← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 89

Sashe 39

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na gyaÉ—a mata kai, amma na kasa jin daÉ—i da jin wai Baba ya fahimce ni, ta fita ta kira likita suka shigo tare da wani likitan da ban, aka yi min tambayoyin me nake ji, na ce"Ciwon kai kaÉ—an, zafin zuciya, sannan na gaji da duniyar, na gaji da aure, don Allah a yi min allurar mutuwa idan akwai".

Ɗayan likitan wanda ya kasance counselor ya ja kujera ya zauna ya ce"Ki kwantar da hankalinki Sayyada, a nan ba mu da allurar mutuwa, amma za mu iya ba ki shawarwarin da idan kika bi za ki ji ba sai kin mutu ne kika samu maganin matsalarki ba, za ki samu farin ciki ki fita daga ƙuncin da kike ciki, sannan za ki dawo mutum kamar kowa".

Na ce"Ba zai yiwu ba, so nake na mutu kawai, ya cuce ni, na tsane shi, ya riga ya kashe min zuciya da gangar jiki mene ne ya rage min kuma? Laifin me na yi ne? Na yi iya yina na gaji, ba ni da wata mafita a yanzu sai ta mutuwa kuma".

Ya ce"Tabbas kin yi ƙoƙari Sayyada, kin yi abin da kowa zai yaba miki tun farko ke jaruma ce, daure ki ƙara haƙuri kaɗan, ki ajiye batun mutuwa, a baya kin rasa 'yancinki yanzu lokaci ne na ƙwatar 'yancinki, har yanzu ke mutum ce kamar kowa, kina da damar gyara gobenki, ki manta da batun damuwar mijinki gabɗaya, ki fuskanci sabuwar rayuwa, mijinki shi ya haife ki?"

Na girgiza kai alamar a'a ina hawaye.

Ya ce"Da shi kika taso tun ƙuruciya ko daga baya kuka haɗu?"

Na ce"Sai daga baya".

Ya ce"A baya rayuwar da kika yi babu shi mutuwa ce? Kafin haɗuwarki da shi ba ki taɓa yin rayuwa farin ciki ba?"

Na ce"Na yi".

Ya ce"To kin ga idan haka ne ba shi ne ainahin farincikinki ba, saboda haka mantawa da shi da matsalarsa ba wani babban abu ba ne".

Na ce"Ya zama dole na zauna da shi, saboda umarnin mahaifina ne, ba ni da burin da ya wuce Baba ya yafe min, kuma ya ce zamana da shi shi ne tikitin yafiyar".

Ya ce"Ai yanzu Baba ya canza, ya yarda ki rabu da shi har abada, kuma ya ce ya yafe miki, kullum yana faÉ—ar ya yafe miki, yanzu ma ya bar asibitin nan, idan ya dawo da daddare za ki ji daga bakinsa".

Na yi shiru kawai, sai na ji ban wani ji daɗi sosai ba, na yi zaton idan na ji Baba ya yafe min har daka tsalle murna zan yi, amma yanzu na nemi farinciki na rasa, sannan ba baƙinciki nake yi ba, babu yabo dai babu fallasa, ni dai fatana a ce da gaske zan rabu da auren nan na ƙaddara.

Kalaman kwantar da hankali da ƙarfafa gwiwa sosai ake yi mini, a hankali na fara jin nutsuwa, irin wacce na rasa tun ranar da na tare a gidan Ustaz, hankalina ya ƙara kwanciya ganin yadda Baba yake ta nan-nan da ni, yana maimaita ya yafe min, kuma za a raba aurena da Ustaz, abin da ya sa na ƙara yarda shi ne ko sau ɗaya ban ga Ustaz ya zo duba ni ba.

Satina É—aya a asibiti aka sallame ni, sai dai zan dinga ziyartar counselor a sati sau biyu, yana tabbatar da samun lafiyata.

Alhamdulillah na ji daɗi da na ga an wuce da ni gidanmu ba gidan Ustaz ba, sannan ga kayan sakawata nan duk an kwaso min, Mama ya cigaba da kwantar min da hankali, na fara warwarewa ina samun sauƙin zuciya sosai, kullum sai Baba ya tambaye ni abin da nake so ya siyo min, kowa tausayina yake ji.

Satina É—aya a gida wataran da yamma Baba yake ce min yau Ustaz zai zo mu tattauna, gabana ya faÉ—i na ce"Baba me zai yi min?"

Ya ce"Ai dole zai zo dama, tun da ba sakinki ya yi ba, a yanzu magana ta ki ce, idan kin ga kin komawa aurensa to da son ranki ne, idan kuwa ba ki amince ba babu wanda zai sake yi miki dole".

Hankalina ya É—an kwanta, amma cikin zuciyata ina fargaba, ko son ganin shi ba na yi.

[20/10, 7:45 am] Sadiya Abdulrazak: 24

Haka na yi wunin ranar suƙuƙu kamar mara lafiya, duk da Mama tana ta kwantar min da hankali, ana idar da sallar isha'i sai ga shi ya kira waya, na kalli sunan Malam Ashiru da yake yawo a screen ɗin wayar, gabana ya ba da rass, na ɗauka da sallama, ya ce"Wa Alaikissalam, Assayyaddata".

Na yi shiru kamar ban ji shi ba, ya ce "Ga ni a ƙofar gida, ya za a yi? Fitowa za ki yi ko shigowa zan yi?"

Sai kawai na kashe wayar, na leƙa tsakar gida kamar zan yi kuka na ce da Mama"Mama wai ya zo".

Mama ma gabanta ya faÉ—i ta ce"To! Anya kuwa ya shigo? Ina tsoron kusancinku da mutumin nan Sayyada".

