Sashe 27
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya ce"Ba ga shi kina neman ja da ni ba, tun jiya nake jera doka kina bi ta kai kina tattakewa, tun da na ce ga yadda lamarin gidan zai kasance ai ke na ki kawai sam'u wa ɗa'a, wannan abubuwan da kike yi ba halin macen ƙwarai ba ne, don Allah ki gyara tun yanzu".
Na ce"In sha Allah!"
Ya raba shayin gida biyu, ya ɗauki fulas ɗin ya ƙara zubawa, zai zuba a ɗayan na ɗauka na ce"Ni ka bar min a haka, ko kurɓa uku ne gara na yi a kan na sha babu zaƙi".
Ya ce"La ba'asa, amma dai Assayyada ya kamata ki rage buri, rayuwar duniyar nan ba komai ba ce".
A tare muka fara cin indomin, sai da ta rage saura cokali biyu ya tashi ya bar min yana hamdala, ya ce"Ma sha Allah! Idan har kana bin ƙa'idar cik abinci za a same ka lafiyayye ta kowane fanni, don haka yana da kyau a rage ci, ba shi da wani amfani".
Na ce"Me za a dafa da rana?"
Ya ce"Ai akwai kayan miya ko?"
Na ce"E".
Ya ce"To ina ga ki dafa shinkafa, duk yadda kika yi ko jollof ko da miya".
Na ce"To a dawo lafiya".
Har ya tafi ya dawo ya ce"Aff, ba mu yanke adadin dafawar ba, ai ina ga gwangwani uku za ta ishe mu daga rana zuwa dare ko".
Na yi jim, kafin na ce"Anya kuwa?"
Ya ce"Za ta isa mana, haba Assayyada, na fa yi zaman auren nan, kuma waccen matar haka take dafawa, Alhamdulillah tana isa a ci, na faÉ—a miki fa ki koyi raba cikinki gida uku, a sha ruwa a bar kuma iska, gobe Litinin ma ai ranar azumi ce".
Na ce"Amma fa zan yi baƙi yau ɗin, kuma ban san su nawa ba ne".
Ya ce"E to, wannan yana da kyau ka tarbi baƙinka, sai ki dafa musu taliya ko macaroni leda ɗaya, kin ga sai ta fi daɗin lissafi, mu shinkafar su taliya ko macaroni".
Na ce"To, a dawo lafiya".
Ya ce"Allah Ya sa".
Na shiga gyaran gidan, na gama na yi wanka na kwanta, na shiga tunanin wannan mijin nawa yana so na ko kuma kawai ya aure ni ne don ya dinga samun wajen sauke buƙatarsa? Ni dai har yanzu ban ji ya zaunar da ni ya ce ya fara sona ba, ko ya tambaye ni ina son shi ko akasin haka, amma dai zan zuba masa ido na ga gudun ruwansa, ni dai har yanzu ba na son shi, kuma ba na jin zan so shi wallahi, sannan idan na yi iya dauriyata na gaji dole mu zauna da shi a kan wannan larurar tashi, ko ya koyi zuge tazugensa, ko kuma ya sake ni ya nemi daidai da shi, domin shi ba sa'an aurena ba ne. Wata zuciyar ta ce min anya Baba zai yarda ya karɓi uzurinki? Na ƙarfafi kaina da faɗin zai yarda in sha Allah.
Tun jiya babu wuta, wayata ta kusa mutuwa babu caji, ga shi ina son yi chatting ko kallo don ɗebe kewa babu dama, kewar gidan Sadam ta kama ni, ta dinga nuƙurƙusata, a can idan cajina ya kare to ni na so, muna da sola babba, ga kuma generator, na fara tunanin anya ban yi kuskure ba kuwa? Me ma Sadam yake yi min da ya sa na kasa yafe masa? Zuciya ta shiga tunasar da ni shi ne wanda ya lalata miki rayuwa, ya sa mahaifinki yake fushi da ke, ya ɓata miki suna a gari har kika kasa auruwa, sannan ya tauye ki ya hana ki haihuwa, a ƙarshe ya karya alƙawarin da ya yi miki na cewar ba zai yi miki kishiya ba, nan take na ji ina kan daidai, Sadam mugu ne ya cuce ni, don haka babu sauran amfanin zama da shi.
Haka na yi ta saƙa da warwara kafin bacci ya ɗauke ni, wajen sha ɗaya na tashi da yunwa, kamar ban karya ba, tsakani da Allah ji na yi ba zan iya jiran dahuwar shinkafa ba, don haka na dafa indomi guda na cinye na sha ruwa, sannan na ɗora ruwan shinkafar, tsakani da Allah ba zan dafa gwangwani uku ba, huɗu na saka, tun da shinkafar za ta kai kwano biyu ya siyo, ba lallai ya gane ba, na ɗumama miyar jiya. Wajen ƙarfe ɗaya ta dawo, na yi masa sannu da zuwa, ya amsa yana murmushi, ya ce"Sannu da gida Assayyada, ya ƙoƙari ya zaman kaɗaici?"
Na ce"Alhamdulillah, ya kasuwa?"
Ya ce"Mun gode Allah".
Na ce"A kawo maka abincin?"
Ya ce"Kafin abincin dai da an yi yaƙin nan, samun lada ai ya fi abinci ko?" Ya yi maganar yana bi na da kallon da ko bai faɗa ba na san me yake nufi.
Na ɓata rai na ce"Don Allah ka yi haƙuri, wallahi na fara gajiya".
