi aure nake nufi.

Haɗuwarmu ta biyu gidan yayarsa ya ce za mu je, abun mamaki bai sake yi mini zancen zuwa gaida Momy ba, nan ma dai ƙarya na yi da zuwa gidan su wata ƙawata, ya zo ya ɗauke ni a hanya, wannan dai kai tsaye ya faɗa min ba gidan yayarsa za mu je, don kasancewa da ni yake yi, don haka hotel za mu je, hankalina ya tashi na ce"Hotel? Sai ka ce wata karuwa? Don Allah ka rufa min asiri, wallahi ba zan iya ba, don Allah ka mayar da ni gida, sati biyu fa ya rage aurenmu, muka yi haƙurin watanni masu yawa sai na sati biyu ya gagare mu?"

Nan take ya ɓata rai sosai, ya ce"Shikenan ki je kawai, na gode, tun da ni ba ni da wata alfarma a wajenki a matsayina na wanda zai aure ki".

Na fara hawaye ina tunani,ko a hasashe ban taɓa tunanin zuwan ranar da zan je hotel tare da saurayi da nufin aikata masha'a ba, a wannan lokacin dai ban yarda ba, na buɗe murfin motar na fita, ina saka ran ko da za mu zauna yana fushi da ni ba zan yarda ba, tun da sati biyu ya rage auren ko bai huce ba har lokacin idan aka kai ni ɗakinsa zai huce, adaidaitasahun na shiga na tafi gidan ƙawar tawa da na yi ƙaryar zan je, fira muke yi amma hankalina ba ya jikina, ina can ina tunanin halin da yake ciki.

Can na ji shigowar saƙo wayata, na duba na ga shi ne, da sauri na fara karantawa, "Sayyada wallahi kin ji na rantse ba zan iya auren wacce ba ta girmama ra'ayina ba, tun daga waje na bawa wacce zan aura umarni ta karya ina ga an yi auren? Ki sani a yau na yanke hukuncin fasa aurenki, kuma wallahi da gaske nake, ba zan dai fito ƙarara na ce na fasa ba, amma zan ta ɗagawa har a gaji a san cewar na fasa ɗin, don haka na ƙara watanni uku a yau".
Chapter 9 · 0% Book details