Sashe 23
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na yi shiru, ya cigaba da cewa"Akwai wani lamari da ya kamata ki sani game da ni, a gaskiya ina da wata larura, wacce ya kamata a ce na sanarwa da matata lafin auren, to sai shi Baba ya ce babu damuwa ya san za ki amince ki karɓe ni a duk yadda nake".
Gabana ya faÉ—i, na ce"Wace larura ce?"
Ya yi murmushi ya ce"Ba wata babba ba ce, wannan larura ita ce, ni dai ban kasance mutum kamar kowa ba, bi ma'ana dai ni hariji ne, wato mai yawan buƙatuwa, amma fa ga iyalinsa, ga halalina kamar dai ke ɗin nan da kika kasance halal ɗina a yanzu, ina da buƙata mara adadi, wanda sai kin zauna da ni za ki fi fahimta, ina fatan hakan ba zai kawo mishkila a zamanmu ba".
Jikina ya yi sanyi, ina auna kalmar hariji, ko zan iya? Sai zuciyata ta shiga raya min zan iya, tun da dai Sadam ma ai hariji ne, hmm ashe dai na jahilci kalmar hariji.
Na ce"In sha Allah zan iya, Allah Ya ba mu zaman lafiya".
Ya ce"To Alhamdulillah, mun yi magana da Baba ya ce wani satin za ki tare, ina da gidana mai É—aki biyu sai kitchen da banÉ—aki, yana nan tsaf, sai jiranki kawai da yake yi".
Na yi murmushin yaƙe.
Ya ce"Assayadda zan so na gan ki ba tare da hijjabi ba, shin hakan zai yiwu ko sai kin tare?"
Na ce"Zan so a ce dai na tare É—in, amma idan umarni ne kake ba ni zan cire".
Ya ce"A'a, la ba'asa, ba umarni ba ne, Allah Ya kai mu ranar Juma'ar".
Na amsa da amin, ya miƙo min wayarsa ya ce"Yawwa sai ki saka min lambarki a nan ko?"
Na zo karɓa, ya riƙe hannuna ram, na kalle shi na ga yana lumshe ido, ya ce"Assayada duk da ba umarni na ba ki ki cire hijjabi ba, amma da kin ce da zan ji daɗi".
Na ji kamar na rusa ihu don takaici, ni gaskiya wannan mutumin sam bai yi min ba, amma kuma dole zan zauna da shi na yi masa biyayya ko don Baba ya yafe min, na karɓi wayar na saka masa lambar na ba shi, sannan na zare hijjabin, riga da siket ɗin leshi ne a jikina, kuma ba su kama ni ba, ya fara faɗin "Ma sha Allah, ma sha Allah".
Sannan ya ce"Shin za ki yi mini alfarma ki matso daga kusa?"
Na haÉ—iyi wani yawun takaici na muskuta na matsa, ya ce"Ma sha Allah, ya matso yana yi min raÉ—a a kunne ya ce"Ba ki tambayi sunana ba Assayyada".
Na ce"Na manta".
Ya ce"Sunana Ashir".
Na ce"To".
Ya riƙo hannuna ya ce"Na roki wata alfarmar?"
Na ce"A'a don Allah ka yi haƙuri, nan gidan iyayena ne, idan muka tare ba ma sai ka nemi alfarma ba".
Ya ce"To, to, to, la ba'asa, hakan ma ya yi, to ni zan tafi, domin na ga zaman ba zai haifar da fa'ida ba, sai mun yi waya, zan sake zuwa kafin Juma'ar".
Na ce"Na gode, ka gaida gida".
Ya fita daga É—akin, na saka hijjabina, na yi shiru, hawaye ya sakko min.
