Sashe 77
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na ci kuka a ranar, na shiga damuwa fiye da wacce na ji a gidan Isma'il, sai na ji dama ban dawo gidan ba, tun da ga shi na shiga halin rana zafi inuwa ƙuna. Sosai nake son ganin mijina da don ya kula ni mu sasanta, don haka da yamma na yi masa massage na faɗa masa ba ni da lafiya, Daddy yana buƙatar madara saboda ba ni ma da ƙarfin shayar da shi, Abiy yana ta kuka sai an kai shi wajen shi, kuma ina sha'awar cin wannan balangun da yake siyowa, na kasa cin abinci shi kaɗai zan iya ci.
Shiru bai dawo min da amsa ba, har na cire rai zai zo, sai ga shi ana idar da sallar isha'i ya zo, ya shigo har cikin gida, murna ta kama ni, suka gaisa da Mama ta ce masa ya shiga ina cikin ɗakina, ya shigo yana riƙe da Abiy, ya zauna a sallayar da na shimfiɗa, na ce"Sannu da zuwa, da ka zo katifar ai".
Bai kula ni ba, kuma bai dawo É—in ba, yana ta yi wa Abiy fira.
Na dinga kallon shi, ya ƙi ko kallonsa, sai yanzu nake jin son shi yana taso min wallahi, na kalle shi sosai ya ba gane kyakkyawa ne, irin kyaun nan nutsattse wanda ba a ganewa a kallon farko, na dinga tuna tarin alkhairansa a gare ni, na ce"Ina wuni?"
Bai kalle ni ba, yana kallon hannun Abiy ya ce"Lafiya lau, ya jikin?"
Na ce"Babu sauƙi".
Ya ce"To Allah Ya kawo sauƙin".
Na ce"Allah Ya kawo sauƙi kai ne za ka tabbatar mini da shi, don Allah ka yi haƙuri mu tattauna".
Yana kallon Abiy yake cewa"Dauda babarka ta ce kana ta kuka wai kana son ganina, an yi haka ko sharri ta yi maka?"
Na ce"Idan ma sharrin ne ka ga laifina?"
Ya ce"Miƙo min ɗana, tun da sai na roƙa".
Na miƙa masa shi, ya karɓa, ya miƙa min leda ya ce"Ga saƙonki nan".
Na shagwaɓe na ce"Ni fa ba shi nake so".
Ya ce"Amma ai shi kika ce min".
Na ce"Kai nake son gani, don Allah ka saurare ni".
Ya ajiye É—an, ya ce"To idan babu wani abun ni zan wuce".
Na fara hawaye na ce"Don Allah ka yi haƙuri".
Zai fita na riƙo shi, na rungume shi ta baya gam, muka tsaya a haka tsayin wasu mintuna, ya ce"Idan kin gama sai ki sake ni na tafi, na yi kuskure da na yi tunanin za ki so ni Sayyada, da na san haka soyayyarku ta kasance da Sadam da ban shiga tsakaninku ba, sai dai ina godewa Allah da Ya kau da hankalinki ba ki caka min wuƙa a cinya ba har kika dawo gida".
Jikina ya yi sanyi ƙalau, har na sake shi ban shirya ba, na kasa cewa uffan, har ya fice daga gidan, ina ji yana yiwa Mama sallama na kasa ƙwaƙwaran motsi, da ƙyar na ja ƙafafu na koma na zauna, na fashe da kuka, ina tunanin sai yaushe ne tabon laifin nan nawa zai ɓace a idon jama'a, ko shi da na cakawa wuƙar ya yafe min, amma mutane 'yan ba ni na iya sun kasa yafe min, idan har a baya lokacin da ya aure ni bai san rayuwar da na yi da Sadam ba sai yanzu ya sani to na yi masa uzuri, gaskiya dole ya yi fushi da ni, yanzu na gane ashe babu wanda zai ji abin da na aikata ya aure ni ya riƙe ni da zuciya ɗaya, sai irinsu Ustaz wanda su kuma za su zauna da ni ne saboda biyan buƙatarsu.
Kunya ta saka ban sake neman shi ba, ban sake yi masa massage ba, shi ma kuma bai sake zuwa ba har aka yi sati ɗaya, cikin kyautar kuɗin da yake yi mini na turawa ƙanwata Khadija dubu ɗari da hamsin ta siyo min ingantattun magunguna na gyaran jiki da maganin sanyi, ba duƙufa amfani da su kamar an ce min zai zo ya ɗauke ni a cikin satin.
Mama ta fara maganar zan koma ɗakina tun da ba wankan ne ban iya ba ai, nan fa hankalina ya tashi, saboda gaskiya ba na son komawa ba tare da mun gama sasantawa ba, don zaman zai yi min ƙunci a ce kishiya tana kallo ba ma jituwa da miji. Don haka na kira shi bai ɗauka ba, na yi masa massage na roƙi ya zo ba ni da lafiya, sai ya dawo min da tambayar "Mene ne maganin rashin lafiyar ki a tare da ni wanda yasa kike son ganina don ba ki da lafiya? Ko kuma kuɗin ganin likita ne babu na turo miki?"
Na mayar masa da amsa na ce"Komai na jikinka maganina ne, kuma ai ka sani rashinka ne ya kawo cutar".
Bai dawo da amsa ba, amma da daddare sai ga shi ya zo.
Yana shigowa na ce"Sannunku da zuwa ranku ya daÉ—e, ya hanya?"
Bai amsa ba ya zauna, na É—akko ruwa a É—akin Mama na dawo na ajiye masa na ce"Ga ruwa ku sha".
Bai sha ba, bai yi magana ba, sai dai ya ƙarasa yana kallon ɗan shi dake bacci a cikin net, na ce"A ɗakko muku shi?"
