← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 89

Sashe 47

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba ya ce"Mun gode, ba ma buƙatar komai daga gare ka, idan aka zo kan gaɓar da kai ne dole ka yi za a neme ka".

Ustaz ya yi shiru yana jimami shi kam ya so a bar shi ya dinga ganin Sayyada kullum, ya ce"Shikenan Baba, haka ma la ba'asa, ga wannan tun da yau na riga na siyo".

Ya miƙa masa ledar, Baba ya karɓa ya ce"Allah Ya amfana".

Ya shiga gida ya bar Ustaz yana shafa gemu.

Ina zaune Baba ya miƙo min leda, ya ce"Ga wannan inji mijinki, Sayyada idan kin san ba so kike ki koma gidansa ba to kar ya zo ki dinga fita barkatai, ko waya ban ga amfanin ku dinga yi ba".

Na ce"To".

Na buÉ—e ledar, zogalen ya ba ni sha'awa, na hau ci kuwa, sai da na kusa cinyewa na tuna ban yi wa Mama tayi ba, na tura mata ledar na ce"Mama ga zogale".

Ta ce"A'a ki ce ke kaÉ—ai, ke ce kike yunwa".

Na ce"Mama yunwa kuma?"

Ta ce"To idan ba yunwa ba daga kawo zogalen ba tunanin komai ki tusa shi a gaba? Haka kazar nan da ya kawo kika ci son ranki, ko tsoro ba kya ji, yanzu idan ma wata mallakar yake sakawa a ciki shikenan sai a wayi gari kina son shi da son komawa gidan shi".

Mama tana rufe baki tari ya sarƙe ni, sakamakon ƙwarewa da na yi da zogalen bakina, tsoro ne ya kama ni, na naɗe sauran zogalen na kai cikin shara, na kuskure bakina, na dawo na zauna jikina ya yi sanyi na ce"Yi haƙuri Mama, daɗi ya min ne".

Ta ce"Haƙuri ke ya kama Sayyada, idan zogalen kike so me yasa ba za ki faɗa ba a dinga dafa miki?"

Na yi shiru, na tashi na koma ɗaki na zauna na fara gwada layin Sadam, haka ta dinga ringing bai ɗauka ba, na gaji na haƙura, wasa-wasa sai da ya yi sati ba ya ɗaukar wayata, na yi masa massage babu amsa, a cikin sati na biyun ne na samu ya ɗauka, muka gaisa sama-sama na ce"Me na yi maka don Allah?"

Ya ce"Ba ki yi min komai ba, amma idan kin san ba wai kin yarda da batun zubar da cikin nan ba ne kar ki sake kirana daga yau, domin ban ga amfanin alaƙar ba".

Na ce"Ina son haihuwa wallahi".

Ya ce"Zai fi kyau ki ce kina son mijinki, ki ma daina fakewa da yaro".

Na ce"Wallahi ba haka ba ne".

Ya yi tsaki ya ce"Ina da abun yi".

Na sake kira bai ɗauka ba, duk na damu, ƙarshe ma sai ya saka ni a blacklist, hakan ya tabbatar min da gaske yake, na daina walwala ga yawan ciwon kai, sai dai na zauna a ɗaki na yi ta tunani, na rasa me yasa mutane suke da son kansu, ina son haihuwa sosai, amma ina son Sadam, ina fargabar ya ƙi aurena, na firgita da auren Ustaz, na tsorata da maza, ina fargabar idan ban auri Sadam da na saba da shi na san halinsa ba wa zan aura? Kar na auri wanda ya fi Ustaz tsanani, shi yasa rafkananniyar zuciyata ta fara raya min ko na amince kawai, tun da idan ya aure ni komai zai wuce na fara haihuwa, na yi masa massage na ce don Allah ya ɗauki wayata na gaji da yadda yake azabtar da ni, bayan awa ɗaya ya kira ni, ya ce"Sayyada ke ce kike azabtar da mu, na tabbata na fi ki shiga damuwa da tashin hankali, yanzu a ce ina kallo ina ji ina gani wani zai aure ki? Sayyada".

Na amsa.

Ya ce"Ni ne fa, Saddam ɗinki ne, ban yi zaton zan roƙi wannan ɗan abun ki ƙi yi mini ba, har kin manta soyayyarmu? Har kin manta irin zaman da muka yi? Kin manta irin abubuwan da kika yi min na yafe miki? Me zai saka na ƙara son zama da wacce ta so kashe ni idan ba ƙauna ba? Haba Sayyada ki yi min adalci mana, idan kin zubar wata nawa ne mun yi aure kin samu wani cikin? Ina da kishi a kanki, ba zan so ki samawa yaranmu 'yan uba ba, don Allah Sayyada ki amince, kar ki raba mu ki haramta mana kasancewa ma'aurata a karo na biyu, na yi miki alƙawarin farinciki har ƙarshen rayuwarki".

Jikina duk ya mutu, idan akwai abin da na tsana bai wuce Sadam ya tuna min na caka masa wuƙa ba, na share hawayen da ya sakko min na ce"Na amince Sadam indai hakan zai saka ka yarda da ni".

Ya ce"Alhamdulillah, yanzu ya kenan? Zan san yadda za a yi a samu maganin daga hannun Safna, gobe in sha Allah zan kawo miki, tun da bai kai wata biyu ba ba zai wani yi wahalar fita ba".

Na ce"To Allah Ya kaimu" Muka yi sallama, sai na ji raina fess.

