← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 89

Sashe 42

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba ya ce"To wannan ƙemararren kina ganin zai yi sakin nan ta ruwan sanyi ne? Ai ƙarshenta sai an kai ga kotu, kuma kwashe kayan shi zai tabbatar masa da cewar an fa gama zama da shi, wannan kamar wani sharar fage ne, da nuni idan yana da hankali".

Mama ta ce"To shikenan idan Allah Ya kai mu jibi sai a samu wanda za su je su kwashe".

Washegari da safe na ce"Mama ni kam yau ya kamata na je na tattare nawa sauran kayan, ba zan rasa abubuwana masu muhimmanci ba wanda ba na so a taɓa, kin ga gara na je na kwashe nawa".

Mama ta ce"Da mukulli a hannunki ne?"

Na ce"E akwai su a jakata".

Mama ta ce"Amma Sayyada kya je kuwa? Kar fa ku haÉ—u".

Na ce"Mama ba za mu haɗu ba, na san lokacin da yake dawowa daga kasuwa, ina da tabbacin daga ƙarfe tara zuwa kafin azhar ba ya gida".

Mama ta ce"Duk da haka dai, ban yarda da zuwanki ke É—aya ba, ki fara zuwa gidan Anisa ta raka ki".

Na ce"To bari na shirya" A zuciyata kuma ban yarda na je neman rakiyar Anisa ba, don ba na yi mata kallon 'yar'uwar da zan yi wani sirri da ita a yanzu.

Wajen goma da rabi na shirya na tafi, na samu gidan a rufe kamar yadda na yi zato, na saka mukulli na buɗe na shiga, na saka sakata na buɗe daƙin gadon na shiga na fara duba kayan da zan ɗauka, na gama tsaf, sai na zauna ina kallon ɗakin, da baƙin gadon da aka cutar da ni a kansa, na shiga kitchen na ga alamar yana yin girki, na fito da fulas ɗin shayina, da shi zan tafi saboda kar masu kwasar kaya su fasa min, ina cikin dube-duben na ji ana ƙwanƙwasa gidan, gabana ya faɗi, na je bakin ƙofar ban buɗe ba na ce"Wane ne?"

Ustaz ya zaro ido, zuciyarsa ta buga jin muryar abar muradinsa Sayyada, sai ya ji kamar Muryar ce take yi masa gizo, don haka ya sake ƙwanƙwasawa ta sake cewa"Wane ne?"

Ya ɗaga hannu sama ya ce"Alhamdulillah, Allah na gode maka, sannan ya yi gyaran murya tare da maƙale ta ya ce"Nisfu hayatynki ne Assayyada".

Gabana ya ba da wani sauti rass, rass, nan take nadamar zuwana gidan ta kama ni, me ya dawo da Ustaz gida yanzu? Na shiga tunanin mafita, na buɗe ko kar na buɗe? Wata zuciya ta ce kar na sake na buɗe, na rabu da shi ya gama bugunsa idan ya gaji zai tafi, duk nacinsa ai ba ya wasa da sallah, daga nan zuwa azhar idan aka shiga Masallaci dole zai tafi, wata zuciyar kuwa ta ce na buɗe kawai, idan na ɓata rai babu wata maganar banza da zai iya yi min.

Tsautsayi da rabon a yi ya saka ni ɗaukar shawarar nan, don haka na buɗe ina ɓata rai, ya faɗo ciki kamar an hankaɗo shi, yana washe baki ya ce"Alhamdulillah, Assayyada kin dawo, kenan bazata kika yi mini?" Ya danna sakata ya taho gare ni.

Na zabga masa harara na ce"Malam ba ni hanya na wuce, kayana na zo É—iba ai ni da aurenka har abada".

Ma juya don tattara kayan, ya ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yanzu Assayyada dama ba dawowa kika yi ba? Kar ki manta da ba sakinki na yi ba, kin san da haka ko?"

Na ce"Na sani, amma dole za ka sake ni ai".

Ban yi aure ba na ga mutum ya fara kokawar cire rigarsa, gabana ya faÉ—i na ce"Me kake nufi ne?"

Na ɗauki kayan zan wuce shi, ya damƙo hannuna daidai lokacin da ya zuge tazugensa wandon ya zube a ƙasa, na saki kayan saboda firgici har fulas ɗin shayi ya fashe, na ƙwala ihu ina cewa"Wayyo jama'a ku taimake ni".

Muka shiga kokowa, yana son ɗaukata, na ƙi ba shi dama, dukan shi nake ta ko'ina, amma wuya kawai nake sha saboda ƙasusuwan jikinsa, har dai ya yi nasarar kwarfe ƙafata na kusa faɗuwa ta gaba, ya saka hannunsa na faɗa na a kai, ya yi min ɗaukar amarya ya kai ni ɗaki har kan gado, na zabura na miƙe ya mayar da ni, ina zaginsa da kiransa bunsuru, ɗan akuya, ina ihu da neman agajin jama'a amma kamar babu kowa a unguwar nan, tun muna dambe har ƙarfina ya fara ƙarewa, don haka ya samu nasarar kai wa inda yake son kaiwa, bayansa dai ya sha duka, cizon da na dinga gasawa kafaɗarsa bai saka shi ya sare ba, sai da ya yi min abin da ban taɓa tunanin zai sake shiga tsakanina da shi ba, kuma iya son ran shi, har sai da ƙarfina ya ƙare na daina dukansa sai gunjin kuka da nake yi ina yi masa Allah Ya isa, kusan awa ɗaya kafin ya ƙyale ni, na tashi na saka kayana, skert ɗin dai ya yage, a haka na zura hijjabina da yake jalbab ne, na cusa yagaggen a cikin kayan da zan tafi da shi, sai ga shi ya fito daga ɗakin, ko suturta jikinsa bai yi ba, ya durƙusa a gabana yana cewa"Assayyada, ki yi haƙuri don Allah, wallahi ba nufina ba kenan, na kasa saita kaina ne, saboda na tara abun, na yi kewarki, ki dubi Allah ki yi haƙuri ki zauna kawai tun da ban sake ki ba".

