← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 89

Sashe 6

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan take Baba ya haÉ—e rai kamar hadari, ya ce"Ba na son jin komai da ya shafi zaman auren Sayyada da yaron nan, don haka tashi maza ki koma É—akinki".

Mama ta ce"Amma Malam ba ta taɓa kawo ƙararsa ba, ya kamata a tsaya a saurare ta a ji da me ta zo".

Ya ce"Ko da me ta zo ba mu da maganinsa, na dai shi ta zaɓa ba? To ta je ta rayu da shi, ko kashe ta ya yi sai dai na ce Allah Ya ji ƙanta, ba dai na ɗaga kai na yi masa kallon banza ba".

Na fashe da kuka na ce"Baba don Allah ka yi haƙuri ka yafe min, wallahi na gaji da auren nan, kuma na yi nadama".

Ya ce"Nadamarki ta zo a makare, kar ma ki sake ki furta abin da ya yi miki, ni sai dai ma na ce ya yi min daidai, kuma daga yau kar na sake jin wata matsala ta kawo ki gidan nan, tun daga ranar da na ba shi ke na faÉ—a muku kyauta ce ta har abada idan ya ga dama ya kwaÉ—a ki ya cinye, ko sakinki ya yi dama kar ki tunkaro gidana, tashi ki koma!" Ya karasa da daka min tsawa.

Na kalli Mama sai na ga ta kau da kai daga kallona, haka na fita ina gursheƙen kuka, ina tafe a hanya ina kuka kamar mara galihu ko wata ƙaramar yarinya, ba na ma kallon gabana kawai jefa ƙafata nake yi, a raina ina tambayar shin wace irin zuciya ce da babana? Allah mamallakin kowa da komai ma muna yi masa laifi ya yafe mana, shi Baba me yasa ba zai yafe min ba? Horn ɗin mota na dinga ji babu ƙaƙautawa ta bayana, don haka na waiwaya don na ga ta ina na tarewa mai motar hanya, sai na ga motar Sadam ce, na juya na cigaba da tafiya, ya fito daga motar da sauri ya sha gabana ya ce"Ki zo ki shige mu tafi, ai dama kin san ba ki da wani sauran matsuguni a gidanku, ina fata dai haukanki bai yi tsananin da har kika faɗa musu abin da ya faru ba".

Ina kuka na ce"Abin da ya faru wanne daga ciki? To wanda kake gudun shi na faɗa musu, na faɗa musu kai mazinaci ne, fasiƙi".

Ya É—age kafaÉ—a ya ce"Fine! Ai dama sun san ni da ke mazinata ne tun tuni, don ba a mazinaci sai da mazinaciya".

Na ji maganar kamar saukar aradu a kaina, kafin na nemi amsar ba shi, ya fizgi hannuna mai lafiyar ya ja ni zuwa wajen mota, ya buɗe ta ya tura ni, idan ma bai tura ni ba shigar zan yi wallahi, don yanzu na fahimci da gaske gidan nashi da nake ganin shi ne damuwata zaman cikinsa ya zame mini dole, sai ranar da baƙinciki ya yi ajalina zan bar shi, ya shiga motar ya ja muka tafi, na kifa kaina a cinyata ina ta rera kuka, bai yi min magana ba har muka ƙarasa gidan.

08028966015
[24/09, 5:27 pm] Sadiya Abdulrazak: Shi ya buɗe min motar na fito, ya kama hannuna kamar gaske muka shiga falon, ya zaunar da ni a kujera, shi ma ya zauna yana riƙe da hannuna ya ce"Sayyada, Allah Ya sa dai ba ki faɗi abin da kike zargi a gidanku ba, wallahi dariya ma za a yi miki".

Na ce"Au zargi ma nake yi kenan? Har yanzu kana da ƙwarin gwiwar da za ka kare kanka duk da shaidun da na gani da idona? Sadam wace ce ta zo ta kwana a gidan nan? Idan za ka yi zinarka ba za ka yi a waje ba sai ka ci mutuncina ka zo har cikin gida a gadona?"

Nan take yanayin fuskarsa ya juye daga na damuwa zuwa ɓacin rai, ya ce"Ke Sayyada kar ki sake danganta ni da zina, idan kuma zargina kike yi to ki fara saka minjaye, e ina nufin ni ma ina zarginki".

Gabana ya faÉ—i na kalle shi hawaye yana sakko min na ce"Me na yi na zargi? Sai ka faÉ—i hujjarka".

Sai ya yi tsaki ya ce"Kin ga ni ba na son tashin hankali, mu bar zancen haka, tabbas na kawo wata ta yi girki, amma wallahi babu abin da ya shiga tsakanina da ita, ni ba mazinaci ba ne Sayyada, wallahi ke kaÉ—ai na sani a 'ya mace".

Na girgiza kai na ce"FaÉ—i wata maganar dai, don har abada ba za ka samo kalaman da za su wanke ka ba, tun da ba zargi nake yi ba na tabbatar".

Ya ce"Kin tabbatar? Shaidar zina ba fa ba ƙarama ba ce Sayyada, kin taɓa kama ni turmi da taɓarya? Kuma kin kira shaidu sun shaida? To wallahi ki iya bakinki, ki kiyaye ni".

Na tashi zan tafi ya janyo ni na dawo, sai na zauna É—in na kifa kaina a kujera, ba kuka nake ba, kawai dai na rasa ma yadda zan yi, shiru na sakanni kafin ya sanyaya murya ya ce"Sayyada".

