← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 89

Sashe 51

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk nacinsa haka ya haƙura ya rabu da ita, da asuba yana dawowa daga masallaci ya shiga yi mata magiya, a dole ta ba shi, nan ma da ƙyar ta yakice shi, ta narke ta ce ba za ta iya yin aikin komai ba, Ustaz ya ce la ba'asa, ya shiga kitchen ya dafa musu shayi, ya tambaye ta da me za ta karya, ta ce danlali, ya soya shi da yawa, sannan ya ɗakko butter da biredin fa ya taho da shi jiya, ya haɗa komai ya kai dining, sannan ya je ya taho da ita tana ta narkewa, a baki ya dinga ba ta har ta ce ta ƙoshi, ya ɗauke ta ya mayar da ita ɗaki ya kwantar, tana cewa"Ni da ka bar ni a falo".

Ya ce"A'a, gara nan É—in, tun da ai kin ga share falon zan yi idan na gama".

Ya fita yana murmushi, a ransa kuwa ya yi haka ne don kar ya karya a gabanta, don ya san ta'asar da zai yi wa kayan shayi, Ustaz ya zauna ya zuba shayi a kofuna biyu, kowanne ya zabga madara da milo, mai shan shayi da sugan naira ɗari su biyu sai ga shi ya zabga wanda bai san na nawa ba ne, shayi ya yi kauri murtuk, ya saka shi a gaba, tass ya cinye dankalin duk yawanshi, ya ci rabin ƙaton biredin, ya yi hamdala gumi yana karyo masa, ya ce"Ma sha Allah, to fa indai aka cigaba da tafiya a haka la shakka yanzu zan murmure na zama mutum, bi ma'ana duk inda ya komaɗe zai taso, wa man taraka bati siddan".

Ya kwashe kanukan ya kai kitchen ya yi wanke-wanke, ya gama ya share ko'ina a gidan ya goge tass, ya zauna yana mayar da numfashi, yanzu kuma babu abin da yake so sai Rauda ta taimake shi, don haka ya tafi ɗakin don gwada sa'ar shi, bacci ya ɗauke ta, ya tuɓe ya hau gadon, yana fara taɓa ta ta tashi da sauri, ta kyaɓe fuska kamar za ta yi kuka ta ce"Wai da wane yaren zan yi maka bayani ka fahimta?"

Ya ce"Larurata ba ta jin kowane yare sai na ba da haÉ—in kai, kuma ai na yi miki bayani".

Ta ce"To a gaskiya ba zan iya ba, na gaji, dama haka ake auren?"

Ya ce"Haka ake yi mana, ke nufinki hutu kika zo? Da ake cewa aure ibada ne ai wannan ce ibadar, lada ne fa kike samu bila adadin, shin dama akwai wanda zai ce lada ya yi masa yawa ba ya buƙatar ƙari? Daure ki ƙara min kin ji, daga na yanzu zan daure in sha Allah sai kuma dare ko bayan la'asar haka".

Haka Rauda ta miƙa kai, duk jikinta ya yi sanyi, yau ɗaya har ta gaji duk yadda take jin sha'awa da zumuɗin abun, ta so ta daure ta rabu da shi har ya samu gamsuwar da yake cewa bai samu ba, amma da ta gaji ta ga ba za ta iya ba dole ta saka masa kuka, ya ƙyale ta.

Shi ya yi girkin rana ma, ya dafa musu jollof É—in macaroni, yana kitchen É—in ta shiga tana kallon yadda ya zage yana ta aiki, ta yi murmushi tana yi masa vedio a waya, ta ce"Sweetheart ya zama mai girki".

Ya yi dariya ya ce"Ai kuwa indai vedio za ki yi min har kya gaji, tun da aikin nan kullum ma ni zan dinga yi miki".

Ta ce"A haba dai, mene ne amfanina da zan bar mijina da aiki?"

Ya ce"Amfaninki shi ne ki dinga bawa mijinki hakkinsa, indai za ki dinga amsa kirana ba za ki dinga nuna gajiyawa ba to ni kuwa zan iya É—auke miki duka aikin gidan nan".

Ta ce"Zan yi iya ƙoƙarina na gamsar da kai in sha Allah".

Ya ce"Alhamdulillah, tabbas akwai alamun ke ce za ki zama mai share min kuka, ke ce matata har gidan aljanna, ina ƙaunarki Rauda, don Allah ki daure kin ji, da sannu ke ma za ki zama harija kin ga abun nema ya samu, sai mu ci karenmu babu babbaka".

Suka yi dariya duka, ta ce"Je ka huta kawo na taya ka".

Ya ce"Wallahi ba zan huta ba, ki je ki yi zamanki ki ƙara hutawa, yadda za ki ji daɗin bani tallafi anjima".

Ta shagwaɓe ta ce"Gaskiya sai gobe".

Ya ce"Ai wannan zance ne, na san za ki tausayawa mijinki".

Ta koma ɗaki ta zauna, ta kira lambar babbar ƙawarta, wacce ta kasance me aure da yaranta biyu, suka gaisa tana ta tsokanarta amarya, Rauda ta ce"Wai ni Zainab na tambaye ki mana?"

Ta ce"To ina jinki".

Ta ce"Don Allah dama haka auren yake? A yi ta yin abu babu gajiya, kuma sannan a yi awanni ana yi?"

Zainab ta kwashe da dariya ta ce"Ka ga farin shiga, dole a nemi sani a wajenmu, yanzu kin yarda ni yayarki ce ko?"

