← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 89

Sashe 63

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Takanas ya saka shi a addu'a a wannan daren, yana mamakin irin zuciyar shi, bai faɗaqa Zulaiha shi hariji ba ne, saboda ya yi alƙawin zai rage, ba zai takurata sosai ba, sannan sati ɗaya da auren ma ya kama zai tafi Cotonou, da ranar ta zo aka ɗaura auren Ustaz a karo na huɗu, yana ta farincikin yau zai sauke nauyin da ya jima bai sauke ba, bayan an kawo amarya kowa ya watse suka shiga firar farinciki ana cin kaza, ita ma yarinyar tana son shi, don haka ta so ta saki jiki a wannan daren ta ba shi farinciki, amma Ustaz sai da ya ƙaryata jarumtarta, don tun yana lallaɓawa yana binta a hankali har dai ya manta da amarya yake tare, don haka sosai ya jigata ta, kuma da asuba ma duk yadda ya so daurewa kasawa ya yi sai da ya ƙara nemanta, da rana ma kafin a fara yin baƙi ya yi, ai kuwa cikin wuni ɗaya yarinya ta firgice ta yi zuru-zuru, idanunta sun kumbura, ga wani tsoron shi da ya shiga zuciyarta, ta yi kuka babu adadi kafin la'asar 'yan'uwanta su zo.

Suna ganinta a haka suka san abin da ya faru, amma a zaton su raki ne kawai ya saka ta wannan firgicin, da suka tambaye ta ta fashe da kuka tana cewa"Ba zan iya ba Anti, wallahi kashe ni zai yi".

Yayar tata ta fara dariya tana tuna yadda Zulaiha ta dinga rawar kai da aka haɗa mata magunguna, na sanyi sai da ƙyar take sha, amma daka da tsumi haka ta dinga sha babu ko jin kunya, shi ne a kwana ɗaya za ta karaya? Suka dinga kwantar mata da hankali da faɗin za ta saba, kowa ma a haka ya saba, haka suka tafi suka bar ta bayan sun yi mata girkin dare, ta dinga jin kamar ta bi su.

A daren ma Ustaz bai tausaya mata ba, saboda ko ya ce zai rabu da ita, sai ya ƙi kamar mayen ƙarfe yana jan shi, dole ba zai iya jurewa ba, a ranar ta uku kuwa dare yana yi ta rufe ƙofa, duk wa'azin shi da magiya, tare da alƙawarin yau ba zai yi mata komai ba ta ƙi buɗewa, haka ya haƙura, daga ranar ba ta sake yarda da shi ba, sai ana gobe zai yi tafiya ya samu nasarar dirtse ta da rana ya yi ta ƙarfi, ai kuwa washegari yana tafiya ta haɗa kaya ta tafi gidansu, a ƙa'ida kuma cewa aka yi kakarta, za ta zo su zauna, ai kuwa ta koma gida tana ta kuka, ta ce ita fa na za ta koma ba sai dai ya sake ta, kuma tambayar duniyar nan ta ƙi faɗar dalili, aka tambaye shi ta waya shi ma ya ce bai san dalili ba, a dole aka bar batun ana jira ya dawo a tattauna.

SAYYADA

A hankali na saba da rashin fita waje, da kuma rashin Saddam, ba don na manta da shi a zuciyata ba, kuma soyayyar shi tana nan daram, sai dai kawai na danne, har na yaye É—ana yana wata goma sha shida babu wanda ya zo ya ce yana sona, to wa ma ya san ba ni da aure ban da 'yan cikin unguwarmu? Tun da ba fita nake yi ba, ban ga ta inda zan haÉ—u da wani har ya ce yana sona ba, kuma ni hakan daÉ—i yake yi min sosai.

Ana haka ne wataran kawai Baba ya ce min yau zan yi baƙo, gabana ya faɗi na ce"Baba baƙo kuma?"

Ya ce "E baƙo, magidanci ne mai hankali, ya zo sati biyu da suka wuce mun yi magana da shi, kuma na fahimci aurensa ne ya dace da ke, matarsa ba ta haihuwa shi ne yake so ya ƙara aure, ba shi da wata matsala, don 'yar'uwarki Anisa ce ta ba shi labarinki, Ogan mijinta ne a wajen aiki, ya ba shi cigiyar ya samo masa mace mai hankali, shi ne yake bawa Anisan labari dayake tana sonki da arziƙi sai ta ce ga ki nan, yanzu haka ya ga hotonki kuma ya ce kin yi, saboda haka yau zai zo ku gana, ina fatan ba za ki yi abin da za ki kunyata ni ba ko?"

Na jinjina kai alamar e, wani abu ya taso ya tokare min ƙirji, ko zan yi hasashen ga ni na yi aure da Sadam kawai nake hangowa a gidanmu da muka yi rayuwa, ta ina zan fara rayuwa da wani ba shi ba? Kuma wai ma yana da wata matar, sannan auran ma don yana son haihuwa ne zai yi, kenan ma abin da zan haifa zai so ba ni ba, na share hawaye da ya sakko min.

Har ji na yi kamar zazzaɓi zai kama ni, da yamma ya zo, zan fita Mama ta ce min"Sayyada a matsayina na mahaifiyarki ina ba ki shawarar ki saurari mutumin nan ki ba shi dama, a kan Sadam kike yin komai, kuma ni da mahaifinki mun lashi takobin ba za ki aure shi, don haka ki bawa wannan ɗin dama".