Ko kallon shi ban yi ba, sai hawaye nake yi, wanda ban damu da sharewa ba, na kwashi kayan na fice daga gidan, yana ta kiran sunana da maƙale murya kamar munafuki.

Ina zama a cikin adaidaitasahu na sake rushewa da kuka sosai, gabana wara irin azaba yake yi min, na shiga rayuwar da na yi zaton na barta har abada, a yau na tabbatar da mene ne fyaɗe tsakanin mata da miji, na baya a gidan Sadam duk ƙarya nake yi, na yi nadamar auren Ustaz sau babu adadi, kuma na ji a raina idan duk duniya shi kaɗai ya rage namiji na haƙura da aure har abada.

Haka na ƙarasa gida a birkice kamar mahaukaciya, Allah Ya taimake ni Mama tana banɗaki, na yi wuff na shige ɗaki, da ta fito kuma ta yi baƙuwa suka shiga ɗaki, da wannan damar na yi amfani na fito na fara zuba ruwan wanka, Mama ta ce"Waye a nan?"

Na ce"Mama ni ce, ina zuwa kwata na faÉ—a, bari na yi wanka".

Kafin ta fito na yi wuff na shige banɗakin, ina jiyo ta a tsakar gidan tana tambayar ban ji ciwo ba? Na ce"E ƙaramar kwata ce".

Ina wanka ina kuka, na yi na tsarki na yi na sabulu sannan na fito, na yi ƙoƙari sosai don ganin Mama ba ta gane ba, amma sai da ta zarge ni, saboda yadda idanuna suka yi jawur, da na ce mata kaina ke ciwo sam ba ta yarda, ta rabu da ni ne kawai, na wuni cikin damuwa, na kwana ban runtsa ba, zuciyata sai zafi take yi mini.
[23/10, 7:29 pm] Sadiya Abdulrazak: 26

Washegari na tashi da zazzaɓi da ciwon kai, kafin azhar ya rufe ni ruf, na yi rigijib, sai kuka nake yi, ita Mama a zatonta kukan ciwo ne, ba ta san kukan zafin abin da Ustaz ya yi min ba ne, ta ce na je asibiti na ƙi zuwa, na sha magani dai ina ta kwanciya.

Aka je kwasar kaya wajen ƙarfe tara, Ustaz yana gida lokacin, suka kwankwasa ya buɗe, suka gaisa a mutunce, suka yi masa bayanin an zo kwasar kaya ne, nan fa ya yi tsalle ya dire ya ce"Kayan wa za a kwashe? Shin kun manta ban saki matata ba ko kuwa magagin bacci kuke yi"

ÆŠaya daga cikin matan ta ce"Ko ka sake ta ko kar ka saki bai dame mu ba, amma mu dai mun zo mu kwashe kaya, saboda".

Ustaz ya ce"A gaskiya ba zai yiwu ba, ko Allah Ya ƙaddara akwai rabuwa a tsakaninmu ba zan yarda a kawashe kaya ba sai ta gama iddarta, don haka ku koma ku faɗa musu kwasar kaya ba yanzu ba, bi ma'ana ban lamunce ba".

Ya ja suka ja, ƙarshe dai ya banke ƙofar ya saka sakata, a dole suka juya suka koma, ai kuwa ran Mama ya ɓaci da jin saƙon Ustaz, Baba ya ce a rabu da shi, ni ma raina ya ɓaci, fargaba ta sake kama ni, tsanarsa sai hauhawa take a zuciyata.

Ƙarin wani abun takaicin ma sai ga shi ya haɗo kan manyan unguwarsu da na unguwarmu da limamai wai sun zo su yi wa Baba nasiha ya yi haƙuri ya ba wa malam Ashir matar shi, ba a shiga tsakanin ma'aurata, Baba tun yana ɓoye musu dalilin son kashe auren har ya fito ya sanar da su hariji ne shi yasa zaman ba zai yiwu ba, nan Ustaz ya yi farat ya ce ai zai gyara zai rage duk yadda Sayyada ta tsara haka za a yi zaman, wasu cikinsu suka yarda da maganarsa, tare da bawa Baba shawarar a gwada a gani, wasu kuma suka ce rabuwar ce maslaha, domin tabbas ya cutar da Sayyada, ƙarshe dai Baba ya roƙi da su saka shi ya sakar masa 'ya, idan ba haka ba cikin satin nan zai kai shi kotu a san abun yi, haka taro ya watse Ustaz ya ƙi yin saki.
Chapter 42 · 0% Book details