← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 89

Sashe 35

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bacci ya kwashe Ustaz, zuwa azhar ya tashi, ya ji an shiga sallah a masallacin asibitin, ya ce"Subhanallah! Alhamdu billahillazi ahyana, ba'ada ma amatana, wa ilaihinnushur".

Ya yunƙura ya tashi, jikinsa duk babu ƙwari, sai yake ganin duhu-duhu tamkar duhun magriba, ya ɗauki wayarsa dake gefen gadon ya danna, ya ga ƙarfe biyu saura, ya ce"To ya aka yi na ga garin duhu? Ko dai dare biyu za a yi? Subhanallah da alama yau ana kusuf al shams, bi ma'ana rana tana rashin lafiya, ya zama dole na yi sallar da ake yi yayin faruwar haka".

Ya sauke daga gadon, yana miƙewa tsaye ya ga duhun ya ƙaru, kansa ya fara juyawa, ɗakin duka juya masa yake yi, yana ta ƙoƙarin laluben bango ya dafa shi ya fake, amma ya ji kamar wan yi sama da shi an maka shi da ƙasa, ji kake yifff, daidai lokacin kuma Baba ya shigo ɗakin don ganin jikin nasa, kawai ya gan shi wanwar a ƙasa, Baba ya fara salati ya fita da sauri ya kira likita, aka kwashi Ustaz aka mayar gadon, likitan yana mita da faɗin dama ya san za a iya yin haka, ƙarshe dai Ustaz sai da aka ƙara masa jini leda biyu, da na yayansa da na ƙaninsa, don Baba wayarsa ya ɗauka ya duba lambar mahaifinsa ya sanar da shi.

Lokacin ita Sayyada ta dawo normal, amma sai kuka take yi na rasa É—anta a karo na biyu, Mama duk ta damu ta ce"Sayyada ko dai da laifin mijinki a zubewar cikin nan?"

Sayyada ta kalli Baba, sai ta girgiza kai ta ce"Babu, Allah ne ya ƙaddara".

Mama ta ce"A'a Sayyada na san halin mutum hariji..."

"Saboda kin zauna da shi ko?" Baba ya katse ta da faÉ—in haka yana haÉ—e rai.

Ya ɗora da faɗin"Shikenan ciki ba zai zube ba idan Allah Ya ƙaddara? Duk matan da suke ɓarin ciki mazajensu harijai ne kenan? Kalmar hariji ta fita daga bakinki, ba na son neman fitina".

Mama ta ce"Na tabbata idan ba shi ya zubar da cikin nan ba, to baƙincikin da yake ƙunsa mata ne, don haka wannan karon ba za ta koma ba".

Na share hawaye na ce"Mama zan koma, in sha Allah ba zan sake yin yaji ba, zan zauna na jure komai, idan kun ga na gaza to na mutu ne, ka kwantar da hankalinka Baba, na yi alƙawarin ba zan sake kawo ƙarar mijina ba, zan zauna da shi a yadda yake, roƙona ɗaya kawai shi ne Baba ka dubi azabar da nake ciki da sunan aure, ka yafe min bayan mutuwata".

Jikin Baba ya yi sanyi, amma ya dake bai ce komai ba ya fita ya bar É—akin.

Mama ta ce"A'a Sayyada na za ki koma ba, wallahi ba za ki kashe kanki ba, daga nan gida za ki koma".

Na ce"A'a Mama daga nan gidana zan koma in sha Allah, ki taya ni Baba ya aminta da ni".

Mama ta ce"Amincewar Allah kawai za ki nema Sayyada ba ta mutum ba".

Na ce"Ta shi ɗin ma ina buƙata".

Mama ta ce"Ba za ki iya ba Sayyada".

Na yi murmushi mai ciwo hawaye bai bar zuba ba na ce"Zan iya in sha Allah, sai dai gawata ta faÉ—a muku na gaji ba dai ni da bakina ba".

Ustaz yana kwance hajaran majaran, ido ya yi zuru-zuru, don ma ya ci faten wake mai alayyahu da kifi, sannan ya sha maltina da madara, ya sha fruit,kana kallonsa ka san yana jin jiki amma don ƙarfin hali faɗi yake"Alhamdulillah, ko mutuwa na yi ba ni da kaico, tun da kamar jihadi ne na yi, bi ma'ana na kare matata daga gudanuwar jinin wani ƙato a jikinta, Alhamdulillah!"

Da Baba ya ce da Sayyada tun da nata jikin da kwari ta je ta duba jikin mijinta, haka ta je ba don ranta ya so ba, ta yi masa sannu, ya amsa shi ma yana yi mata sannu, zai fara yi mata surutu ta fice daga ɗakin, a asibitin dai suka kwana, washegari aka sallame su, Mama ta yi, ta yi Sayyada ta zo su tafi gida sai jikinta ya ƙara kwari, amma ta ƙi, shi kuma Baba ya fa faɗan da gaske Mama ce take so ta kashe mata aure, a dole ta koya mata yadda za ta dinga kula da jikinta, sannan ta ce za ta dinga zuwa tana duba ta, suka rankaya ita da Ustaz suka tafi gida.

Ustaz fa ya narke da gaske har lokacin jikinsa bai dawo daidai ba, ga shi an ce dole shi da Sayyadar su dinga cin abinci mai gina jiki, haka ya lallaɓa ya je ya yi musu cefanen kayan miya, har da alayyahu da kifi, ya zo ya ajiye a kitchen, ya shigo falon da nake a kwance ya ce"Assayyada, daure ki fito ki ɗora mana abinci, ga shi nan na siyo har da kifi".

