Sashe 43
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin satin kullum sai ya zo, ba na fita, ba dama na kunna data sai na ga voice ɗin shi, ina ga dai aron waya yake yi yana yi min voice, da na gaji na goge whatsApp ɗin duka daga wayar, sati yana cika watarana da daddare Baba ya faɗa min gobe za a je Hizba a fara ta nan, tun a daren ya faɗawa Ustaz ya zo su je Hizba sai a tattauna a ji hukuncin wannan auren nasu, ya ce to zai zo, amma haka aka dinga kiran shi bai zo ba, Baba ya ce mu tafi, muka je Hizba muka shigar da ƙorafinmu, suka karbi lambar shi suka kira, yana ɗagawa suka yi masa bayani tare da ba shi umarnin ya zo, babu jimawa ya zo tare da ƙanin mahaifinsa, sai yanzu na lura da ramar da ya yi, ya ƙara yin zuru-zuru, sam ba shi da nutsuwa, aka sake zube zance aka tambaye shi hakane?
Ya yi gyaran murya ya ce"Tabbas haka ne, ni hariji ne, to amma sai dai ban yaudare ta ba, tun farko kafin auren na so na sanar da shi Baba, sai ya ce babu wata damuwa a ɗaura kawai, amma kafin a tare sai da na faɗa mata ita Sayyada ga ta nan, ɓaro-ɓaro ban ɓoye ba na ce mata ni hariji ne, ta ce ita ma mijinta na baya hariji ne, don haka babu damuwa, har ma na ce mata a kullum zan dinga nemanta dau biyar ta ce ta amince kuma har sama da haka ma za ta iya jurewa, sai bayan an tare kuma komai ya canza".
Hawaye ya sakko masa ya share, ya ce"Allah ne shaidata, Sayyada ta cutar da ni, tun da aka yi auren nan daidai da rana ɗaya ba ta taɓa barina na ƙoshi ba, tun da kwance take yi min kamar ruwa, ba ta da adalci sam, a ce na ba ta ci, sha, muhalli da sauransu amma ta dinga guduwa saboda 'yar nutsuwar da nake nema daga gare ta? Ga ta nan ai idan sharri na yi mata ta musa".
Aka tambaye ni shin ya sanar da ni shi hariji ne? Kunya duk ta kama ni na ce"E ya sanar da ni".
Mai yi mata sasancin ya ce"To ya aka yi kika yarda za ki zauna da shi, sannan kuma kika canza magana?"
Na ce"Ni ban san abun nashi ya kai haka ba, kuma bayan na gane ba zan iya ba ai na ce masa ya sallame ni amma ya ƙi, zamanmu akwai cutarwa, ya cuce ni, ya saka min jinyar zuciya da ta gangar jiki, ba zan iya cigaba da zama da shi ba, kashe ni zai yi...". Na fashe da kuka
Baba ya ɗora da faɗin"Har ciwon damuwa ne ya kamata ta sha jinya saboda wanann larura ta shi, sannan har ciki ta samu ya zube saboda yanayin nashi, Sayyada yarinya ce, ya fi ƙarfinta, ba za ta iya ba, don haka ni ba sasanci na zo nema ba, a raba auren kawai".
Ustaz ya ce"Don Allah a yi haƙuri, ni fa na karɓi laifina kuma na ce zan gyara, zan rage za mu daidaita abun, ai na faɗa mata duk yadda ta tsara haka za mu yi".
Mai sulhu ya ce"To Baba ka ji, shi sulhu alkhairi ne, za mu so a bar yaran su sasanta, tun da har ya ce zai gyara sai a yi haƙuri a ƙara ba shi dama a gani..."
Kukan da ya kwace min ne ya dakatar da sauran maganar da ya kwaso, na ce"Ba na son shi, ba zai iya gyarawa ba, kashe ni zai yi".
Shi ma Ustaz ya fara kuka da shassheƙa ya ce"Don Allah ku yi min adalci, kar ku ce na rabu da matata, saboda ina sonta, na san na yi mata abubuwan da za ta tsane ni, amma bi izininllah zan gyara, wannan sabon zama ne za mu fara, ta saba da ni idan ta auri lusari ba za ta ji daɗin zaman ba".
Baba ya kafe firr a kan ba za a yi sulhu ba sai dai a raba aure, Ustaz kuma yana ta roƙon a yi haƙuri zai gyara, shi ba zai yi saki ba, suka ba mu kwana uku wai ya yi bikona sai mu dawo, Baba ya faɗa musu ai an daɗe ana bikon abun bai yiwu ba, suka ce mu je dai a sake ba mu dama.
Ai kuwa washegari Baba ya saka ni a gaba muka tafi kotu, ya shigar da ƙara, aka kai wa Ustaz takardar sammaci, hankalinsa ya tashi ainun, ya kasa zaune ya kasa tsaye, shi dai ko shaida bai taɓa zuwa kotu ba, a ce yau shi aka kai ƙara? Yanzu fargabarsa ɗaya a yi shari'ar nan wanda ba su san larurar shi ba ma duk su sani, ƙarshe aure ya gagare shi, don haka ya yanke hukuncin ba zai yarda a yi shari'ar nan ba, sai ga shi da daddare ya zo, ya yi sallama da ni na ƙi fita, ya shigo har cikin gidan, Baba dake tsakar gida ya haɗe rai ya ce"Malam lafiya?"
