Sashe 85
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na hau gadon na kwanta, shi kuma ya kashe hasken É—akin ya kwanta ya juya bayan kamar yadda ya ce.
Sai dai babu daÉ—ewa ya ce"Sayyada".
"Na'am" Na amsa ina ƙara matsawa gefe.
Ya ce"Ba ki yi kewata ba ko?"
Na ce"Ai kai ne ba ka yi kewata ba, shi yasa kake ta ja min rai".
Ya ce"To bari, É—an matso ki ji".
Na ce"Bacci nake ji, ba abin da zan ji".
Ya ce"Sayyada ki fa daina mazewa, na san cike kike da kewata, ki matso na ba ki hakkinki".
"Ai tun da hakkina ne na yafe maka, duk sanda na nema sai a ba ni".
Ya yi dariya ya matso ya janyo ni ya ce"Kin rantse sai ni ne zan dinga binki da hakkinki ke ba za ki nema ba ko? Ke ce kawai kike ruguza sarautata Sayyada".
Na ce"To ai ko sarkin gasken ma idan aka zo wannan batun ajiye sarautar yake yi ballantana kai taka-haye".
Ya ce"Yau kuwa za ki ga taka-haye, idan ba ki fara yi min jam'u da kirari ba sai gobe zan saurara miki".
Na ce"Allah Ya huci zuciyarku, ƙarya nake 'yar talakawa".
Muka yi dariya a tare, ya kwashe ni muka shilla duniyar masoya.
Faɗin nutsuwar da muka samu ɓata baki ne, wannan daren ya fi kowane dare a tsayin zamanmu samun nutsuwa, don na gyara kaina sosai, ko daren farkona a gidan Sadam albarka, mai martaba ya yaba ya ƙara, da safe ya ba ni tukuici mai nauyi, sannan ya ce na yi masa alƙawarin ba zan yi planing ba, saboda yana son haihuwa da yawa, yana so ya tara yara tun da girma yake, na yi masa alƙawari kuma na amince har zuciyata, tare da yaƙinin ko yau na samu wani cikin ba zan damu ba.
Na fito da kayan tsarabar da na zo da shi, na warewa Hajiya Halima nata na ce masa ga shi idan ya shiga ya miƙa mata.
Ya zabga min harara ya ce"Ni ɗan aikenki ne? Sai ki bari idan Dauda ya dawo, ko kuma idan Daddy ya yi ƙafa ki aike shi".
Na ce"Ni fa ba haka ba, gani na yi ai za ka shiga dole".
Ya ce"To ke ma dole za ki shiga ki gaishe ta ki kai mata, idan ba haka ba ki bar shi ba ta so".
Har zai fita ya dawo ya ce"Zan faɗa mata indai ba da kanki kika kai mata ba kar ta karɓa, kuma idan ba ki ba ta tsarabar nan ba na san zaman da zan yi da ke".
Wani tunani na yi, idan har da gaske zai faɗa mata na san ba za ta taɓa barin ƙofar nan ƙalau ba, sai ta san tuggun da ta haɗa min, don haka na tashi da sauri na ce"To na ji mu je tare sai na ba ta".
Na ɗauki kayan, shi kuma ya ɗauki Daddy muka fita, muna tafe yake cewa"Wallahi Sayyada ina tausayin matata, rashin haihuwa ƙaddara ce mai zafi, sai mutum ya jure, shiyasa nake ta addu'ar Allah Ya sanyaya mata ranta, sannan don Allah ki taya ni ganin ba mu yi wani abu da zai sosa ranta ba a kan wannan yaron".
Na ce"In sha Allah zan yi iya yina".
Ya ce"Ina so ki dinga kai mata shi duk safiya, ko kuma idan za ki yi wani abun, ya zamana yana da É—aku biyu dai, yadda za ta dinga jin daÉ—i da ganin ita ma tana da É—a".
Na amsa da to, muka shiga ɗakin, tana cikin ɗaki, ya shiga ya kira ta, sai ga su sun fito tana riƙe da ɗan tana ta murmushi, na gaishe ta, ta amsa tana cewa"Ya ɗana ya kwana?"
Na ce"Lafiya ƙalau"
Na ba ta tsarabar na tashi zan tafi, tun kafin ya fara rungume ta raina ɓaci.
Amma kawai sai na ji ta fashe da kuka, kafin na juye ta ce"Sayyada ina neman alfarma, mai martaba ku saka baki don Allah ko zuciyata za ta yi sanyi".
Duk sai ya ruɗe yana tambayar me take so, na dawo na zauna, ta ce"Ina son yara tun ina yarinya, sai ga shi Allah bai ƙaddara ina cikin mata masu haihuwa ba, mai martaba duk da dai ɗanku nawa ne amma akwai bambanci indai Sayyada ba ta buɗe zuciyarta ta zauna da ni lafiya ƙalau kuma da zuciya ɗaya ba".
A raina na ce'An zo wajen'.
Mai martaba ya ce"Hajiya Sayyada ba ta da matsala fa, kuma ai ga shi kuna zaune lafiya, yanzu mene ne buƙatarki?"
Ta ce"Ina so ne mu ƙara samun kusanci sosai, ta ɗauki Kamar yaya ba kishiya ba, sannan wannan yaron ya dinga kawo min shi don Allah, kuma ta dinga zuwa nan tana zama muna wuni ko kuma ni na dinga zuwar nata, alfarma za ki yi min Sayyada, saboda soyayyar wannan yaron da ta kama ni, don Allah ki nuna masa ni ma uwarsa ce".
Na ce"In sha Allah zan dinga kawo miki shi, Allah Ya huci zuciyarki".