Washegari kuwa sai ga kiran shi da azhar, ya ce "Maganin ya zo hannu fa My Baby"

Gabana ya faɗi, saboda har zuciyata ina son abin da yake cikina, ina so na haihu, kawai dai ba ni da wani zaɓi ne, saboda ina fargabar idan ya kufce min gidan wa kuma zan faɗa, na ce"Da sauri haka? Amma ya aka yi ta yarda ta ba ka?"

Ya ce"Sakawa na yi ta rubuta min, na ce mata wani abokina ne matarsa ta samu ciki kuma É—ansu watansa biyu, shi ne za a cire cikin".

Na ce"Ma sha Allah".

Ya ce"Ya za a yi ki fito ki karɓa?"

Na ce"Zan ce zan je gidan su Anisa, sai mu haÉ—u a hanya".

Ya ce"Ok, to bari zuwa la'asar ko?"

Na ce"Allah Ya kaimu".

Tun da muka gama wayar na ce da Mama zan leƙa gidan su Anisa, ta ce"Sayyada yawo fa ba naki ba ne".

Na ce"Wallahi iya nan kawai zan ke, kuma ba zan daÉ—e ba".

Ta ce"A dawo lafiya".

Kamar yadda muka tsara, haka na fita bayan ya ce min ya kusa ƙarasowa, muka tsaya a hanya ya ba ni maganin, har da gashasshiyar kaza da lemo, na karɓa na yi godiya, ba mu wani tsaya ko gaisawa ba kawai ya shiga mota ya tafi saboda tsaro, haka na sunƙe ledar a hijjacina har na koma gida, dab da magriba, sai da na idar da sallar isha'i na zauna na ci kazar a ɗakina, ina fargabar kar Mama ta jiyo ƙamshi, bayan ta ishe ni, na sha lemon, na ɗakko maganin, na tsaya ina kallon shi hannuna a kan cikina, ina jin son abin da yake cikina, a ce da kaina zan kashe ɗana? Ɗan da nake burin a ce yau na ajiye shi a doron duniya? Anya kuwa? Hawaye suka fara sakko min, a fili na furta zan yi komai ne ba da son raina ba, sai don son gyara gobena".

Na ɓallo maganin, na ɗauki ruwa, salatin da Mama ta rafka tare da shigowa ɗakin bagatatan shi ya dakatar da ni, har na saki ruwan hannuna da maganin cikin nuna rashin gaskiya, ta ƙaraso ta ɗauke ni da mari tass, na dafe kuncina na fara kuka, ta ce"Ashe ba ki da hankali Sayyada? Yau na tabbatar da wautarki mai girma ce".

Cikin ƙarfin hali na ce"Mama me na yi?"

Ta ce"Ubanki da uwarki kika yi, kin yi zaton ban san duk takunki ba? Kin yi zaton don yanzu kin girma na daina rainonki da kulawa da amanar Allah? To duk wayar da kika yi da Sadam jiya a kunnena kika yi, na taho zan kawo miki zogale na ji kina waya na dakata, na ji komai na ji shirinku, amma Sayyada kin ba ni mamaki wallahi, me yasa yaran ya zu ba kwa yi wa iyayenku adalci? Sayyada me kike nufi? Sadam ta fi miki kowa kenan? A tunaninki wannan soyayya ce? Duk mai sonki yana son farincikinki bari ki ji, Sadam ba ya sonki, kuma ko soyayyar juna za ta kashe ku ba za ki aure shi, na bar hanyarsa har abada ni ma, ba na tare da aurenku ko bayan raina, daƙiƙiya kawai wacce ba ta san ciwon kanta ba".

Daga haka ta kwashe maganin, kazar, da wayata ta bar ɗakin, ta bar ni ina gursheƙen kukan nadama da tashin hankali.

Na daɗe ina yi kafin na tashi na shiga ɗakin nata, na durƙusa ina hawaye na ce"Don Allah Mama ki yi haƙuri ki yafe min, na yi kuskure, wallahi sharrin shaiɗan ne, ba zai sake faruwa ba".

Mama ta ce"Ke da shi ne shaiɗanun, kar ma ku ƙalawa shaiɗan sharri, shi wannan Saddam ɗin har ya fi shaiɗan, ban da yana nufinki da sharri zai ƙi son ki haihu ki samu jininki ne? Ke jahilar ina ce kina cikin idda kin san ko yau mijinki ya ce ya mayar da ke kin maidu kuma wai ki fara kula wani banza wanda ba ya son cigabanki?"

Na sake rushewa da kuka na ce"Ki yi haƙuri Mama don Allah, wallahi ni ma ina so na haihu dama".

Ta zaburo ta ce"Tashi daga nan kafin na mangare ki, wallahi kin ci albarkacin abin da yake cikinki, da yau sai na yi miki dukan tashi ki sha kunu a cikin gidan nan".

Na ce"Don Allah ko ba za ki haƙura ki yi min hukunci ke kaɗai, don Allah kar ki faɗawa Baba, korata zai ƙara yi, na ji na haƙura da auren Sadam, amma don Allah kar Baba ya ji".

Mama ta ce"Ya zama dole ya ji, idan kina tsoron shi ai ba za ki aikata ba, kuma da kaina zan je gidan su Sadam É—in na sanarwa iyayen shi a yi mana tsakani, a kan shi rayuwarki ta lalace har yanzu kike cikin walagigi".

Da sauri na ce"Don Allah Mama ki yi haƙuri, wallahi tsautsayi ne, na yi na farko na yi na ƙarshe".

Mama ta yi banza da ni, na ci kuka na ƙoshi, sai da na ji dawowar Baba sannan na tashi na fito daga ɗakin, na saita kaina na ce"Baba sannu da zuwa".

Ya ce"Yawwa, Sayyada ƙalau ko?"

Na ce"Lafiya lau".
Chapter 47 · 0% Book details