Na ce"Mu tsaya a wajen kawai".

Ta ce"A'a ai mijinki ne, babu daÉ—i ku tsaya a waje, ya shigo É—in, amma don Allah ki kama kanki Sayyada, ki tuna wahalar da kika sha a hannunsa, da shi kafin ki fara sauraron daÉ—in bakinsa".

Na ce"Haba Mama, sai kace dama son shi nake?"

Ta ce"To ai tsakanin mata da miji sai Allah".

Na koma ɗaki a raina ina jin lallai Mama ba ta san yadda na tsani Ustaz a raina ba, hijjabi na saka na leƙa ƙofar gidan, da yake layin namu akwai sola, tarr na kalle shi cikin hasken ƙofar gidan, ya sha wata shadda ɗinkin babbar riga kamar wanda zai je ɗaurin aure, ko ma a ce shi ne angon, hannunsa riƙe da wata leda, muka haɗa ido ya washe min baki yana murmushi, na ɓata rai na ce"Ka shigo".

Ya biyo ni yana cewa"Assayyada babu ko sallama ballantana gaisuwa?"

A tsakar gida ya tsaya ya gaishe da Mama, sannan ya ƙaraso ɗakina, ya zauna idonsa a kaina kamar zai cinye ni don kallo, na ce"Ina wuni".

Ya yi murmushi ya ce"Lafiya lau Assayyada, ya jikin naki?"

Na ce"Da sauƙi".

Ya ce"Ai na ga alama kam, wannan ai kin riga kin warware ma".

Na yi shiru.

Ya rage murya tare da nakashe ta cikin yaudara ya ce"Assayyadata kin yi ƙiba abunki ma sha Allah ! Ni kuwa ina ta ramewa, shin da gaske ba kya kewata? Ni fa kin ga rashinki ya sa duk na firgice, ko baccin kirki ba na iya yi wallahi, bi ma'ana babu nutsuwar gangar jiki, idan na dawo gidan sai na ga kamar kango, babu mai tarairayata ta ɗauki laurarata, ke fa? Ba kya jin cewa rayuwarki ba ta cika ba saboda ba ma tare? Wai ma don Allah kina sona? Na yi kuskure da ban yi miki wannan tambayar ba, kuma na mayar da hankali don samun amsa, bi ma'ana na fahimci kina sona ko ba kya sona".

Na ce"ÆŠan Ustaz".

Ya yi wata dariya mara sauti sosai ya ce"Sunan da na samu kenan?"

Na ce"Bari ka ji na faɗa maka, ni ba na sonka, ban taɓa sonka ba, ai ba ka yi abin da zan so ka ba a duk tsayin zamanmu, don haka ban taɓa kewarka ba, kuma ba na fatan zuwan ranar da zan yi kewar miji irinka".

Ustaz ya fara girgiza kai, ya ce"Ya subhanallah! Subhanallah Assayyada ki yi gaggawar faɗin Astagfirullah bi ma'ana ki tuba, saboda kin aikata tsaka-tsakiyan saɓo, e don ba a ce masa babba ba, tun da zai iya yiwuwa suɓutar kalam ne, kuma ni a bisa adalcina na yafe miki, e idan don ta ni ne dai wallahi na yafe, sai dai kuma ya za ki yi da hadisan da suka yi magana a kan girma da hakkin miji a wajen matarsa? Anya kuwa Assayyada?"

Na kawar da kai gefe.

Ya ce"Kodayake, ni ma da nawa laifin, duba da ganin yadda wato ainafin na biyewa sharrin rauni na zuciya da gangar jiki, na dinga sauke miki buƙatata ba bisa ƙa'ida ba, duk da ba wai na kauce hanya ba ne, Lala-lala ina kan hanya tun da ai hakkina ne, kuma shi harkar raya sunna wanda masu hikima suka ce kashe arna haƙiƙa shi ne auren, idan babu shi babu jin daɗin aure, sannan babu haihuwa, to na sani ban yi duba da ba ki da lafiya ba a ranar da abin ya faru, hakan kuwa ya faru ne biyo bayan kaidi na mace, wato bi ma'ana ke".

Hararar da na galla masa ce ta saka shi dakatawa bai shirya ba, ya runtse ido ya ce"Assayyada haƙiƙa da sauranki a sanin darajar miji, ba don ina yafe miki ba da sai kin halaka, kin tashi cikin mata rafkanannu masu yawan zunubi, bi ma'ana waɗanda ba su da rabo".

Ya ɗora da faɗin"To abin da ya sa na ce kaidi na mace shi ne wannan farar cinya taki da na gani a daidai lokacin, haƙiƙa ita ce ta ruɗe ni na kasa riƙe kaina, kada ki manta ni hariji ne Assayyada, wallahi a hakan ma ina iya yina don ganin na sassauta miki tun da na gane kina da rauni".

Na ce"Tun da har ka faÉ—a da bakinka kai hariji ne, to Alhamdulillah, idan har kana da adalci ka san ba zai yiwu a zauna zaman aure da hariji da mai lafiya ba ko?"

Ya ce"A'a Assayyada ai shi ma hariji ba mara lafiya ba ne, hasalima ya fi kowa lafiya ta wannan fanni, kawai dai halitta ne, da kuma laruri bi ma'ana mu mace ba ta taɓa gamsar da mu ko za mu dawwama a tare, wannan shi ne".

Na ce"To ai kamata ya yi a ce ku dinga neman mace harija, wato mai irin lafiyarku, idan kun ga dama kar ma ku dinga tsayawa sallah da cin abinci, tun da dai cewa aka yi abin da aka halicce ku don shi kenan".
Chapter 39 · 0% Book details