Sashe 49
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba ya ce"Babu damuwa ai, akwai yadda za a yi in sha Allah, Rauda ita ce autata, duk na aurar da 'yan'uwanta, kuma Alhamdulillah sun yi aure wasu a inda ya fi inda suka taso, wasu kuma a daidai da shi, don haka don dai Rauda ita kaɗai ba za a ƙi sama mata mafita ba, zan iya ba ka aron gidana sai ku zauna a ciki har zuwa lokacin da za ka mallaki wanda ya fi wancen naka ɗin, sannan zan ɗora ka a wani ɓangare na kasuwancina, yadda za ka samu cigaba kai ma har ka dogara da kanka".
Ustaz ya ce"Na gode sosai Abba, Allah Ya saka da alkhairi, ya ƙara girma".
Abba ya ce"Babu komai, wanann ai yi wa kai ne, fatana dai ka zama mai riƙe amana, sannan ka riƙe Rauda riƙo na gaskiya da adalci, in sha Allah babu abin da ba zan yi maka ba, ai surukinka ɗanka ne".
Haka Ustaz ya bar gidan cike da farinciki, kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha, a ransa kuwa rayawa yake lallai mahaƙurci mawadaci, har ya hango shi a babban gida, a luntsumemiyar katifa, a ranar ya so faɗawa Rauda shi hariji ne, amma ya fasa gara ya bari abun ya kankama, don shi yana jin ma zai iya canza kansa idan ta nuna ba za ta iya zama da hariji ba, ya haƙura kawai ko da sau biyu a rana take ba shi ya gode Allah, tun da har ita ce silar arziƙinsa ba zai bari wannan damar ta wuce shi ba, a fili ya furta "Alhaji Ashiru ga kuɗi ga Rauda".
Dubu É—ari biyu ya tanada zai ba da sadaki, dubu É—ari tashi, É—ari kuma bashi ya ci, sati uku da zuwan shi gidan aka É—aura aure, kasancewar Ustaz ya gama kashe Rauda da wa'azi da nasihohi a kan gudun duniya, kuma dama can ita ma tana da gudun duniya, shi yasa babu wani party da za a yi, kawai tarewa za ta yi, amma ta ce sai nan da sati biyu idan kammala shirinta.
Ranar da aka ɗaure Ustaz ya rasa ina zai saka kansa don daɗi, takaicinsa ɗaya ba yau za ta tare ba, tsakani da Allah ya matsu, ba don kar ta ga zalamarsa ba da ya roƙe ta su je gidan nasu ta rage masa zafi ko babu katifa, amma dai ya daure sai dai ya yanke ranar ya shirya zai faɗa mata shi wane ne.
Wajen tara na dare suna yin waya, ya ce"Amaryata".
Ta ce"Na'am angona".
Ya ce"Ina son mu yi wata magana da ke, akwai wata matsala da na manta ban faÉ—a miki ba, kuma babba ce sosai, ina fargabar ma kar ki ji ki fasa auren".
Ta ce"Subhanallah, mene ne?"
Ya ce"Don Allah ki yi min adalci, wallahi ina ƙaunarki, ni ma ba yin kaina ba ne, haka Allah Ya ƙaddara min, ke ce ƙarshen hope ɗina, idan kika guje ni na san shikenan kuma, ba baki nake yi wa kaiwa ba, ba zan sake samun mace ta gari ba".
Duk ta rikice ta ce"Don Allah ka faÉ—a min Sweetheart, mene ne wai? Duk ka tsorata ni".
Ya ce"To a gaskiya ni ba normal mutum ba ne kamar kowa, ni hariji ne, bi ma'ana mai yawan buƙatuwa, ina da yawan yin sex fiye da zatonki, shin za ki iya jurewa?"
Rauda ta yi dariya siriri har da rufe fuska saboda kunyar maganarsa, ta kashe wayar.
Ya sake kira ta ƙi ɗauka, sai washegari da ya kira yake jaddada mata, ta ce"Kar ka damu, in sha Allah zan iya".
Ita gani take mene ne wani abun damuwa don miji yana yawan yin sex? Sam ba ta san akwai wani hariji ba, kawai a tunaninta yawan yin sex yana nufin shi ɗan soyayya ne, tana da sha'awa mai ƙarfi, don wani lokacin har tana jin kamar ta fara biyawa kanta buƙata, amma da yake ta san illar hakan a addinance da kuma likitance sai take ta haƙuri da fatan Allah Ya kawo mata miji na gari, yanzu ta samu lafiyayye me za ta yi idan ba farinciki ba?
Ustaz ya ce"Amaryata kin yi shiru, shin za ki iya da ni? Matana biyu a kan haka suka rabu da ni, sun azabtar da ni, guduna suke su hana ni haƙƙina, don Allah ki zama mai share min kuka a rayuwar aure".
Ta ce"To ni ban san amsar da zan ba ka ba ne, kawai dai zan ce maka na gode Allah da ya ba ni lafiyayye miji, ka saka a ranka kukanka ya zo ƙarshe daga kaina".
Ustaz ya yi tsalle ya dire, farinciki kamar ya kurma ihu, ya dinga jero hamdala yana yi mata godiya da faɗin"Indai ni ne mijinki Rauda na ɗaga miki ƙafa ki shiga Aljanna, ina kyautata zaton za ki zame min Raudatul dunya, Allah Ya miki albarka matata".
