← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 89

Sashe 55

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Watarana yana falo yana yi, Rauda ta farka yin fitsari, ta ga ba ta gan shi ba, ta leƙa falo ta gan shi ya hau kan hannun kujera yana ta motsa jikinsa, gabanta ya faɗi, don idan ba ka kalle shi sosai ba sai ka ce da mace yake tare, yadda duk ya fita daga hayyacinsa, ta koma ɗakin, ta zauna a bakin gado, tausayin shi sai ya kama ta, ta fara tunanin anya Allah ba zai kamata da hakkin mijinta ba kuwa? Kuma ita ma fa tana jin kewar shi a wasu lukotan, amma inda a ce zai tsaya a iya romance, abin da ta yi kewa kenan ba wancen babban lamarin ba, ta koma ta kwanta jiki a mace, tana tunanin za ta faɗa masa su yi yarjejeniya idan zai dinga romance ɗin.

SAYYADA

A lissafina cikina watansa uku ya shiga na huɗu, amma na fara jin motsin shi kaɗan-kaɗan, ina nan ina ta lissafin watannin haihuwata, Mama har yanzu ba ta gama sakin jiki da ni ba, 'yar firar nan mun daina, Baba dai yana kula da ni sosai, zan iya cewa ba ni da damuwa sai ta zuciyata, soyayyar Sadam ce take ragargaza ta, wani lokacin idan na matsa kaina da tunanin shi fitar numfashina har canzawa yake, wani irin son shi nake ji wanda ban ji ba ko a farkon haɗuwarmu, ga shi ba ni da damar da zan bayyana masa, ina cikin idda, sannan ba a ba ni wayata ba har yanzu, kuma uwa-uba na san yana can yana fushi da ni, ƙila ma da gaske yake ya haƙura da soyayyata, idan na tuna yana can tare da matarsa sai baƙinciki ya turnuƙe ni, na matsu na fara zuwa awo ko Allah zai sa watarana mu haɗu idan ya kawo shaguɗaɗɗiyar matarsa, wancen satin na ce da Mama zan fara zuwa awo ta ce nmin ba yanzu ba, na lura sam ba ta son abin da zai saka na fita waje, kuma ban ga laifinta ba, tun da ni ce na saka mata zargina.

08028966015
[01/11, 8:22 pm] Sadiya Abdulrazak: 33

Ustaz ya kwantar da kai sosai a wajen Rauda, sam bai taɓa gwada nemanta ba, sanda ta zo masa da batun a dinga romance ya ce ba ya so saboda abun akwai sammatsi, zai iya kasa riƙe kan shi, tana jin tausayin shi, amma Zainab tana ƙara zuga ta kan illolin zama da hariji, a haka suka dinga zaman, sai dai yana yawan kunna wa'azin da ke nuni da hakkin miji a kan matarsa ko ya kunna wanda ake gargaɗin mata masu ƙauracewa miji, amma ba ya ma nuna don ita ya kunna. A ɓangaren kasuwanci kuma Alhamdulillah yanzu ya san makamar aikin, kuma mahaifin Rauda ya yi masa duk wasu gwaje-gwaje ya yarda yana da amana, sam ba ya cogen kuɗi, tun da ya sha gwada shi, ya yi kamar ya manta lissafin, amma sai Ustaz ya tuna masa s ji kuɗin daidai ko naira biyar bai rage ba, wannan abu ya farantawa mahaifin Rauda, don haka ya saka shi a babban shagon shi, ya ba shi matsayin babba a shagon, da kuma alƙawarin zai dinga aikensa ƙasashen waje ya dinga siyo kaya.

Alhamdulillah Ustaz harka ta buɗe, yana samun kuɗi, amma wannan mammaƙon na shi yana nan, sai Rauda ta ɓata rai sosai sannan yake yin cefanen arziƙi, kuma har yanzu yana nan a kan bakanshi ba ya cin nama, sai dai ya faki idonta ya sata ya ci.

A hankali Rauda ta fara jin hukuncin da ta yanke ya yi tsauri, da gaske kewar mijinta take yi, kuma tana jin kunyar faɗa masa, tun tana daurewa har dai wani dare ta neme shi, Ustaz kuwa ya ce da wa Allah Ya haɗa ni? Ya gwangwaje sosai, ta samu gamsuwa, duk da ta wahala, tun daga wannan ranar sai Rauda ta zama kamar ita ce mijin Ustaz matar, sai ranar da ta bushi iskanta sai ta neme shi, shi kuma babu zuciya sai ya amsa kira, yana jin zafin lamarin zaman nasu sosai, amma yana daurewa ne saboda alkhairin da ya samu ta silarta, kuma duk shirinsa shi ne sai ya gama kafuwa ya zama mai kuɗi sannan zai gallo mata kishiyoyi, don mata biyu yake burin ya aura a rana ɗaya, idan ta ga dama ta zauna sai su zama su uku, ya dinga rabon kwana kwana ɗaiɗai, duk tsiya dai duk ragwantarsu ai idan suna hutun kwana biyu ba za su dinga yi masa raki ba, da wannan tunanin yake haƙuri da tsarin Rauda.