Rauda ta ce"Ba fa zancen wasa ba, don Allah ki ba ni amsa".

Zainab ta daina dariyar ta ce"Ai dama a satin farkon nan dole haka za ki gani, tun da yana cikin shaukinki ne, to dole sai kin daure kin yi haƙuri, amma da an kwana biyu kun saba shikenan sai komai ya daidaita za ki ga yana ragewa, ku fara ma fashin kwana ɗaya, daga nan kwana biyu, ni yanzu kin gan ni ma sai mu yi kwana biyar bai taɓa ni ba, idan na tuna lokacin amarci har mamaki nake yi, kamar ba zai wuce ba wallahi".

Rauda ta sauke ajiyar zuciya ta yarda ta kuma gamsu, ta ce"To da sauƙi tun da zai wuce, amma fa abun nan babu sauƙi wallahi har na gaji".

Zainab ta ce"Kowa da haka yake sabawa ƙawata, daure ki ƙara haƙuri, ki farantawa mijinki, ki sakar masa jiki kar ki bar space ɗin da matan waje za su ƙwace miki shi, don wallahi tun daga lokacin amarcin nan idan kina gudun miji a haka za ku ɗore ba kya sakin jiki da shi, ga kuma mata can a waje da suke nema ido rufe wata ma ita take biyan namiji don haka sai ki yi hankali, ki kama mijinki ram, don dai farko ne yanuy, amma nan gaba za ki daina jin wahalar abun, har ma ki zo kina neman shi".

Rauda ta ce"To Allah Ya sa, na gode Zee".

Suka yi sallama, ta shiga tunanin anya za ta iya kuwa? Amma tana son mijinta, kuma ta tsani kishiya, don haka dole za ta daure ta yi masa yadda yake so É—in, sai dai tana fatan lokacin da zai saba ya rage É—in ya zo cikin gaggawa.

Ya gama abinci suka ci, yana ta ba ta kulawa da nuna soyayya, idon a son ran shi ya ƙara abun nan, amma tausayinta yake ji, don haka ya yi wanka ya fice daga gidan, don idan yana ganinta ba zai iya riƙe kansa ba. Da la'asar ta yi baƙi, suka taya ta zama har magriba sannan suka tafi, sai bayan sallar isha'i Ustaz ya dawo gidan, ta tare shi da oyoyo, tana yi masa shagwaɓar ya bar ta ita kaɗai a gida, ya shiga ba ta haƙuri.

Ya ce"Me zan dafa mana?"

Ta ce"Ai na zata za ka taho mana da wani abun, ni bana cin abu mai nauyi da daddare fa".

Ya ce"To ai ba damuwa, kamar me kike so kenan?"

Ta ce"Ko irin kazar jiya ce ma, da fruit salad".

Ustaz ya É—an yi jim, kafin ya ce"To zo ki raka ni kitchen É—in, ki zauna kina yi min fira ina kallonki ina jin daÉ—i ina yi miki aiki, don wannan abubuwan da kika lissafa duk na iya su, ba dai na ga fruit a firjin ba?"

Ta yi murmushi ta ce"Sweetheart yau ka sha aiki fa, Please ka huta haka, gara a siyo É—in mu je na raka ka".

Ya ce"A'a Rauda, wai ya za a yi ga kayan aiki a gida kuma a tafi waje a siya? Wannan fa ya shiga layin almubazzaranci, shi kuma haramun ne".

Ta ce"To shikenan dama na ga kamar za ka gaji ne".

Ya ce"La ba'asa ban gaji ba, ba damuwa".

Ya shiga kitchen, ya ɗakko kaza daga cikin firji ya gyara, a ransa ya a shi wa iyayen Rauda albarka, don wannan aure shi gaba ta kai shi, gara a ce an haɗota da komai har da kayan miya fa, tana zaune tana yi masa fira, tana nuna masa wasu abubuwan ya gasa kazar nan a oven, ya haɗa fruit salad ɗin, ya yi wanka ya bar ta a falo tana ci, bayan ya ci shi ma, ya ce da wa Allah Ya haɗa mu? Aka shiga aiki, tunawa da maganar ƙawarta na cewar na ɗan lokaci ne yasa ta dauriya take iya ƙoƙarinta don ta gamsar da shi, ta saka a ranta za ta daure a gama cinye satin farkon ta gani.

08028966015
[29/10, 8:34 pm] Sadiya Abdulrazak: 31

Ustaz fa aka gyara zama, komai daidai duniya sabuwa, sosai yake ɓarje guminsa da Rauda, ga kuma cima mai kyau, a jikinsa yake jin har ya fara cicciko da komaɗarsa, sosai ya zamewa Rauda bawa, ya yi mata shara, wanke-wanke wanki, girki, sannan ya yi mata wanka, amma soyayyar sam babu armashi a wajenta, saboda wahalar da ita da yake yi, ga shi Zainab sai faɗa mata take ta dinga shan maganin ƙarin ni'ima idan wajen a jiƙe yake za ta dinga samun sauƙi, tana ta sha amma sam babu sauƙi, ƙarshe ta kawo mata gel ta ce ta dinga shafawa a wajen, yauƙinsa zai sa Ustaz ya samu gamsuwa da wuri, amma Rauda sai ta ga nan ma babu sauƙi, kamar ma ƙara tunzura shi take yi.
Chapter 51 · 0% Book details