← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 89

Sashe 64

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ɗora da faɗin"Sai dai kuma, idan na samu labarin kina waya da yaron nan Saddam, ko kuma kun haɗu da shi ko sai ɗaya ne, to ki sani kina da zaɓi biyu a lokacin, ko dai na aura miki wanda na so a ranar, ko kuma na zare hannu a lamarinki ki bar min gida bari na har abada don ni ba ƙaramin yaro ba ne da za ki dinga raba min hankali".

Na jinjina kai, alamar na yarda amma a zuciyata ban yarda ba, Mama ta shiga ɗaki ta ɗakko min wayoyin ta ba ni, na karɓa jikina yana rawa, sai tsakar dare aka kawo wuta, amma haka na bi daren na saka caji, na kunna ta wajen Sadam, na yi mamakin ganin babu saƙon shi, dama whatsApp tuni ya yi expire, na saka kati ta bankina na sayi data, na sauke whatsApp ɗin, na nemi lambar shi, na yi masa sallama, don ma dare ne na san yana bacci da kiran shi zan yi.

Ai kuwa da asuba ina idar da sallah na kunna data, ban daɗe a online ɗin ba na ga ya ƙi hawa, kawai na kira shi, tun da na san ai ba shi da aure ba laifi ba ne idan na kira shi, ya ɗauka da sallama, na amsa na ce"Ka tashi lafiya?"

Ya ce"Lafiya ƙalau".

Na ce"Sadam, na yi kewarka sosai".

A takaice ya ce"Ok".

Jikina ya fara yin sanyi na ce"Amma ba ka yi kewata ba ko? Na ga kamar babu shauƙi ko zumuɗi a muryarka".

Ya ce"To so kike na kashe kaina saboda ke? Sayyada ba kya sona, shi yasa kika karɓu hukuncin da iyayenki suka yanke a kan soyayyarmu, wallahi ni kin ba ni mamaki matuƙa".

Kamar zan yi kuka na ce"To ya zan yi? Iyaye ne, sannan sun toshe duk wata kafa da za ta sada ni da kai, ba na son yawan saɓa musu a yanzu aljannata a ƙarƙashin ƙafarsu take, don Allah ka fahimce ni".

Ya ce"Fahimta ai na gama tun da kika nuna min ba ki damu da ni ba, sannan kar ki sake kirana a daidai wannan lokacin".

Na ce"Me yasa?"

Ya ce"Saboda na yi aure, hakan zai sosa ran matata, yanzun ma falo na fito nake É—aga wayar".

Kalmar 'Na yi aure' ta shiga amsa kuwwa a kunnena, fitar numfashina ya canza nan take, na ce"Ka yi me ka ce?"

Ya ce"Na yi aure, na auri wacce take sona, yanzu haka ma tana da cikin wata biyu, zai fi miki kyau ki je ki cigaba da bin umarnin iyayenki".

Wani irin ƙunci ya mamaye ni, duk yadda zan faɗi halin da na shiga na ɓacin rai ba za ku gane ba, nan take ya sire min a raina, na ce"In sha Allah zan yi musu biyayya, ba zan tozarta ba kuma albarkacin biyayyar da zan yi, kai guba ne a gare ni Saddam, ba zan taɓa yafe maka ba".

Na yi jifa da wayar na fashe da kuka mai sauti, wanda ya ankarar da Mama akwai matsala, don tana tsakar gida tana haÉ—a wutar da za ta dafawa Baba ruwan zafi, zai yi sammakon fita.

Ta shigo É—akin da sauri tana tambayata "Sayyada lafiya? Mene ne?"

Na kasa magana sai kuka, sai da ta fara zagina sannan na ce mata"Babu komai".

Ta ce"Kin ci gidanku, to hauka kika fara yi da za ki dinga wannan kukan kuma ki ce babu komai?"

Sai ga Baba ma ya zo yana tambayar me aka yi min.

Na ce"Wallahi babu komai, kawai dai na gane na yi kuskure, ku yafe min don Allah, Baba ba sai na fara fita na jira wani ya ce yana sona ba, ko wane ne ma indai ya yi maka ina son shi, a yi auren kawai fatana dai ku yafe min".

Baba ya ce"Sayyada na yafe miki, Allah Ya shirye ki, Ya shiga lamarinki, Ya tseratar da ke daga kaidin namiji, Allah Ya ba ki miji na gari".

Ya juya ya bar É—akin.

Mama kuma ta zauna ta saka ni a gaba da tambayar me ya saka ni kuka?

Na ce"Kawai tunani na yi Mama, ban kyauta muku ba, shi ne na saka a raina zan cire son Sadam daga zuciyata, shi ne kawai abin da ya saka ni kuka".

Mama ta ce"Sayyada na san kina son shi, na san rabuwa da abin da kake so akwai zafi, amma ki gane shi ba sonki yake yi ba, ke ce kike son shi, zai wahalar da ke, saboda kin ba shi kofofi da dama wanda zai taka ki yadda yake so idan ya aure ki, wannan tozarcin nake guje miki, ina so rayuwarki ta inganta ne, yanzu zan roƙi mahaifinki ya ƙara miki lokaci zuwa wata uku, ko Allah zai kawo wani wanda kike so, tun da kin ce wannan ɗin bai yi miki ba".

Na ce"Mama ai a yau na buɗe ƙofar zuciyata duka, zan karɓi duk wanda kuka zaɓa min in sha Allah, ko an ba ni lokaci babu wanda zan kawo a matsayin ina son shi, amma zan yi aure, saboda kuna so, kuma ibada ne, domin na gama so!".