Ta dinga dariya tana cike da farinciki, Allah ne ya É—ora mata soyayyar Ustaz, kuma ga shi ya cika mata burinta ya zama mijinta, sannan tana son miji mai ba da kulawa da nuna soyayya, da alama ta yi dace burinta ya cika, ta gode Allah da ya haÉ—a Ustaz da wawayen mata a baya, inda sun san abin da suke yi ta tabbata da yanzu ba su yi wasarere da shi ba har ta tsinci dami a kale".
Ya ce"Anya zan iya jiran lokacin tariyar nan kuwa? Don Allah a É—an rage kwanakin".
Ta ce"Gaskiya ba sai an rage ba, kuma ma ai ƙaruwarka ce, kai fa nake yi wa gyaran".
Ya ce"Gyara ko a gidanmu ai za ki yi".
Ta ce"A'a ka bari a hakan kawai kamar fa yau ne".
Suka yi sallama kowanensu cike da farinciki, bacci yana É—aukar shi ya fara mafarkin ga shi ya kasance da Rauda.
SAYYADA
Wani irin yanayi na shiga na ƙunci da baƙinciki, ga kuma fargabar irin yadda Sadam zai kalli lamarina, na saka damuwa a raina na yi ta zaman kaɗaici, Mama kuwa ta ba wa banza ajiyata, gaisuwa ce kawai take haɗa mu, sai dai idan tana yin aiki na je na karɓa wataran ta ba ni, wataran ta ƙi sakar min, Baba kuwa da bai san abin da na aikata ba, ƙalau muke da shi, kullum zai shigo min da leda, kayan marmari ko ɗan nama, sannan kullum zai kawo zogale ɗanye na dafa ko kuma dafaffe, na yi kwaɗon shi, cikin wata ɗayan ko da wasa ban fita ba, ga shi Mama ba ta ba ni wayata ba, kuma ban tambaye ta ba, akwai ranar da ta tafi unguwa, na shiga ɗakinta, na dinga bincike, da ƙyar na gano wayar, sai dai na yi saranda, ganin layukan cikin wayar an tattauna su an watsa su cikin ledar da aka ƙulle wayar, takaici ya saka ni fashewa da kuka, na san Saddam yana can yana ganin na yaudare shi, da wane idon zan kalle shi? Duk da dai ta wani fannin ina farinciki da rashin zubewar cikin.
Sanda na shiga wata na biyu da faruwar wannan abun, watarana Mama ba ta nan na shiga maƙota na ari waya, hannuna yana rawa na saka lambar Saddam, plashing ma na yi don babu kati a wayar, na yi sa'a ya kira, na shiga gidanmu na rufe ƙofa har da saka sakata, na shiga ɗaki na kwanta sannan na ɗaga wayar.
"Hello, Hello da wa nake magana?"
Muryarsa ta sa na ji wani rauni ya rufto min, zuciyata ta fara kumburowa, kawai na saka kuka, da kukan ya gane ni ce, ya ce"Sayyada".
Na ce"Na'am".
Ya ce"Ba ki da abin da za ki ce min Sayyada, kin bayyana mini komai a aikace ai".
Ya katse kiran, na tashi zaune na sake yi masa plashing, bai kira ba, ai kuwa na dinga jera masa babu ƙaƙƙautawa, sai ga shi ya gaji ya kira, ya ce"Sayyada me kuka za ki ce min? Ni dama na san tun da kika tsane ni ba za ki ƙara sona ba, saboda ba ki da yafiya, ba ki da adalci, amma abin da ya ba ni mamaki shi ne me yasa za ki yaudare ni ki yi min ƙarya? Haka kika tsara ko? Shikenan ki je ki haihu Sayyada, ki koma gidan harijin mijinki ya dinga yi miki abin da ya sabar miki da shi, wanda ni ba zan iya ba, tun da ni ba doki ba ne, ba kuma jaki ba ne, dama na san kina son shi dole za ki koma, shi yasa kika ɗauke ni wawa wanda ban san me nake yi ba, ki je ki haihu, ki haifi yara dubu ma Sayyada, Allah Ya sauke ki lafiya, amma bari ki ji na faɗa miki, ba ki da adalci, ba ki da kirki, ba ki yi min adalci ba, kuma duk ranar da kika sake kirana ko kika gan ni a hanya kika nuna kin taɓa sanina, za ki sha mamakin wulaƙancin da zan tata miki".
Ya kashe wayar, na ajiye wayar hannu na rushe da kuka, na kifa kaina a cinyata ina ta yi, sai da na yi mai isa ta sannan na fita na wanke idona na mayar da wayar, na dawo na kwanta, zuciyata tana ta zafi, wai da me zan ji ne? Ga Mama tana fushi da ni, ga shi wanda ya ja mini fushin nata shi ma ya ƙi fahimtata, ina suke so na saka kaina ne? Na shafa cikina na ce"A kanka ne komai yake faruwa, amma ba ina nufin laifinka ba ne, zan haife ka in sha Allah, ba zan sake yunƙurin kashe ka ba, tun da wanda na so yi domin shi bai yi mini yardar da zai tantance abin da zan iya da wanda ba zan iya ba, Astagfirullah Allah".
08028966015
[28/10, 7:49 pm] Sadiya Abdulrazak: 30
USTAZ