To sai ga shi ma a hankali ita ma Rauda ta zama 'yar gari, tun da yanzu neman nashi fashin kwana ɗaiɗai take yi, idan ta neme shi yau gobe sai ta huta, ana haka ne kuma ta samu ciki, da fari ta yi laulayi, amma yana yin wata huɗu ta daina laulayi, sai kuma take jin yawan sha'awa, don haka kusan kullum yanzu sai ta nemi Ustaz, shi kuwa farinciki kamar ya kashe shi, har wata 'yar ƙiba ya fara yi.

SAYYADA

Duk yadda Mama ba ta so na fita dole sai da na fitan da lokaci ya yi, cikina yana cika wata biyar Baba ya ce ya kamata na fara zuwa awo, na ce to, ranar Alhamis ne aka yi maganar, ai kuwa har zumuɗin zuwan ranar Litinin nake, fatana ɗaya idan na je asibitin na haɗu da Sadam ko a hanya ne, na faɗa masa ba yaudarar shi na yi ba, a ƙalla ya daina fushi da ni ko da zai daina sona, duk yadda zan yi na ga na cire son shi daga zuciyata na kasa. Ranar Lahadi da daddare muna zaune Baba yana cin abinci yake ce min"Gobe da wuri za ki tafi asibitin? Kuma nawa ne zai ishe ki?"

Na ce"E da wuri ake zuwa, kuÉ—in kuma ka bar shi ina da kuÉ—i".

Ya ce"Kika samu a ina?"

Na ce"Dama tuna account É—ina tun ina gidan Sadam".

Ya ce"Ok, amma duk da haka zan ba ki ɗin, hakkin mijinki ne ya ba ki, ni kuma na ɗauki alƙawarin idan ba abun ya gagare ni ba ne ba zan tambaye shi ba, musamman ma da ni ne na dakatar da shi, don haka ki adana kuɗinki, ga nawa ki yi amfani da shi".

Ya yi maganar yana miƙo min kuɗi, na karɓa na ce"An gode Baba Allah Ya ƙara arziƙi".

Mama ta ce"Goben tare za mu je ma ai".

Baba ya ce"A kan me? Sayyadar ƙaramar yarinya ce da sai kin raka ta wajen awo?"

Mama ta ce"Shikenan".

Ya ce"Ko akwai wani dalilin da yasa kike son rakiyar?"

Ta ce"Babu komai, shikanan Allah Ya kai ta lafiya".

Na tashi sum-sum na bar wajen, na san dai Mama zargina take shiyasa har ba ta yarda na tafi asibiti ni kaɗai ba, jikiwnsa duk ya yi sanyi, na ƙirga kuɗin dubu goma ne, na adana na nemi waje na zauna, Baba yana fita daga gidan Mama ta shigo ɗakina, sai da gabana ya faɗi da ganinta, tun da na san ba ni da cikakkiyar gaskiya, ta zauna ta ce"Sayyada".

Na ce"Na'am".

Ta ce"A zahiri za ki fara zuwa awo ke kaɗai, amma a baɗini ba ke kaɗai ba ce za ki fara zuwa, akwai Allah, yana kallonki yana jinki, dokarsa kike burin takawa, ki sani idan kin cigaba da soyayya da wanda kika so da aurenki to dokar Allah kike takawa ba tawa ba, kuma za ki iske shi a madakata ki karɓi hukuncinki, ki ji tsoron Allah Sayyada, ko me za ki yi ki haƙura ki kallama iddarki, kuma kar ki manta na rantse ke da auren Saddam sai dai a lahira, idan kika sake kula shi kuma Allah Ya isa ban yafe miki ba".

Hawaye ya zubo min na kasa cewa komai har ta ban É—akin, wannan kalmar ta cewar ni da Sadam har abada tana firgita ni, ji nake kamar suna cewa na yi sallama da farinciki ne a rayuwata, don shi ne farincikina, haka na kwana da tunani barkatai.

Washegari da sassafe na tashi na shirya, na sha kunun da Mama ta dama na tafi awo, tun da na fita daga gida nake jin daɗi saboda na sabunta iskar da nake shaƙa, ina ta takawa a cikin layi har bakin titi, riga da zani na saka na atamfa da hijjabina har ƙasa, yau ban saka niƙabi ba, na tari adaidaitasahu na hau muka kama hanyar asibitin, a raina ina fatan na ga Saddam, amma idan na tuna Allah Ya isa da Mama ta yi min sai jikina ta yi sanyi, na ji ko na gan shi ba zan iya yi masa magana ba, haka na shiga asibitin ina ta kalle-kalle, karaf idona ya sauka a kan motar shi, na ƙare mata kallo tabbas ita ce, nan take bugun zuciyata ya canza, na daburce na rasa ma me ya kamata na yi, wata zuciyar tana faɗa min na je na fahimtar da shi yadda abun ya kasance a ranar da ya ban maganin nan, wata zuciyar tana faɗa min shi ma fa bai damu da ni ba, ya daina so na, ga kuma kalaman Mama na maimaita kansu a cikin kaina kamar yanzu take furtawa, amma haka Shaidan ya yi min linzami ya tallafi ƙafafuna na fara takawa a hankali har na isa wajen motar, akwai tint a gilashin don haka ba zai yiwu na ga na cikin motar ba, jikina ya fara ba ni yana ciki yana kallona, don haka na ƙwanƙwasa, shiru ba a buɗe ba, na ɗan yi kamar minti biyu a tsaye, na shagwaɓe fuska wai ko zan ja hankalinsa ya buɗe amma shiru, har na gaji na bar wajen ina waiwayen motar.
Chapter 55 · 0% Book details