← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 89

Sashe 13

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na amsa da amin, sai kuma ya ce"Don Allah ki yi min shikenan za mu zauna lafiya, kin fitini kanki duk kin rame, ba ki taɓa zuwa gida da zummar kina fushi da ni ba sai a wannan karon, don Allah ya zama na ƙarshe kin ji?"

Na ce"Idan ka so zai zama na ƙarshen in sha Allah, zan yi bacci".

Ya ce"A tashi lafiya" Ya fita ya bar min É—akin.

Tun daga ranar Sadam ya dage da kulawa da ni, kullum sai Mama ta kira ni ta ji lafiyata, don na faɗa mata ba ni da lafiya, amma ban ce mata ga abin da ya same ni ba, a yadda na lura duk ta yi zaton laulayi nake yi, har yanzu ba ta taɓa zuwa gidana ba, kuma ina zargin Baba ne ya hana ta zuwa. Bayan na warke muka cigaba da zaman lafiya da Sadam, kamar gaske ya rage yin chatting ɗin dare, yana ba ni lokacinsa kamar baya, a yadda ya ce min ya dakata da kula Safna har sai wata biyun ta yi an ga yadda zan kasance, sosai na hana idona idona baccin dare, rabin dare Sadam ya yi yadda ya so da ni, rabi kuma na raya shi da sallah, haɗi da addu'ar Allah Ya ba ni haihuwa mai albarka, sannan ina ta lallaɓa Sadam, ina kyautata masa, ado da kwalliya kuma na linka a kan wanda nake yi, bayan wata ɗaya ina ta addu'a da fatan Allah Ya sa kar na ga period ɗina, ai kuwa sai ga shi ya zo, ranar har kuka na yi, saboda a yadda nake sakarwa Sadam jikina wallahi ban yi zaton ba zan samu ciki a watan ba, ashe ba daga nan take ba, sai na tsananta addu'a, har sadaƙa nake kaiwa islamiyyar kusa da mu, haka nake turawa Mama kuɗi na ce ta sa a yi min sauka a islamiyya Allah Ya cika min burina, da ta ritsa ni da tambayar burin nawa na faɗa mata Sadam ne zai ƙara aure saboda ban haihu ba, yanzu kuma ga sharaɗin da laƙanya min, shi yasa nake fatan samunta ido rufe.

Haka wata na biyu ya zo, ina ta fargaba wallahi har ramewa na yi, saboda abinci ma ba ni da nutsuwar ci yadda ya dace, watarana muna zaune da shi nake tambayarsa "Wai yanzu a ina kuka kwana da batun yarinyar?"

Ya ce"Ai na faÉ—a miki sakawa na yi a É—aga auren ko? Idan kuma ba ki samu cikin ba sai a yi a lokacin da aka saka tun farko, kin ga yanzu saura sati biyu kenan".

Na ji na sare, saboda ban ga alamar ina da ciki ba, kuma a lissafi wani satin al'adata za ta zo, na ce"Don Allah ina neman alfarmarka".

Ya zuba min ido bai ce komai ba.

Na ce"Idan ban samu ciki a watan nan ba, ka dubi girman Allah da manzonsa ka ƙara min wasu watanni biyun".

Ya ce"A'a, ko kwana ɗaya ba zan iya ƙara miki ba Sayyada, indai ba ki samu cikin nan ba shikenan kawai ki yi haƙuri a yi auren nan a wuce wajen, ni ban ga dalilinki na tada hankali fa ba ma, ba fa gida ɗata za ku zauna ba, tana gidanta kina naki, kuma ba wai zan canza miki don na yi aure ba, ƙalau za mu zauna idan kika so".

Kamar zan yi kuka na ce"Ai ba zan iya zama da kishiya ba ne, me zan yi ka fahimci ba zan iya haÉ—a miji da wata ba? Kamar yadda na yi maka biyayya a baya na so abin da kake so, don Allah ka yi min alfarma ni ma ka ba ni dama ko da 'yar kaÉ—an ce, duk fa kai ne silar komai, da tuni na yi haihuwa biyu".

Ya ce"Hmm! Allah Ya zaɓa abin da ya fi zama alkhairi kawai".

Tun daga ranar bai sake tattaunawa da ni game da aurensa ba, ko maganar nake yi sai dai ya yi shiru, na ƙaraci kukana ba zai ce min ƙala ba, ana haka al'adata ta zo, tabbacin dai na karya wannan sharaɗin, ta tabbata ban samu ciki ba, hakan yana nufin auren Sadam sati ɗaya ya rage babu fashi.

Na fara al'ada ranar Juma'a, ranar Asabar yake ce min"Sayyada, na lura kamar jiya kin fara al'adarki ta watan nan ko?"

Na gyaɗa masa kai alamar e, na ce"Amma don Allah ka taimake ni ka ƙara min lokaci".

Na ce"Ba zai yiwu ba, Sayyada ki yi haƙuri kawai ki ɗauki ƙaddara, Allah Ya sa hakan shi ya fi alkhairi".

Na ce"Ta ya kishiya za ta zama alkhairi? Kishiyar da aka yi ta don a ƙuntata min? Sadam don gaskiya Allah ka sake ni".