Jikin Mama ya yi sanyi, ni kuma na share hawayena, a daidai wannan lokacin na saka a raina ba zan sake kuka saboda Sadam ba, ba ma shi kaɗai ba, babu wani namiji da zan bari ya ƙara saka ni kuka wai saboda ina son shi, na yi alƙawari da zuciyata zan rabu da shi har abada, don haka na tashi na bar Mama a zaune, na fita na kunna mata wutar, kafin azhar na warware na saki jiki sosai, amma idan ka yi min kallon nazari ba na fuskata ba za ka gane ƙarfin hali kawai nake yi, da son ɓoye jinyar dake cikin zuciyata, na cigaba da ƙarfafa kaina saboda na san ta hakan zan manta da shi har abada.

Da daddare Mama take cewa Baba tun da na amince ai sai a yi a wuce wajen, ya ce a'a, ya riga ya dakatar da shi, kuma wata uku ya ce masa, a bar ni na huta tukunna.

Bayan kwana uku sai Sadam ya kira ni, ban ɗauka ba, sai ma block dinsa da na yi ta ko'ina, kuma na goge lambarsa. Haka na fara gudanar da wata rayuwa mai cike da son ƙarfafawa kaina gwiwa, a hankali mu fara dawowa kamar da ni da Mama da ma sauran 'yan'uwa, na fara zuwa sabga, biki ko suna ko dubiya, idan na so sabunta iska ma haka kawai nake kai wa 'yan'uwa ziyara, amma sam ban da Anisa.

USTAZ

Sati biyu ya yi ya dawo, a jigace ya dawo, kawai son kasancewa da matarsa yake, ya yi takaicin rashin zamanta a gidan, haka ya yi wanka ya tafi gidansu da yamma, rarrashin duniyar nan ya yi mata tare da alƙawarin zai rage, amma sam ta ce ba ta yarda ba, ita ba za ta koma ba, Allah Ya taimake ta iyayenta ba masu tirsasawa yarinya ba ne, don haka suka tambayi Ustaz ya faɗa musu me ya haɗa su tsakanin shi da Allah, kunya duk ta kama shi, ya fara bayani"To Baba a gaskiya ba zan ɓoye maka ba, ina da wani laruri, bi ma'ana ni hariji ne, wannan shi ne, ita kuma Zulaihat ta kasa jurewa".

Babanta ya ce"Dama ya za a yi ta jure? Ai mu idan haka ne ka yaudare mu, tsakani da Allah ba ka kyauta mana ba, kana Malami kake irin wannan munafurci?"

Ustaz ya ce"A yi haƙuri Baba, in sha Allah zan gyara, zan rage lamarin, duk da dai halittar ce a haka, amma zan yi iya ƙoƙarina na rage".

Baban ya ce"A'a babu wannan maganar, ba zai yiwu ba, ni dai ba zan yi mata tilas ta koma ga halaka ba, Zulaiha tana da hakuri, tun da ta kasa jurewa to fa an kai maƙura ne, don haka tun da ta ce ba za ta koma ba ka sallame ta kawai".

Ustaz ya ce"Subhanallah, Baba saki fa ba abu ne mai sauƙi ba, shi ne halal ɗin da Allah ba ya so".

Baba ya ce"Tun da aka halatta ai ba haramun ba ne, kuma an yi shi ne don an san dama irin haka za ta faru, wanda saki ne zai zama maslaha, don haka ka sallame ta É—in kawai".

Ustaz ya duba ya ga kuÉ—in da ya kashe, ya tuna yadda ya dinga ba da kuÉ—i ana haÉ—a lefen nan, kuma a ce wai ya sake ta? Kwana uku ne fa kawai ya mori kuÉ—insa, ya ce"Kai, ina! Baba a ba ni lokaci zan yi shawara da tunani".

Suka rabu a kan haka, Baban yana jin ko auren kwana É—aya ne ya yarda ya mutu a ce mata bazawara da dai ta yi zamam auren da za ta cutu.

Ustaz ya koma gida jiki a mace, haka ya buɗe babin kewar mace a kusa da shi, sai ya fara azumi idan ya yi yau gobe ya huta, sannan da abun ya bijiro masa zai ɗauki Qur'ani ya fara karantawa, da daddare ne dai dole sai ya yi istimna'i yake iya bacci, abun yana damun shi sosai, sai da ya yi watanni biyu a haka, a wata na ukun suka nemi ya sake ta ko su yi ƙarar shi, haka ya sake ta ba don ran shi ya so ba, ya rasa yadda zai yi, yana buƙatar auren kuma shi zuwa yanzu ya fara karaya, yana tsoron sai ya gama kashe kuɗinsa ya sake auro gaibu, don haka zuciya ta ba shi shawarar kawai ya komawa Rauda su sasanta, ai dama don zai yi aure ne, yanzu kuwa tun da babu auren za ta yarda ta dawo.

Da wannan tunanin ya shirya ya je gidan su Rauda, tun a farfajiyar gidan zuciyarsa ta tsinke, sakamakon ganinta da ya yi tana zance da wani babban mutum, ya zauna cikin ɓacin rai sai da ta gama mutumin ya tafi sannan ya tsayar da ita, ya daure suka gaisa, ya ce"Rauda wannan wane ne?"

Ta ce"Tsohon saurayina ne, kuma wanda zan aura yanzu in sha Allah, a baya ya so ƙwarai ya aure ni, amma soyayyar ka ta rufe min ido, yanzu kuma idona ya buɗe".
Chapter 64 · 0% Book details