Na tashi na fita, na shiga kitchen ɗin, na buɗe ledar na yi zaton zan ga ɗanyen kifi, kawai sai na ga soyayye ne, irin ƙawarar nan mai ƙaya a jikinsa, ya ƙaraso kitchen ɗin ya ce"To kin ga kifin da aka samu, sai a ƙarshen girkin za ki saka shi, bi ma'ana idan abincin ya ɗakko tsotsewa, sai ki zuba shi a ciki ki juya, ai ina ga ma tun da ga alayyahu nan za ki cika a abincin, shinkafar sai ki dafa gwangwani biyu da rabi maimakon uku da ake dafawa, tun da ba lafiya gare mu ba".

Ko kallon shi ban yi ba, na hau gyara kayan miyan, gwangwani biyar na dafa a maimakon huɗu, na cika masa faranti kuma ya cinye tass, ni kuma na ci kaɗan, don bakina babu tes, na sha magani na yi sallah na kwanta, da yamma Anisa ta zo ta duba ni har da yo min jar miya mai yawa, mai cike da nama, da kuma gasasshen nama cikin 'yar kula, na karɓa kadaran kadahan, tana zuwa ya fita, kuma har ta tafi bai dawo ba, tana tafiya ni ma na saka hijjabi na fita, na je na ciri kuɗi, na sayi kayan shayi manyan gwangwani, maltina katan ɗaya, ƙwai, cornflakes, golden morn, suga, da babban biredi da butter, indomi kwali ɗaya, don ba zan bari ya kashe ni da yunwa ba, kuɗin nan kuma ko ma wane ne ya turo min, ko mene ne manufarsa ta ba ni kuɗin ni dai ci zan yi, tun da ina da buƙata.

Da na ga na mallaki wannan kayan shikenan ba na yi masa girki, ko ya yi ko ya siyo a waje, ni kuma idan ba ya nan zan fita na siyo alayyahu da kifi ko nama na yi girkina iya cikina na ci na yi wanke-wanke don kar ya gane.

Kwana biyu da dawowarmu daga asibiti, ya fara nuna rashin haƙurinsa, haka zai yi ta naniƙata yana tumirmushe ni da sunan samawa kansa nutsuwa, ni kuwa har ba na fatan ma na samu tsarki nan kusa.
[15/10, 7:17 pm] Sadiya Abdulrazak: 22

Wani irin zama muke yi da shi, babu gaisuwa, idan ya yi min magana sai wacce na ga dama zan amsa, saboda sosai nake jin tsanar shi a zuciyata, kullum sai ya yi mini nasiha da wa'azi mai tsoratarwa a kan wannan abin da nake yi masa wulaƙanci ne, haka kullum sai ya tambaye ni ko na samu tsarki? Ba na kula shi, sai dai idan yana samawa kansa nutsuwa ya taɓa ya ji, sai ya ce"Subhanallah! Allah Ya kawo mana ƙarshen abun nan".

Kwana na takwas da zubewar cikin jinin ya É—auke na yi tsarki, ranar na makara sallar asuba, bai tashe ni ba saboda bai yi zaton na fara sallah ba, ina tada sallar ya dawo daga masallaci, ya yi turus, sai kuma ya fara murmushi ya ce"Alhamdulillah! Ma sha Allah!".

Ya tuɓe ya zauna a bakin gado yana jira na idar, ina idarwa ya ce"Assayyadata".

Ban kalle shi ba ballantana na amsa, ya fara girgiza kai alamar jimami kafin ya yi gyaran murya ya ce"Subhanallah! Kaico! Kaicon mutanen da suka shagala da ruɗin wannan zamani, kaico da nasara da ya kawo mana abubuwan da suke canza al'ada wasu har ma suke taɓa addini, yanzu Assayyada dama kin yi tsarki, kin zama tsarkakkiya kuma halattaciya a gare ni amma shi ne kika ƙi sanar da ni? Mu fa ba turawa ba ne, mu musulmai ne, ke kin san babu abin da nake jira a 'yan kwanakin nan kamar a ce kin samu wannan tsarki, amma kika yi biris kika bar ni a wahale, a jigace, a raunace?"

Idona ya kawo ruwa, amma ban bari ƙwallar ta sakko ba, na shiga ƙarfafar kaina da cewar na daina yin kuka a kan lamarin aurena. Mama ta kawo min maganin sanyi, da na ƙarin ni'ima, amma suna nan ban taɓa ko ɗaya ba, a ganina gyara jikinsa tamkar ƙara zuga shi ne ya sake maƙale min, gara na zauna a yadda nake ko Allah zai sa ya ga canjin ya yi yawa ya ja baya da ni.

Ya ce"Hmm, shikenan na yafe miki, sai dai kuma ya za ki yi da alhakina da kika É—auka?"

Ya taso ya ɗaga ni tsaye, yana kallon fuskata, na sunkuyar da kai baƙinciki kamar zai kashe ni, ya ce"Assayyadda ni mijinki ne, kuma wannan haƙƙina ne dole ki ba ni ko ba kya so, sannan ina jiye miki zuwan ranar kuka, bi ma'ana ranar da turar da kike yi min za ta kai bango, har zuciya ta ci galaba a kaina na aikata abin da ba shi Kenan ba, wallahi Assayyadda sai ƙaddara ta saka kin auri wani za ki gane ashe ni ɗan baiwa ne kuma Allah yana sonki da ya na ki ni a matsayin miji".

Ganin dai ba zan kula shi ba, ya shiga raba ni da suturar jikina, yana yi yana tasbihi kamar yadda ya saba, ya gama ya ja ni zuwa gadon.
Chapter 35 · 0% Book details