Tana shassheƙar kuka ta ce"Na gode sosai Sayyada, Allah Ya haɗa kanmu".
Mai martaba ya ce"Wannan yaron da duk wanda za a aifa ke ma É—anki ne ai, haihuwarsa ce kawai ba ki yi ba, kina da iko da su".
Ta ce"Na gode ranku ya daɗe, Allah Ya cigaba da dafa muku, Ya biya muku buƙatunku na Alkhairi".
Na tashi na ce"To ni zan je na ƙarasa aiki, tun da ban faɗawa mai taya ni ɗin na dawo ba, sai ka dawo Allah Ya tsare".
Ya amsa da Amin, na fita na koma sashena, na zauna ina tunani, ni dai ba zai taɓa yiwuwa na dinga zuwa sashenta na zauna ba, ƙarya ne wannan, sai dai ita ta zo nawa sashen idan za ta iya, ɗa dai tun da na san babu yadda zan yi na nuna masa ba lallai da gaske take son shi ba to zan dinga ba ta shi idan ta zo ta karɓa, don ba zan kai mata ba, tun da ba neman kai nake yi da shi ba.
Mai martaba ya fita babu jimawa sai ga mai aikinta ta dawo da yaron yana ta kuka, na karɓe shi gabana yana faɗuwa, ta ce"Kuka yake yi ina ga yunwa yake ji, ta ce idan ta sha a dawo da shi".
Na ce"To" na karɓe shi ina jijjiga shi, na fara shayar da shi, sai ya yi bacci, ko da ya tashi ma ban mayar da shi ba, don ni ma ina son ganin abuna.
Da ya dawo ya fara tsayawa a ɓangarenta, sai ga shi ya shigo min ransa a ɓace, na tare shi da tambayar lafiya? Ya ce"Sayyada ba na son fitina fa, ni gaskiya indai kika ce fuska biyu za ki dinga yi min to za mu dinga samun matsala da ke".
Yana faÉ—in haka na san ta haÉ—a min wani tuggun ne, na ce"Me na yi maka?"
Ya ce"ÆŠazu da ke aka zauna aka yi magana da Hajiya a kan yaron nan, me yasa ba ki ce min ba ki amince ba?"
Na ce"Me na yi wanda ya nuna ban amince ba? Me na yi mata?"
Ya ce"Ta ce min ina tafiya kika zo kika É—auki yaron, kuma ta zo da rana za ta É—auke shi kika hana".
Na yi shiru na kasa magana.
Ya ce"To ba na son haka, ba zan lamunta ba".
Na ce"To, ka yi haƙuri".
Jikina a sanyaye na kawo masa abinci, na zauna na shiga ba shi a baki irin yadda yake so, sai dai na ƙi sakin fuskata saboda zuciyata babu daɗi, shi da kansa ya lura da hakan ya ce"Sayyada, ba na so na dinga yi miki faɗa, ki daina don Allah, ki dinga kiyayewa, idan kika lura matar nan abar tausayi ce, ko yaya kika nuna ba ta isa da ɗan nan ba kuma na yi shiru ban tsawatar ba, za ta ga kamar na koma ɓangarenki ne gabaɗaya saboda kin haihu ita ba ta haihu ba".
Na ce"To".
Ya ce"Ban gane to ba, magana za ki yi ki faÉ—i dalilinki na yi mata haka".
Na ce"Ko na faɗa ba za ka fahimta ba, tun da ka yarda da ita, ita ce mai gaskiyar da komai ta faɗa daidai ne, babu buƙatar ka ji ta bakina ko kuma ka yi bincike".
Zai yi magana na ce"Don Allah ba sai ka ce komai ba, Shikanan na ɗauki laifin ka yi haƙuri, ba dai sashenta kake so na dinga zuwa ba kuma na dinga kai mata ɗa? Zan je in sha Allah, idan ka ce na bar mata ɗan ma sai na bar mata, ai dai ba a mahaifiya biyu sai dai uwa biyu".
Ya ce"Kina da rigima fa, shikenan a bar zancen".
Muka bar zancen, yau ma muka yi kwanan farinciki kamar jiya.
Washegari wajen ƙarfe goma mun goma komai, na ɗauki Daddy na tafi ɓangaren Hajiya, ba ta falo tana cikin ɗaki, mai taya ta aiki ta leƙa ta faɗa mata na zo, amma matar nan ta ƙi fitowa, na ba ta minti talatin ina zaman jira, goma da rabi tana yi na tashi na tafi, na kira shi a waya na yi masa ya aiki, ya ce"Lafiya lau ya mutanen gidan? Kin kaiwa Hajiya ɗanta?"
Na ce"Na je, ba ta falo kuma na yi jiran minti talatin ba ta fito ba, don haka na tafi".
Ya ce"Ƙila bacci take yi, don Allah anjima ki koma".
Na amsa da to, na bi umarninsa da yamma ma na leƙa, amma ina shiga na kunna recording a wayata, lokacin tana falo tana tsifa, na zauna na gaishe ta fuska babu yabo babu fallasa, ta amsa a daƙile, na ce "Ga Daddy na kawo miki ku gaisa".
Ta ce"Ai kin ga tsifa nake yi ko? Ko ki jira ko kuma ki kwashe shi ku koma inda kika fito".
Na ce"To mun gode".
Ta ce"Umma ta gaida Assha, gayyar tsiya, mai suffar munafukai, ni da Isma'il mutu-ka-raba, ko duniya za ki haifa masa ba zai juya min baya ba, domin tun da na riga ki kwana sai na riga ki tashi!".
Na ce"Hmm, to a yi dai mu gani".
Na fice daga É—akin, na kashe recording É—in.