Sashe 29
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta ce"Sayyada Maraƙisiyya ta so zama da malam Ashir sosai, abun ne kawai ya fi ƙarfinta, ina nuna mata ba za ta iya ba su rabu kawai, ita tana nuna min ita ce ta gaza, ta sa na samo mata maganin sanyi da na tadawa mace sha'awa, tana ta sha babu sauƙi, sai ta nemi a samo wanda zai rage masa sha'awa, na tambayi wacce take siyar mana da magani ta ce akwai, ta siya, to a ranar na kai mata ina yi mata bayanin yadda maganin yake, an ce idan ta dafa masa shayi da shi, abun zai zama kamar lagwani har sai bayan sati biyu, nake ba ta shawarar idan ta yi ta huta na sati biyu, sai ta ƙyale shi ya tashi idan ya ɗana na kwana biyu sai ta ƙara kwantar da shi, wallahi tsautsayi Sayyada, ashe ya dawo gidan yana ƙofar ɗaki yana jinmu, sai ji muka yi ya fara Subhanallah da Innalillahi, ni dai kamar na nitse a wajen, da ƙyar na iya fitowa daga ɗakin, ai kuwa ya ce idan ya sake gani na a gidansa sai ya faɗawa mijina zan kashe masa aure, kuma yanzu ma sai ya haɗa ni da Allah, daga ranar ban sake shiga gidan ba, ita ma ba ta sake shigowa ba, ashe mutumin nan ƙwace wayarta ya yi, kuma yake kulle ta a gida".
Tsoro ya kama ni, don na hasko a ce ni ya yi wa haka, na ce"Kullewa kuma?"
Ta ce"Wallahi, ranar dai da ta gaji ta kira ni ta katanga take faɗa min, ta ce takarta yake kamar zai kashe ta na taimake ta, shi ne na je na sami wani na biya shi, aka yanke mukullin, na shiga na same ta a jigace, ni da kaina na haɗa mata kayanta na ce ta tafi gida, tsakani da Allah aure irin wannan akwai cutuwa, kowace ƙwarya da abokin burminta, kamata ya yi ya samu daidai shi, muna cikin haɗa kayan ya zo gidan, ita kuwa ta ce wallahi sai ta tafi gidansu, ya riƙe ta, ta dinga zagin shi, ni kuma ina faɗa masa gaskiya, na ce wallahi idan bai rabu da ita ba, ta kai shi ƙara Human right a bi mata hakkinta, ke na dai zaƙarlale sosai fa, da ƙyar dai ya ƙyale ta ta tafi, na raka ta har gida, a gidan ma ai ta daɗe kafin ya haƙura ya sake ta, tun daga lokacin na yi alƙawarin duk wacce zai auro ba zan shiga gidansa ba, su kuma sauran mutane abin da ya sa kika ga suna hana yaransu shiga, a gaskiya akwai ranar da maman Ihsan ta aiki ɗanta gidan, kin san yaro ba hankali, ya je ya shiga har ɗaki, ya same su turmi da raɓarya da ranar Allah, ya faɗawa abokansa, yara duk wanda ya je gida sai ya ba da labarin an je gidan Amarya an ganta ba kaya ita da mijinta, shi ne kowace uwa ta zaunar da nata ɗan ta yi masa kyakkyawan gargaɗi, shi yasa har yanzu babu me shiga".
Sayyada ta sauke ajiyar zuciya ta ce"Ikon Allah, ki ce dai ke kika taimaki Maraƙisiyya".
Ta ce"Uhm ai ni na yi mamaki ma da ya bar ki kike shigo min".
Na yi murmushi na ce"To ai wanann ya wuce".
Da son jin gulma ta ce"Kuma ke kina iya zama da shi ba ruwanki".
Na ce"Ina iya ƙoƙarina".
Muka taɓa fira na yi mata sallama na koma gida.
Na zauna na yi shiru, bayan jin labarin nan yaƙe kawai na yi wa maman Haneefa, tsakani da Allah na ji kunya na ji takaici, wallahi ba na burin tonawa mijina asiri na faɗawa duniya ga larurar shi, ashe ni kowa na unguwar tsirara yake kallona an riga an sani, sosai na ji baƙincin wai an taɓa ganin shi da matarsa, na rasa ina zan kai kunya da takaici, da a ce na san da wannan labarin da ba zan shiga gidan kowa ba a maƙotan, tun daga lokacin kuma na yanke ba zan shiga gidan kowa ba, gara na yi rayuwata ni kaɗai, don haka na gyara zaman kaɗaici.
Ina iya ƙoƙarina na ganin na jure jarabarsa, duk ina ina cutuwa, amma shi ba ya gani, a hankali na lura abun nashi gaba ma yake yi, yanzu bayan an yi kafin a kwanta, sai ya tashe ni tsakar dare an sake yi, sannan a yi sallah, wannan sallar ni dai na san wataran ba lada nake samu ba, saboda dole yake min, wataran na gaji bacci nake ji, ba a son raina nake yi ba, sannan da asuba ya a dawowa daga masallaci zai sake yi, to wataran bayan ya karya kafin ya tafi kasuwa sai ya sake kirana, sannan ya dawo da rana, da yamma ma idan ya dawo da wuri bai kai magriba ba sai ya yi ko kaɗan ne, Alhamis da Litinin ne kawai nake samun sassauci, lokaci ɗaya na firgice, duk na rame komai ya daina yi min daɗi, wataran sai na zauna na yi ta kuka, ga shi na kasa faɗawa kowa damuwata.