[07/10, 8:18 pm] Sadiya Abdulrazak: LITTAFIN NAN NA KUƊI NE A KAN NAIRA 700
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay
Shaidar biya ta nan
08028966015
15
Tunani na shiga yi, wannan shi ne mijina? Ashe dai ƙaddarata akwai zaman aure da namiji ba ɗaya ba, a baya kafin na auri Sadam gani nake idan ba shi na aura ba har abada ba zan iya zaman aure da wani ba, sai ga shi komai ya canza, yanzu dai ga wanda ƙaddara ta zaɓa min, kuma dole na yi masa biyayya ko da ba na son shi, ko don Baba ya yafe min, yi wa Baba biyayya na zauna da Ashir lafiya ne kawai zai sa ya gane nadamata, don haka zan daure na zauna da shi ko ba na son shi, kasancewarsa hariji kuma ina tunanin babu wata damuwa, tun da Sadam ma haka yake da yawan buƙatuwa, tun da na saba ai kuwa zan jure, na ɗaɗe zaune a ɗakin cikin duniyar tunani, shigowar Mama ne ya sa na dawo daidai, ta zauna tana cewa"Sayyada ki yi haƙuri, don Allah ko ba kya son bawan Allahn nan ki daure ki yi masa biyayya ku zauna lafiya, saɓa masa kuwa kin san zai ɓata ran babanki, kuma zai ɗauka shikenan ba za ki sake yi masa biyayya ba, bai isa da ke ba, kuma burinki na ganin ya yafe miki ma ba zai taɓa cika ba".
Na ce"In sha Allah Mama zan zauna da shi lafiya".
Ta ce"Allah Ya ba ku zaman lafiya, ga abu ya zo a ƙurace, amma wannan gyara da kika yi na maganin sanyi ai ba na jin ya bar jikinki, duk da haka gobe zan sa a kawo wasu sai ki fara, idan kuma akwai inda kike siyan na gyaran jiki sai ki siya".
Na yi shiru kaina a ƙasa, ta ce"A nan za ki kwana ne?"
Na girgiza kai alamar a'a.
Ta ce"Ya kamata ki tafi gida kin sa tara ta gota".
Na tashi na É—auki wayata na fito, Baba ya ce"Za ki tafi gida ne?"
Na ce"E".
Ya ce"Yanzu na kaiwa babanki sadakinki yana hannunsa".
Na ce"To, sai da safen ku".
Na tafi, a gidan na tarar da Anisa, da alama kwana ta zo yi, na yi wa yaranta wasa, ita kuwa kallo É—aya na yi mata na É—auke kai, Umma ta ce"Sayyada ashe kuma haka abu ya faru, babanku ya dawo daga masallaci yake faÉ—a min".
Na ce"E wallahi".
Ta ce"To Allah Ya sanya alkhairi ya nuna mana ranar tariyar lafiya".
Ban amsa ba, na shige É—aki, Anisa ta biyo ni, babu yabo babu fallasa ta ce"Sayyada amarya, ashe an É—aura aure".
Na ce"Idan Allah Ya nufa duk gulmar algungumi sai dai ko ya haƙura ko ya haɗiyi zuciya ya mutu".
Ta ce"Ikon Allah,to kenan wane ne munafuki?"
Na ce"Wanda ya tsargu".
Kafin ta ba ni amsa kira ya shigo wayata da baƙuwar lamba, haka kawai jikina ya ba ni mijina ne, na ɗauka, na kuwa ji wannan maƙalalliyar muryar tasa ta ustazai yana yi min sallama, don na cusawa Anisa haushi na ce"Wa Alaikassalam mijina".
Ya yi murmushi mai sauti ya ce"Alhamdulillah, ma sha Allah! Assayyada na ji daɗi sosai da kika kira ni da mijinki, duk da dai dama haka yake a bisa ƙa'ida, amma da kika furta ɗin sai na ji assurur ya kama ni".
Na kalli Anisa da ta kwanta a katifa, na harare ta ta gefen ido na ce"To idan ban kira ka da mijina ba wa zan kira? Yau na fara ganinka, amma sonka ya cika zuciyata babu masaka tsinke, har nake jin anya kuwa ban zaƙe ba?"