Ya ce"Subhanallah!" Yana girgiza kai kamar abun tausayi ya ce"Da ladan kika gaji? To a gaskiya ko da a ce kin gaji da gasken, gajiya ba hujja ba ce, aure ibada ce, wannan wannan lamarin shi ne auren, daure ki dinga ba ni hakkina a duk sanda na nema, hakan ne zai tseratar da ke daga siraÉ—in tsinuwar mala'iku".
Ya janyo hannuna yana cewa"Daure kin ji, nan gaba kaÉ—an za ki saba, gobe ma kin ga iya na dare ne, sai kuma na gabannin asuba, tun da da rana muna azumi".
Kamar zan yi kuka, haka na miƙa kai zuciyata cike da fargaba, da gaske na gaji, kuma wallahi na fara hasashen zan ma iya buɗewa na zama kamar ƙofar gari matuƙar na cigaba da zama da wannan mutumin.
Muna cikin cin abinci yake cewa"Assayyada sai fa kin dage, domin zama da mai irin larurata da fari akan ɗan sha wuya, amma yana da daɗi idan ka saba, kin ga dai ita waccen matar cewa ta yi ba za ta iya ba, duk yadda nake sonta ƙarshe haka ta fita fit daga raina wallahi, to duk macen da ba za ta taimake ka ba ina ranar zama da ita?"
Na ce"Kenan ni ma nan gaba idan na gajiya zan fita daga ranka?"
Ya yi murmushi ya ce"Ban ce ba, amma dai ki sani ba ni agajin gaggawa a duk sanda na nema shi ne tikitinki na shiga zuciyata".
A raina na ce'Ashe kuwa har mu rabu bazan ko leƙa zuciyar taka ba, domin ba a taɓa cigaba da tafiya a haka ba'.
Ya ce"Ni fa saboda ban ɓoyewa ogana na kasuwa larurata ba, shi yasa ya ba ni damar zuwa da rana gida na dinga sauke nauyi, hala muka yi da waccen matar, amma ƙarshe da ta fara taɓarɓarewa ko na dawo sai ki ga ta bar ni a wahale, haka zan ja jiki na koma, daren ma wataran ta kulle ƙufa sai dai na kwana a falo, ƙarshe ma sai ta fara yin ƙunzugun ƙarya".
Ya girgiza kai ya ce"Ya subhanallah! Wato Maraƙisiyya ta gana min azaba, don Allah Assayyada kar ki zama kamar ita, ki daure ki cika dokokin aure da sharuɗansa".
Na ce"Allah Ya ba ni iko".
Ya ƙaraci iyayinsa da surutu ya fita, yana fita aka kawo wuta na saka wayata a caji, na kunna data, abun mamaki sai ga saƙon Sadam, sai da gabana ya faɗi, na duba na ga sallama ya yi min, ban amsa ba, kuma yana online, har zan kashe datar na ga ya fara typing, ya rubuto"Sayyada amaryar ustazai, ashe kin yi aure, ba ni da labari sai jiya, to Allah Ya ba ku zaman lafiya ya kawo zuri'a ɗayyiba".
Tsaki kawai na yi na danne lambar tasa na goge ta daga whatsApp ɗin, na fita ina wanke-wanke ina tunanin rayuwa, ni ban ga amfanin Sadam ya yi min fatan alkhairi ba, tun da na yi aure babu sauran wata alaƙata da shi, don haka na yanke idan ya sake yi min magana zan taka masa birki.
Sai da yamma 'yan'uwana suka zo, su huɗu ne har da Anisa, taliya na dafa musu kamar yadda ya ce, suka kawo min kayan gara, buhun shinkafa babba, katan ɗin taliya da na macaroni, katan ɗin indomi, sai galan ɗin man gyaɗa, magi, spices ɗin girki da na shayi, har da su kuka da busasshiyar kuɓewa, daddawa, kanwa da dai sauransu, ga kuma cincin da dubulan fal bokitai guda biyu, sosai na ji daɗin kayan, bayan sun tafi na kira Baba na dinga yi masa godiya, ita ma Mama na kira ta.
Kafin Ustaz ya dawo kamar yadda Sadam ya yi masa suna, na zauna na yi wa kaina karatun tanutsu, ko ba ni da dogon nazari dole na gane mijina matsolo ne, mammaƙonsa ya yi yawa, don haka dole na san dabarun da zan samo don ganin ulser ba ta kama ni ba, ko cuwa-cuwa dole zan fara don na dinga ƙoshi, a ganina tun da ba dafawa zan yi ya yi yawan da za a zubar ba, kuma ba wai zan dinga rabawa ba ne ai Allah ba zai kama ni da wannan ba, don haka na sungumi kwalin indomi na sauke kayana dake cikin sif na saka shi daga ƙasa, na mayar da kayan, da niyyar sai na dinga dafawa bayan ya fita, tun da ba ƙoshi za mu dinga yi ba, tunawa da na dafa guda ɗaya ɗazu ba bisa ƙa'ida ba ya da ni farke kwalin na ɗakko ɗaya na mayar kitchen ɗin.
Da ya dawo ya ga kayan ya dinga jera Alhamdulillah, ma sha Allah, sai ga mutum ya ɓarke da surutu, yana tsara yadda za a dinga sarrafa kayan abincin nan, ya dinga janyo addu'o'i wa iyayena ina amsawa, kuma addu'ar ta yi min daɗi.