Sashe 37
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko da makaho nake zaune dole zai gane ina cikin damuwa mai tsanani, amma Ustaz kamar bai gane ba, kawai ba shi da wani buri sai na kwanciya da ni ya biya buƙatarsa. A hankali abubuwa suke ƙara ta'azzara, yanzu sai na yi kwana uku ban yi wanka ba, kayana duk sun yi datti ban wanke ba, idan na zauna ba ni da aikin yi sai tunani, tunanin da yake ƙara min zafin zuciya, sannan ina yawan zargin kaina, ko alwala na yi sai na ga kamar ba daidai na yi ba, sai na yi sallah na manta na yi na ƙara yi, ko kuma na dinga ganin kamar na yi, alhalin ban yi ba, ciwon kaina kuwa ya yi tsanani, ga rashin bacci, haka zan kwanta na yi ta tunani na kasa bacci, ko ya ce na tashi na yi sallah ba na yi.
Tun yana banza da ni har ya fara damuwa, ya sha zaunar da ni yana tambaya ta mene ne yake damuna, amma ko kallonsa ba na yi, saboda ni ma ban san abin da yake damuna ba, a hankali kuma na fara jin jiri, wani lokacin idan ya kwashe ni sai na tsaya na dafa bango, saboda duhu nake gani, idan na dawo normal sannan na cigaba da abinda nake yi, a haka nake yin girki, amma wanke-wanke na daina yin shi yadda ya kamata, É—aurayewa kawai nake yi, wani lokacin sai na ji kamar ana ihu a cikin kaina, ko na ji na tsani kowa, mutuwa kawai nake so, har na fara tunanin me zai hana na kashe kaina? Sai zuciya ta ce min ko zan mutu ba yanzu ba, na bari sai na haihu, na bar bayana wanda zai saka a dinga tunawa da ni.
Sai na fara tunanin idan na mutu ko Ustaz zai damu? Ko wa zai aura? Ko za ta iya zama da shi? Sai kuma na tuna ko Baba zai yafe min? Wane irin kuka Mama za ta yi? Kawai sai na fashe da kuka, na yi mai isa ta babu mai rarrashi, wataran kuma sai na dinga tuna rayuwata ta baya, ta gidan Sadam, lokutan farinciki nake tunawa, wanda a da na neme su na rasa sai na baƙinciki, yanzu suna ta dawowa kaina, sai na yi murmushi, idan na tuna wani abun kuma na ƙyalƙyale da dariya, kuka ko dariya duka ina yi a gaban Ustaz, don haka ya fara tunanin ina da aljanu.
Idan ina irin haka kuka ko dariya, ko kuma na zauna na ƙurawa waje ɗaya ido ya yi min magana na ƙi amsawa, sai ya yi addu'a a cikin ruwa ya zo ya dinga watsa min, yana tambayar "Su wane ne ku? Me kuka zo yi jikin matata?"
Idan yana wani surutan har dariya yake ba ni, sai dai kawai na yi murmushi.
Wata rana na tashi da ciwon kai mai tsanani, ko motsa kan na yi kamar na kurma ihu, ga jirin da nake ji yana kwasara, har dafa bango nake yi idan zan yi tafiya, daren jiya ban samu bacci ba ko na minti ɗaya, idona sai zafi yake yi, ina kwance a tsakar gida Ustaz ya zo kaina ya fara faɗa"Sayyada, ke Sayyada, wani sabon salon ne kuma kika samo? Yau da me za mu karya? Ki tashi ki ɗora, ko na kira mahaifinki na sanar da shi halin da ake ciki, a gaskiya na fara gajiya, 'yar nutsuwar da nake samu ma yanzu haƙuri kawai nake yi, bi ma'ana ɗanɗanon kullum raguwa yake yi, ga shi abu yana ƙara buɗewa, a gaskiya ki gyara".
Haka na tashi ina dafa bango na kunna wuta na dafa masa indomi, na koma na kwanta a falo, ya karya ya fita kasuwa, wajen sha biyu ya dawo kamar yadda ya saba, ina kwance a tsakar ɗakin ina jin dawowarsa amma ba ni da ƙarfin da zan ɗago ma na kalle shi, yana ta yi min faɗan ban ɗora girki ba, na yunƙura zan tashi na kasa, ni ina ta kaina shi kuma zani na da yaye ne ya sa shi matsowa ya fara shafa cinyata, a nan tsakar ɗakin ya raba ni da kayan jikina ya shiga biyawa kansa buƙata, numfashina yana ta sama da ƙasa ina jin kamar zan mutu, har dai na samu ya gama, ya shiga banɗaki, na yi jarumtar tashi tsaye, na ji kaina ya fara juyawa kamar ana hajijiya da ni, na tafi luuuu na zube a ƙasa.
Ustaz ya ji ƙarar faɗuwar Sayyada, a hanzarce ya karasa wankan, ya fito, ya same ta a wannan yanayi, ya shiga tashinta yana jijjiga ta, amma shiru, shi a tunaninsa aljanunta ne suka tashi, ya ɗakko zani ya lulluɓa mata, sannan ya yi addu'a a ruwa ya fara yayyafa mata, ya buɗe murya ya dinga yi mata karatun ruƙiyya shiru kake ji, ko motsawa ba ta yi ba.
Can dai ya É—akko waya ya kira Baba, suka gaisa ya ce"Baba wato akwai babban lamari da yake faruwa a nan gidan namu".