Ban amsa, ya fara faɗin"Duk iya ƙoƙarin da zan yi don na ga mun zauna lafiya ba tare da shiga hakkinki ba ina yi, ina ta gudun cutar da ke amma ke kamar ba kya gani, idan kina wani abun sai na ga kamar kin manta wane ne ni a wajenki, kamar kin manta ramukan da kika tsallake kafin burinki ya cika ki same ni, a zatona ko ni ne na sake ki don raɗin kaina ba za ki iya cigaba da rayuwa ba, amma yau wai ke ce kike cewa na sake ki, to ba zan sake ki, don haka ki kalle Ni mu tattaunawa kowa ya gyara halinsa, ina so zamanmu ya dawo kamar na baya, ba na jin daɗin ganinki a damuwa".

Na yi shiru ina ta hawaye, ya É—ago ni yana cewa"Ki yi magana don Allah, kin ji?"

Na ce"Sadam, za ka iya fasa wannan auren da kake shirin yi?"

Ya ce"Wallahi ba zan iya fasawa, ai na faÉ—a miki umarnin mahaifiyata ne, kuma ba na haÉ—a umarninta da na kowa a duniyar nan, ba zan iya bijire mata ba".

Na ce"Duk da na san Momy ba sona take ba, amma a wannan karon ba don ta ƙuntata min ta sa ka aure ba, don ka samu haihuwa ne, kuma yanzu tun da an cire tsinken ai zan haihu, me zai hana ka ce mata ta ɗan ƙara maka lokaci? Idan na samu cikin sai ka ce mata kawai ka fasa, ai ba za ta ƙi ba, tun da haihuwar da take fata za a samu".

Ya ce"Ita kuma ya zan yi na wanke ta daga ganin baƙinta da za a yi? Ina nufin su gidan su yarinyar da za a aura min ɗin, kin ga za su mayar da ita ƙaramar mace idan ta dawo ta ce an fasa, sannan auren nan saura watanni biyu, kina da tabbacin za ki samu a cikin wata biyun?"

Na ce"Idan na samu a cikin wata biyun za ka san yadda za ka yi a fasa auren?"

Ya ce"Ban yi alƙawari ba".

Na ce"To tun da hakane babu amfanin na tsaya ina tattaunawa da kai, aure dai sai ka yi ko? Ka je ka yi, amma ka sani daga ranar da ka auri wata ba zan sake amsa sunan matarka ba".

Sai ya yi dariya ya ce"Za ki saki kanki ne ko kuma kotu za ki je ta raba mu?"

Na ce"Ko da ina nan da aurenka ba za ka sake haÉ—a jiki da ni ba, na bar mata kai har abada".

Ya ce"To shikenan, hakan ma ya yi indai za ki samu nutsuwa".

Na tashi zan shiga É—aki ya ce"Anjima kaÉ—an likita zai zo ya duba ki".

Na gyaɗa kai, still ya sake riƙo hannuna, ya ce"Don Allah ki daina zargina, ban kwana da wata mace ba, amma wacce zan aura ta zo ta yi girki, kuma ita ce kika ga fitarta daga gidan ɗazu, Allah ne shaidata, ke ma kuma ki yi min adalci, tun da tare kuka kwana a asibiti da ita, yanzu ma ta dawo ne don ta yi miki abun karyawa, don Allah ki sassautawa zuciyarki".

Takaicinsa ya linku a zuciyata, inda ya san zafin da zan ji da ya gwammace ya ɓoye min gaskiya, don wallahi a yadda nake da kishi har gara a ce wata karuwa can ya ɗakko haya a titi ta zo suka kwana a gidan, da a ce wacce zai aura ce ta zo ta yi mini girki a kitchen har ma ta zo ta taya ni kwana a asibiti, to idan da na san ita ce sanda na farka tana baccin nan da ban shaƙe shegiya ba na wuce lahira?

A tsayen da nake na rushe da kuka ina maimaita idan ka cuce ni Allah Ya saka min, Allah Ya bi mini hakkina".

Ya yi tsaki ya shige ɗakinsa, ni ma nawa ɗakin na koma na zauna ina fashewa da sabon kuka. A hankali kuma na taƙaita kukan, kafin ma ya ɗauke cak kamar an yi ruwa an ɗauke, ƙwaƙwalwata ta shiga tariyo mini shuɗaɗɗun lokuta masu daɗi a wajena da akasinsu.

A asibiti muka haɗu da shi, lokacin Mama ba ta da lafiya an ba ta gado, shi kuma ranar ya je duba jikin abokinsa, Allah Ya ƙaddara haɗuwarmu, da fari ya fara ne da kallona yana faɗin na yi masa kama da wata Zainab a Kaduna, na faɗa masa ni ba ni da wata 'yar'uwa mai suna haka a Kaduna, ya dage ya ce dole 'yar'uwa ta ce tun da kamarmu ta ɓaci, har dai Anisa ta shiga zancen ta ce to ya nuna mana hoton Zainab, ya ce ba shi da hoton amma na ba shi lambata idan ya sa ta turo masa zai tura min, wannan ne silar haɗuwarmu da kuma faruwar komai, hoton Zainab kuma har yau bai nuna mini ba, ƙarshe dai ma ya sanar da ni babu ita, kawai yana neman link ɗin da zai jona alaƙarmu ne.
Chapter 6 · 0% Book details