Ya ja tsaki ya ce"Wallahi Sayyada kukan daɗi ma kike yi, ta ya zan ta baki da lallaɓa ki kamar wata jaririya? To ki je ki tambaya ki ji, ki tambayi matan da mazan su suka ƙara aure, haka suke yi musu komai a tsanake suna kwantar musu da hankali? Wallahi samu kika yi ma"

Na ce"Ai da ni da sauran matan ba É—aya ba ne?"

Ya ce"Ok ke da gwal aka sassaƙa ki ko?"

Na ce"Ba halitta nake faÉ—i ba, halacci da sadaukarwar da na yi maka, azabar da ka gana min kafin ka aure ni".

Ya ce"To Sayyada kin yi min halakci na butulce miki, a je a hakan sai me? Idan kin so ai kina iya rama butulcin, a iya sanina duk wani adalci da ya kamata na yi miki na yi, ko na ce ina kan yi, amma tun da kina ganin ban yi miki daidai ba to ki É—auki mataki".

Cikin kuka na ce"Ai matakin yana hannunka! Ka sake ni mana".

Ya ce"Za ki iya sakin kanki ai ko?"

Na ce"Kana nufin ka bar min igiyar sakin a hannuna?"

Ya yi banza da ni ya fice daga ɗakin, babu jimawa ya dawo da akwati 'yar tsakiya, ashe dama tana cikin motarsa, na saki baki ina kallon akwatin, ya ajiye min ya ce"Ga kayan faɗar kishiya nan, an kai kayan lefen Safna tun sati biyu da suka ce, saboda dama na san ba samun cikin za ki yi ba, wannan tsinken wasu idan aka cire musu shi, sai sun yi wata shida kafin su samu ciki, duk da an ce akwai masu samu da zarar an cire, don haka gara ma ki kwantar da hankalinki, kawai ki cigaba da addu'a idan Allah Ya dube ki ya ba ki shikenna sai mu gode masa, idan sex ne ke saka a samu ciki ai da azabar da kika gana min cikin wata biyun nan sai kin samu cikin 'yan biyu, don haka na daina ɓata lokacina, kuma ki daina mafarkin zan sake ki, idan kika cigaba da cewa na sake ki wallahi wataran sai na fasa miki baki, shashasha kawai, za ki ga alert, sai ki yi ɗinki da shi".

Daga haka ya shiga ɗakinsa ya rufe ƙofar da mukulli, ya bar ni tsaye ina kokawa da numfashi, sai da ƙyar na samu na daddage na rusa ihu, kuka kuwa ya ɓarke min, na tashi a haukace a buɗe akwatin, na shiga fito da kayan dake jere a ciki ina watsi da su a falon ina faɗin"Wallahi Sadam sai ka sake ni, ba zan zauna da kishiya ba!".

Ko sake fitowa falon bai yi ba, na je na dinga buga ƙofar ɗakin nasa ya ƙi buɗewa, da na leƙa ta windo sai na hango shi a tsakiyar gado yana waya haƙoransa a waje, da alama yana cike da shauƙi, ni ya mayar mahaukaciya, na durƙushe a wajen ina ta kuka, na yi mai isata na ta shi na shiga ɗakina, da asuba ina jin dawowarsa daga masallaci na fita na tare shi a falo, na ci kwalar rigarsa zan fara sababi, ai kuwa ya fincike ya wancakalar da ni a ƙasa, na shiga zaginsa ina yi masa Allah Ya isa, ya dinga dukana ta ko'ina, har ƙafa ya saka ya dinga tattaka ni yana zagina shi ma da faɗin, tun da haukan na zaɓi a yi ai shi ma ya iya mu zuba mu gani, tass ya yi min jikina ya yi tsami sosai, ya shiga ɗaki ya yi wanka na fice daga gidan, takaici ya hana ni motsawa daga kwancen da nake ina yin kuka kamar marainiya.

Sai da yunwa ta fara damuna sannan na tashi, siket ɗin jikina duk ya ɓaci da period saboda gumurzun da muka yi, don haka wanka na fara yi na gyara kaina, na shiga kitchen na ɗora indomi, na haɗa shayi, na karya, na sha maganin zazzaɓi don na fara jin alamaunsa, ciwon kai kuwa dama tuni ya dirar mini.

Haka na wuni cikin ƙunci, da rana na yi girki ɗan kaɗan na ci na rage na dare, yau ko shara ban yi ba, kayan nan na faɗar kishiya a falon suka wuni a warwatse, na so na kai ɗakinsa na watsa su, sai na tarar ya rufe da mukulli, ina jin dawowarsa na koma ɗakina na kulle, sai ga shi bai ma neme ni ba, hakan kuma sai ya ƙara ƙona zuciyata, na rasa ta yadda zan nunawa Sadam son shi da nake yi ne ya sa ba zan iya haɗa shi da wata ba, amma shi ya kasa fahimta, ni dai na san zan iya mutuwa idan ya auri wata, shi yasa nake yin iya yi na, amma na lura nema ake a ci ni da yaƙi.
Chapter 13 · 0% Book details