Da sauri ya ce"La la la, la ba'asa ya Sayyada, sam ba ki zaƙe ba, wannan shi yake nuna ni da ke mun karɓi hukunci Allah kenan, Alhamdulillah, duk da dai ɗazu na yi mamakin yadda ba ki saki jiki da ni ba".
Na ce"Haba duk firar da muka yi me kuma kake saka ran zan iya yi maka bayan nan?"
Ya ce"Alal haƙiƙa kin saki jiki, amma iya na fatar baki ne, ni a zatona za ki zauna dab da ni mu yi firar fahimta juna, musamman ma da na sanar da ke larura ta, Assayyadda".
Na ce"Na'am".
Ya ce"Zan so a ce kin yi min tambihi a kan kalmar hariji, domin ina so na san cewa shin da gaske kin gane me kalmar take nufi kuwa?"
Na ce"Me yasa kake tunanin ban fahimta ba?"
Ya ce"Saboda mata uku na nema aure bayan rabuwa da matata, amma idan na ga dacewar sanar da su ni hariji ne sai su ce ba za su aure ni ba, duk kuwa da irin natija ta, kodayake ba a son yabon kai, sai na yi mamaki da ke kika amince tashin farko, shi yasa na yi zaton ko ba ki san kalmar ba".
Na ce"Na sani mana, kuma mijina na baya ma ai haka yake".
Ya ce"Allahu akhbar! Alhamdulillah, Alhamdulillah, to a gaskiya ni da ke mun yi dace, mun samu rabo mai girma, domin kuwa Allah ne Ya dube ki ya ba ki ni, domin ba a ce ba ni kika aura ba, akwai yaƙini mai girma na cewar ba za ki iya zaman aure da wanda ba hariji ba, hakan take ni ma a gare ni, idan na auri wacce ba irin halittarmu ɗaya ba, akwai hasashe mai girma a kan cewar za ta cutu, kuma za ta iya tauye mini hakkina idan ba ta ji tsoron azabar Allah ba".
Na ce"Uhm!" Don na fara gajiya da zancen harijancin haka, wannan mutumin ban ga alamar yana da kunya ba, yau fa ya san ni kuma daga ganin an ɗaura mana aure sai ya ɓare baki ya dinga sakin wannan maganganun haka?
Ya ce"Assayyada"
Na ce"Na'am Ya sayyadina".
Da wata murya kamar raÉ—a ya ce"Waccen matar tawa da muka rabu sau biyar nake kiranta a rana, shi ma saboda akwai sauran al'amuran rayuwa ne, shin za ki iya jure hakan?"
Wallahi na yi zaton kiran waya yake nufi, don haka na ce"Me zai hana, ni kira biyar ma ai ya yi min kaÉ—an"
Ya ce"Allahu akhbar! Allah shi ne abun godiya, wato dai a bisa dukkan alamu ke ce, bi ma'ana ke ce wacce nake ta roƙon Allah a ƙiyamul laili ya ba ni ke, Alhamdulillah".
Na yi yar dariya na ce"Ni ma ina kyautata zaton kai ne".
Ya ce"Ƙwarai kuwa".
Na ce"Zan kwanta, ina jin bacci sosai".
Ya ce"Ma sha Allah, To amma kar ki manta da sallar dare, yanzu kafin ki kwanta yaba da kyau ki yi nafila ki raka'a biyu ce, tana da fa'ida, saboda ko da ba ki samu tashi a tsakiya ko ƙarshen dare ba, bi ma'ana idan bacci ya yi miki nauyi, kin ga da sauƙi tun da kin yi a farkon daren".
Na ce"Hakane, na gode da tunatarwa".
Ya ce"Hmm zan so a ce kina gefena a yanzu haka, da abubuwa da dama sun faru".
Na yi dariya na ce"Sai da safe".
Ya ce"Allah Ya tashe mu lafiya".