Na ce"To" A sanyaye na fita.

Na yi zaton zan ga irin ɗirka-ɗirkan mazan nan masu ƙiba, sai na ga saɓanin haka, ba dai siriri ba ne, amma ba za a kira shi da lukuti ba, ban ma wani ƙare masa kallo ba ballantana na gano muninsa ko kyau, na yi sallama, ya amsa, na yi shiru ina jira na ji ta inda zai fara, dai ji na yi ya ce"Ke ba ki iya gaisuwa ba ne?"

Na ce"Ita ka zo ji?"

Ya yi shiru na 'yan sakanni kafin ya ce"A'a, ganinki na zo, kuma na ganki kin yi, duk da ba ki da kunya, amma ki kwantar da hankalinki in sha Allah zan aure ki a hakan, to ni fa? Na yi miki?"

Na ce"Ba ka yi min ba, kuma ba za ka taɓa yi min ba, sannan rashin kunya kaɗan ma ka gani".

Ya jinjina kai ya ce"Na yi ko ban yi ba wannan ba zai zama damuwa ba, tun da dai mahaifinki ya ce ya ba ni ke, kuma na ga kin yi min, to ki kwantar da hankalinki in sha Allah za a yi auren, kuma shi ma rashin kunya da kike ji da shi, ki kwantar da hankali zan sauke miki shi da izinin Allah".

Na ce"Idan ka gama zan tafi".

Ya ce"Babu damuwa, na lura ba kya sona, amma ki kwantar da hankalinki ni ban damu sai kin so ni ba, indai za ki dinga bari na yi amfani da ke a matsayinki na matata to babu damuwa".

"Amfani?" Na maimaita kalmar a zuciyata, wannan anya kuwa ba É—an iska suka turo min ba?

Ya ce"Ki je gida ki kwantar da hankalinki, na cewa Baba ya ba ki wayarki, amma ya ce ba zai yiwu ba sai bayan aure, don haka zai iya kiranki a wayar Mama a kowane lokaci, sai ki tara, sai anjima, na bar ko lafiya".

Na daskare a tsaye ina bin shi da kallo, har wanda yake tsaye a jikin motar ya buɗe masa ya shiga suka ja suka tafi, baƙinciki ya yiwa zuciyata ƙawanya, na ƙara jin tsanar Anisata taso min, na shiga gidan, na fashe da kuka na yi ɗakina.

08028966015
[06/11, 5:05 pm] Sadiya Abdulrazak: 38

Na zauna na ci kukana, ina tunanin Anisa tana sane ta kawo min wannan ɗan iskan, mara mutunci, da Baba ya dawo ya kira ni, ya ce"Sayyada baƙonki ya zo, kin gan shi, ya yi miki ko bai yi ba?"

Da sauri na ce"Bai yi ba".

Baba ya ce"Mene ne matsalar shi".

Na ce"Kawai bai yi min ba".

Ya ce"To ai kuwa dole sai kin samo matsalar shi kafin a sallame shi".

Na rushe da kuka ina so na faɗa musu ni duk wanda ba Saddam ba ba zai yi min ba, amma babu dama, na dinga kuka ina jin ƙuncin zuciyata yana raguwa silar kukan, a halin da nake ciki kafaɗar da zan kwanta na yi kukan nake nema, amma babu idan ba ta ɗana ba, kukana ta taɓa zuciyar Mama, da alama ta fara tausayina, a sanyaye ta ce"Sayyada ya isa haka, ba fa son ki ne ba a yi ba, ke ce kika ja komai, kin yi abubuwan da dole za mu zarge ki ko da matar Saddam ƙarya ta zo ta faɗa mana, idan 'yar da kika haifa ce aka ɗarsa miki zargin tana aikata zina wane irin mataki za ki ɗauka? Ki yi wa kanki adalci mana, dole za a karɓu wayarki tun da ba kya jin magana, dole za a hana ki fita saboda kina taurin kai, idan aka bar ki ki fita ba za ki haƙura da Sadam ba, sannan tun da kin saba da aure ba za ki juri dogon zaman zawarci, shi yasa muke so ki auri wani".

Cikin kukan na ce"To don Allah kar ku yi min auren dole, ba na son mutumin nan".

Baba ya ce"Sayyada, na ji kokenki ba kya son auren dole ko? To zan dakatar da shi in sha Allah! Sai dai na ba ki wata É—aya ki fitar da wanda za ki aura, amma ban da Sadam".

Mama ta ce"Yawwa, kin ga kin samu sassauci, wannan shi ne adalcin da za mu iya yi miki, ki samo wanda kike so ki kawo, ban da Sadam".

Gani nake idan zan kewaye duniya ina duba maza da halayensu ba wanda zai yi min sai Saddam ɗin da ba sa so, amma sanin ba ni damar furtawa sai na ce"Baba ta ina wani zai gan ni ya ce yana sona? Ba fa na fita ko ƙofar gida, sannan a wancen karon haka suka dinga zuwa suna fasa auren, ba na so wannan karon ma ya faru".

Ya ce"To wannan kuma ke ta shafa, tun da dai ke ce kika ja wa kanki abin da za a fasa É—in ai, yanzu na janye takunkumin fitar taki, na tsayin wata É—aya, sannan za a ba ki wayarki".

Na ji wani daÉ—i ya ratsa ni.
Chapter 63 · 0% Book details