Baba ya ji gabansa ya faÉ—i ya ce"Subhanallah me ya faru?"
Ya ce"Wato ainafin ita Sayyada ce ta haɗu da laruri na aljanu, ina ta iya ƙoƙarina a kan lamarin, to yau dai ta faɗi, kuma na yi iya yi na na daga ilimin da Allah Ya ba ni domin na ga ta tashi ko kuma su aljanun su magantu a ji da wacce suka zo, ko kuma a ki wasu iri ne ma, farare ne ko baƙaƙe? Sannan Baba ka san su aljanu kala-kala ne, ka ga akwai Ruhanai, su an ce bayin Allah ne, sannan akwai..."
Baba ya ce"Haba Malam Ashiru! Yanzu a wane hali Sayyada take?"
Ya kalli Sayyadar ya ce"E to, ga ta nan dai a kwance, amma na faÉ—a maka na karanta Fatiha da Ayatul kursiyyu, amanarrasulu, sannan..."
Baba ya ce"Ga mu nan zuwa gidan".
Ya ce"To sai kun zo".
Da sauri Baba ya hau adaidaitasahun, sannan ya kira Mama ya sanar da ita, kusan a tare suka ƙarasa ƙofar gidan, Ustaz ya buɗe, Mama tana shiga ɗakin ta ga Sayyada kamar gawa, ya yafe zanin da ya rufe ta, ta gan ta tsirara, nan take ta zargi saduwa ya yi da ita har ta fita hayyacinta, ta kai hannu ta buɗe ƙafarta don tabbatarwa, ai kuwa ta samu tabbacin, Ustaz ya yi saurin barin ɗakin saboda tsananin kunya yana faɗin"Subhanallah!".
Ta saka mata kaya, suka kwasa suka tafi asibiti, amma ban da Ustaz, cewa ya yi bari ya nemo mukullin gidan idan ya rufe gidan zai biyo bayansu, saboda kar a tafi tare da shi a ce komai shi zai biya, amma ya san idan ya yi jinkiri, duka za su biya komai, kuma za su yafe masa tun da su ma 'yarsu ce.
[16/10, 4:14 pm] Sadiya Abdulrazak: 23
A daidaitasahu, Sayyada tana kwance jikin Mama, ƙafafunta a jikin Baba, duk jikinsa ya yi sanyi, ya fara tunanin tabbas Sayyada tana matsanancin hali, ta rame duka ta ƙare kamar ba ita ba, ita kuwa Mama kuka kawai take yi tana faɗin"Ya kashe ta, ya kashe min 'ya, Allah Ya saka miki Sayyada".
Baba ya ce"Don Allah ki saurara haka, yanzu da kike maganganun nan wa kike faÉ—awa? Ni ko mai adaidaitasahun?"
Ta ce"Allah nake faɗawa, duk da na san yana gani, ƙara nake kai masa ya bi wa 'yata hakkinta".
Baba ya ce"Ai shikenan, kya dai bari a je asibitin a ji me ya same ta, kafin ki É—ora laifi a kan wani".
Mama ta ce"Ai da gaske? Da gaske ba ka san abin da ya same ta ba? Tsirara fa na tarar da ita, ya gama biyan buƙtarsa ya kashe ta, ka san illar zama da hariji, na faɗa maka ga halin da take ciki, amma ka ce ta je ta mutu shi ne burinka, to yau ga shi ta mutu kowa ya huta".
Ta fashe da kuka sosai, har aka ƙarasa asibitin kuka take tana surutai, suna zuwa aka ba wa Sayyada gado a emargency, da kuɗi a account ɗin Baba, don haka komai ya zo da sauƙi, suka biya kuɗin komai aka duƙufa a kanta, Baba ya yi mamakin rashin ƙarasowar Malam Ashiru da wuri, kuma ransa ya ɓaci, suna nan zaune likitan da ya duba ta ya fito ya ce"Ina mijin yarinyar nan?"
Baba ya ce"Bai ƙaraso ba, sai dai ni mahaifinta".
Mama ta ce"Likita ya jikin nata? Ta mutu ko?"
Likita ya ce"A'a ba ta mutu ba, ta farfaÉ—o daga saman da ta yi, ta samu bacci, in sha Allah babu damuwa sosai".
Ya kalli Baba ya ce"Malam mu je office akwai bayanin da zan yi maka kafin mijin nata ya zo".
Mama ma ta tashi ta bi su suka shiga tare, Likita ya fara da faɗin"To a gaskiya kun yi sakaci da lafiyar 'yarku sosai, kuma abin da bincikenmu ya ba mu a yanzu haka 'yarku tana cikin stress ne, wato ciwon damuwa, wannan ciwon ba iya a gangar jiki yake ba, ciwo ne na ƙwaƙwalwa da zuciya, faɗuwar da ta yi yanzu alamu ne da ke nuni da zuciyarta ta gaji, ta gaza ba wa gangar jikinta gudunmawar da za ta iya zama lafiya ta yi rayuwa kamar kowa, idan ba a kula an yi taka-tsan-tsan ba, wannan cutar za ta iya kai ta ga mental breakdown, a yanzu ma haka dole abun ya taɓa ƙwaƙwalwarta, sai dai za ta iya warkewa idan ta fita daga cikin ƙuncin da ya haddasa mata faruwar hakan, sannan a kula da farincikita sosai".
Jikin Baba ya yi sanyi.