Ustaz ya ce"Don Allah ka ba ni dama na yi magana da Sayyada in sha Allah wannan shi ne maganata da ita ta ƙarshe".
Baba ya ƙwala min kira, na fito gabana yana faɗuwa, ya ce"Ki je ku yi magana, amma kar ki daɗe".
Na ce"To"
Muka fita muka tsaya a zaure, yau jikinsa ya yi sanyi sosai, shiru kamar ba zai ce komai ba, sannan ya ce"Assayyada yanzu da gaske rabuwar kika zaɓa? Na faɗa miki zan gyara wallahi".
Na ce"Ai kuwa ka faÉ—a, kuma ka nuna min alamun gyaran a aikace sanda na je gidanka".
Ya ce"Wallahi wannan tsautsayi ne, son ki da nake yi ne da kewarki ya hana ni jurewa har na far miki, ga shi na tara abun, amma daga baya na yi nadama, in sha Allah ba zan sake kwatanta irin haka ba, ki gwada ba ni dama ta biyu".
Na ce"Ita dama sau É—aya take zuwa a rayuwa, dama can ba sonka nake yi ba, biyayya na yi wa mahaifina, a yanzu kuwa ko dole mahaifina ya yi min wallahi ba zan koma gidanka ba, na gwammace na shiga duniya".
Ya ce"Subhanallah! Allah Ya tsare ki taɓewa Assayyada, tabbas kin nuna min ƙiyayya azeema, amma babu komai ni na yafe miki".
Na ce"Ka faÉ—i abin da ya kawo ka, ni zan koma gida".
Ya ce"Hmm ai zan zo daidai wajen, Assayada na yi iya yi na na gane ba kya son cigaba da zama da ni, na yi duk yadda zan yi domin na shawo kanki kin botsare, rayuwar aure ba za ta yiwu dole ba, tun da zai zama tamkar fyaɗe nake yi miki, sannan wannan kwanciya da kike yi min kamar ruwa yana kona min rai, ga shi kuma dama ba kya gyara jikinki, abu ya buɗe kamar ƙofar gari, ga shi salam, kuma ba kya ba ni wata gudunmawa yayin gabatar da ita wannan sunan mai ɗumbin lada, saboda haka..."
Ya ɗan dakata ya ce"Saboda haka cikin ladabi da girmamawa, tare da tausayawa halin da za ki shiga na rashina, nake cewa ni Ashir na sake ki saki ɗaya rak, domin kin san shi saki an fi so idan ya zama dole ka yi ɗaya, wannan saki ɗaya ƙila zai zame miki wata dama, saboda ko da kin gaji da zawarcin kin kasa samun wanda zai aure ki, za ki iya yin welcome back, bi ma'ana ki tariyo soyayyarmu mu komawa aurenmu, na gode, kuma ni dai na yafe miki, ina fatan ke ma ki yafe min".
Na ji wani sanyi har zuciyata, ana cewa duk macen da aka saki sai ta ji zafi a ranta to ni dai wallahi daÉ—i na ji, na ce"Na yafe maka, Allah Ya yafe mana bakiÉ—aya".
Ya ce"Alhamdulillah, wannan shi ne saki cikin mutunci, ga takardarki nan, sannan ga wannan dubu biyar ce, sai ki ja jari saboda zawarci babu daÉ—i".
Ya miƙo min, na karɓu iya takardar na ce"Na gode, amma ba na buƙatar jari, ka ƙara akan naka jarin, saboda samunka ya fi na da, ka ga za ka iya daurewa bayan auren ka dinga siyan suga na ɗari biyu kai da matar".
Ya ce"To shikenan dai, Allah Ya haÉ—a kowa da rabonsa, amma a shawarce me zai hana ki bari sai kin gama idda a kwashe kayan? Kar a kwashe kuma ki zo kina kewata, an saba abun nan sau uku ko huÉ—u kullum, yanzu an zo babu ko sau É—aya, abun akwai tashin hankali".
Na ce"Hankalinka ne zai tashi, ba zan taɓa jin kewarka ba, saboda wahalar abun ka danɗana min ba daɗinsa ba".
Ya ce"La ba'asa, ala ayyi hall dai ni duk sanda kika ji kina son komawa ƙofa a buɗe take, sai ki taɓo ni, sai dai wannan damar ta wata uku ce kawai, daga lokacin da kika gama idda damar ki ta ƙare, domin ba zan sake biyan sabon sadaki ba kuma a ba ni ɗumame, na gwammace na zaɓi wata cikin masu so na na aura".
Na ce"Ka zaɓa tun yanzu, domin ba zan yi kewarka ba har abada".
Ban jira cewarsa ba na shige cikin gidan, na ƙarasa na ajiyewa Baba takardar na shige ɗakina, ina jiyo su shi da Mama suna ta hamdala.
Washegari da aka je kwashe kaya bai hana ba, aka kwashe tsaf, muka yi shawara da Baba na ce a siyar da su kawai, ina da kuÉ—i da Sadam yake ba ni tun ina gidansa, idan an tashi wani auren sai na cika da kuÉ—in da aka siyar da wannan É—in na yi wasu kayan, don haka aka siyar, aka saka kuÉ—in a account É—ina.