Ana cikin wannan ƙadamin ne kuma na samu ciki, wannan ma ba mai laulayi ba ne kamar na gidan Sadam, don da rashin zuwan period ɗina kawai na gane na same shi, don a wannan rayuwar zuwan period ɗina ba ƙaramin abun farinciki ba ne, ko yaya ne wajen nan yana hutawa na 'yan kwanaki, to na ga wata ya zo ya wuce ban yi ba, don haka na siyo tsinken gwaji na gwada, ya nuna ina fa ciki, farinciki ya kama ni, saboda ina masifar son haihuwa, wallahi sai da na ji ƙaunar Ustaz kaɗan a cikin raina, saboda ta wajensa na samu abin da nake nema, wanda Saddam ya tauye ni ya so ya saka ni a layin marasa rabon haihuwa.
To daga nan ne fa dabara ta faɗo min, na fara narkewa ina cewa ba ni da lafiya, sai yana nan sai na tsiri amai na ƙarya, ko na lulluɓa na dinga karkarwar ƙarya na ce zazzaɓi nake yi, har dai ya kai ni asibiti aka tabbatar da cikin jikina, da fari ya ba ni kulawa, ya yi haƙuri ya ajiye jarabarsa, sai dai idan ya kasa jurewa ya yi sau ɗaya da daddare, hakan ya sa na sake narkewa duk da ina ganin yadda duk ya rasa nutsuwarsa.
Shigowar yanayin sanyi ne ya sake zabura shi, ya daina tausayin rashin lafiyar ƙaryar da nake yi, aka koma gidan jiya, tsoro ya kama ni, tsakani da Allah lallaɓa cikin jikina nake yi, don gani nake fyaɗen ƙarshe da Saddam ya yi min a ranar da ya sake ni shi ne silar zubewar cikina, don haka dole na kare wannan duk da Allah ne me karewa, duk yadda nake nuna masa ya ɗaga ƙafa saboda wannan cikin kar ta samu matsala ya kasa fahimtata.
Yau ma bayan ya dawo daga masallaci ina bargo bacci tana gizgata ya shigo bargon, na yi saurin tashi na ce"Don Allah Malam ka tausaya min haka, gaskiya na gaji".
Ya ce"Subhanallah! Wai da ladan kika gaji? Assayyada zai iya faruwa a ce a ranar lahira, an gama hisabi, ana auna ladanki da zumubinki a sikeli, a ce saura kaɗan ladanki ya rinjayi zunubin, ki shiga aljanna, ayyukanki na alkhairi duka sun ƙare, wannan rana ce da ko mahaifanki ba za su iya ba ki kyautar lada ko guda ɗaya ba, saboda kowa ta kansa yake yi, wato bi ma'ana nafsi-nafsi, kina cikin wannan halin kwatsam sai ki ji an ce, ga ladanki nan na taimakon mijinki da kika yi kuka raya sunna, don Allah ya za ki ji? To shi yasa shi aikin lada fa ba a raina shi".
Hawaye kawai nake yi, zuciyata na zafi, na ce"Akwai hanyoyin samun lada da dama, in sha Allah zan shiga aljanna ko ba ta wannan fannin ba, kai malami ne, kana da sani, ka san aurena da kai akwai cutarwa a cikinsa, tun da dai halittarmu ba ɗaya ba, Allah Ya san da haka shiyasa da ya halicci maza masu irin halittarku, sai ya yo mata su ma masu irin halittar, don a samu daidaito da kuma adalci a tsakanin ma'aurata, don Allah don Annabi ka yi min adalci, ba na cikin mata masu yawan buƙatuwa, ina da rauni ta wannan fannin, ka taimaka ka yi min adalci". Na fashe da kuka.
Ya yi shiru kamar jikinsa ya yi sanyi, ya ce"To yanzu kenan ya kike so a yi? Watanninmu uku da ke Assayyada, ya ci a ce kin saba, ba san ba haka kike ba, amma ai sabawa ake yi".
Na ce"Tsakani da Allah idan shari'a ce aka kawo maka matsayinka na Malami wannan hukuncin za ka yanke?"
Ya ce"To me kike so na yi bayan wannan?"
Na runtse ido hawaye suka zubo ina auna maganar da zan faɗa, gabana yana faɗuwa na ce"Don Allah mu rabu kawai, tun da zaman aurenmu akwai cutuwa, ka sawaƙe mini".
Nan take ya fara"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! La ila ha illallah! Subhanallah".
Ya dinga girgiza kai kafin ya ce"Subhanallah! Kaiconki Ya Assayyada, yau kin aikata zunubi mai girma, wai ni kuwa kin yi islamiyya? Kin san hukuncin macen da ta nemi mijinta ya sake ta?"
Na sunkuyar da kai na ce"Amma ai ni da dalili, ka fi ƙarfina, shari'a ba ta ce a yi irin wannan zaman ba".