Ya ce"Rabu da shi kar a tashe shi".
Na yi raurau da ido na ce"Mai martabaz tuna nake ranka ya daɗe, kaina bisa wuya, don Allah a gafarce ni ba don halina ba, a sakaya ni a unguwar adalci ku irin na sarakai masu adalci ga matayensu, ku yi haƙuri ki yafe ni, Allah Ya huci zuciyarku ranku ya daɗe".
Ya ce"Amm... Sayyada mun shaida yau kin yi mana biyayya, kuma kin miƙa wuya ba tare da shaƙiyanci ba, to sai dai kuma kin makara domin a halin yanzu ba ma buƙatar jam'u daga gare ki, na matarmu ma kaɗai ya isa, zai fi ki zauna a matsayarki na cewar ni ba sarki ba ne".
Na fara hawaye da gaske babu wasa, saboda neman duk wata hanya nake yi da za mu sasanta na ce"Tuba nake ranku ya daÉ—e, a baya shaÉ—ain ya yi tasiri, na yi rashin kunya, ina neman gafara, a gafarce ni ranku ya daÉ—e sarki mai mulkin gidansa, mai Hajiya Halima uwar kissa, mai matar so Sayyada, an gaishe da uban Dauda da Daddy, da yardar Allah sai ka ga 'ya'yanka dozin da jikoki babu adadi, tuba nake,a dubi rafkananniyar zuciyata ba za ta iya É—aukar fushin Saraki ba, wane mutum inji mutuwa".
Duk yadda ya ɓata rai ya so daurewa sai da murmushi ya kufce masa, amma ya maze kamar bai yi ba, ya tashi yana cewa"Ki shirya gobe ƙarfe goma na safe zan zo mu je wani waje".
Zuciyata kawai ta raya min gida zai mayar da ni, don haka na ce"Ina godiya, godiya nake ranku ya daɗe, Allah Ya ƙara girma".
Na raka shi har ƙofar gida ina ƙara yi masa kirari kamar maroƙiya, na kwana da zulumin goben idan mun koma magana ta mutu ne ko da saura? Ban yi bacci ba sai da na haɗa mana kayanmu tsaf.
Shi kuwa da ya koma gida sai ya tsinci kansa da kewar Sayyada fiye da ta kullum, don haka yau a sashenta ma ya kwana, duk yadda Hajiya ta yi da shi ya ƙi yarda, ya ce ta rabu da shi a can ɗin, bayan ya gama komai ya kwanta ya kunna recording ɗin firar su da ita, yana ta murmushi, musamman da ya tuna yadda take yin abin bil hakki ba da shaƙiyancin da ta saba yi masa ba, wani furucinta ya tuna, wanda take cewa 'A ranar da na yi maka jam'u na ce maka mai martaba ba da tsokana ko nunawa matarka iyakarta ba, to ka saka a ranka na yi nutso cikin kogin sonka ne, ba sai na la jira na furta ina sonka ba'.
Murmushinsa ya ƙara faɗaɗa ya furta"Ina son matata Sayyada".
Ya nemo wata lamba ya yi kira, suka gaisa, ya ce"D.S.P akwai wani yaro da nake son ya kwana a hannunku yau gobe ina da meeting da shi, zan turo maka address É—insa yanzu don Allah".
Daga can ɓanagren aka ce"Ka ƙaddara kamar an gama indai yana cikin Nigeria".
Ya ce"Godiya nake yallaɓai".
Ya tura masa address ɗin, har ya fara bacci ya kira shi ya faɗa masa ya shiga hannu, sannu ya kunna data akwai saƙo, ya kunna data, sai kuwa ya ci karo da vedio, Saddam ne zaune da kwalbar giya yana ta maye da surutai marasa kan gado, a haka suka tarar da shi suka ɗauke shi, Isma'il ya runtse ido, bai taɓa jin tsanar wani a duniya kamar yadda ya tsaki Saddam ba, kishi yake yi da shi mai tsanani, ya turawa Sayyada vedion tare da gajeren rubutu ya ce"Yanzu wannan ne ya saka kika ƙi sona ko?"
Sai da asuba na ga saƙon, domin fa wuri na yi bacci, na cika da mamakin inda ya samu vedion, amma ban yi mamakin ganin Saddam cikin maye ba, saboda dama a yadda ya tare mu ni da Mama na zargi ya fara zuƙe-zuƙe.
Ƙarfe goma da mintuna ya zo gidan, na faɗawa Mama dama ya ce zai zo mu je wani waje, ta ce"To a dawo lafiya".
Ya ce"Sayyada Dauda ya zauna a gida, ba daÉ—ewa za mu yi ba".
Na ce"Au wai ba gida za mu koma ba?"
Ya ce"Ban sani ba".
Na ce"A huce ranki ya daÉ—e".
Na koma na lallaɓa Abiy ya zauna, sai kuma na shiga tunanin ko kewata ya yi yake so mu ɓarje amarci shiyasa? Wani zumuɗi ya kama ni, domin ni ma na yi kewar tashi ba kaɗan ba kuma na riga na samu tsarki.
08028966015
[16/11, 10:21 am] Sadiya Abdulrazak: 46
Shiru a motar bai kula ni ba, na gyara zama na ce"Sultan".
Ya ce"Wane kuma Sultan?"
Na ce "Sabon sunanka ne, ai na faɗa maka ba zan bi abin da matarka ta ƙirƙira ba, sai dai na samu nawa da ban".
Ya ce"Indai ba za ki ce min mai martaba ba to ki bar shi, ni shi nake so".
Da yake zaman lafiya nake nema sai na ce"To an gama ranka ya daÉ—e".
Ya wani taɓe baki ya ce"Kirarin ya fi daɗi a bakin matata".