← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 89

Sashe 87

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu kalar gatan da ba ya yi mana ni da yarana, wanda ban ga alamar zai bambanta su ba, sai dai ko a gaba, tun da dai naka naka ne, shekarar ɗana ɗaya na samu wani cikin, sai dai wannan me laulayi ne ba kamar sauran cikina ba, na dinga 'yan cututtuka, don haka dole Hajiya ta san halin da nake ciki tun da wuri, ai kuwa ta kasa ɓoye baƙincikinta, makirci ya dawo sabo, wataran ya dawo daga aiki kawai ta saka shi a gaba da kuka wai na yi mata gorin haihuwa, ita ta gaji ba za ta iya zama da ni ba, ko ya canza min gida ta daina jin gorina ko kuma ya sake ta kawai, sam bai yarda da ita ba, tun da dai yanzu ya gane tana yi min sharri, ya taho ɓangarena ya ce na taso mu je ɓangarenta, ina kwance jiki duk kasala haka na tashi, mun zo wucewa ta window muka ji muryarta tana waya, ya dakata ya kasa kunne, ni ma na tsaya, dariya take yi tana faɗin"Yanzu na sake haɗa su ai, kuma na faɗa masa ko dai ya raba mana gida ko ya sake ni, haba ban taɓa tsanar wani yaro ba a rayuwata kamar wannan ɗan nashi mai ƙaton kai, yanzu wai ta sake samun wani cikin, saboda zalama konika ma za ta yi".

Ta ɗan yi shiru kafin ta ce"Ai idan aka raba gidan zan dai samu sassauci, na daina ganin yaron nan, baƙinciki zai ragu, in sha Allah yaran nan ba za su yi albarka, sai dai a samu taron yuyuyu, duk shekarun da muka yi tare me ya nema ya rasa da zai ƙwallafawa ransa sai ya haihu?"

Ta jinkirta ta ce"A'a Asabe, ba zan iya bin bokaye ba, amma fa da kissa da makirci sai na ga bayanta a gidan nan, sai ta tafi ta bar min yaran da take ɗaga kai saboda su, kuma na yi yadda na so da su, na yi musu kisan mummuƙe, shi ma Isma'il ɗin ai munafuki ne, ba ki ga yadda yake sonta ba".

Ta yi shiru na É—an lokaci kafin ta ce"Ai kuma ba zai yiwu ba, ko sakar min fuska ba ta yi, ba na tunanin zan samu hanyar da zan saka mata magani a lemo har ta sha".

Ta ce"To shikenan, ma yi maganar".

Daga haka ta gama wayar, na kalle shi ba ga yadda yake ta huci alamar ran shi ya ɓaci sosai, na juya na koma ɗakina, shi kuma ya shiga nata ɗakin.

Tana shirin zama a kujera ya shiga, ta ƙaraso tana "Sannunku da zuwa ranku ya daɗe". Za ta rungume shi ya zame ya zauna.

Ta sha jinin jikinta ta zauna ta ce"Ranku ya daɗe me ya faru? Wane ne ya taɓa min ku? Allah Ya huci zuciyarku".

Ya É—aga mata hannu ya ce"Malama ki dakata da wannan pretending É—in haka, zai fi kyau ki kira ni da Isma'il É—ina, wanda ma kike yi wa kallon munafuki wace gulmar ce za ki dinga É—ora min sarautar banza da wofi?"

Sai gabanta ya faÉ—i, ta ce"Ban gane me kuke nufi ba mai martaba".

Ya ce"Kar ki sake ki sake ce min mai martaba daga yau! Na ji komai na san wace ce ke yanzu, na ji abin da yake ranki, na san irin kallon da kike yi min, da kuma mugun fatanki a kan matata da yarana".

Zuwa yanzu ta gane tabbas ya ji wayar da ta gama yi ne, don haka hankalinta ya tashi, ya sakko daga kujerar ta durƙusa a gabansa ta ce"Mai martaba ban fa gane ba, ba ni da wani fata a kanku ku fa yaranku sai na alkhairi, yaranku nawa ne, ko wani tuggun matarku ta haɗa mana?"

A tsawace ya ce"Idan kika sake yi min jam'u ban yafe miki ba, munafukin Isma'il É—in ne abun yi wa jam'u da sunan girmamawa? Na ji duk wayar da kika yi yanzu, kina da sauran musu?"

Sai ta fashe da kuka ta ce"Don Allah ka yi haƙuri ka gafarce ni, wallahi sharrin shaiɗan ne, da wata ƙawata nake waya, kuma ina faɗa ne kawai ba wai haka ne a zuciyata ba".

Ya yi danne-danne a waya ya kunna mata recording ɗin nan, ta gama saurara jikinta har rawa yake yi, ta ce"Don Allah ku yi haƙuri".

Ya ce"Lokacin da na samu recording ɗin nan na yi miki uzuri ban ce miki komai ba, amma yanzu tun da har ƙiyayyar taki ta tsallake kan kishiyarki ta hau kan yarana dole zan magantu, Halima ba ki yi min adalci ba, ba ki yi min kara ba, duk yadda nake zaune da ke da zuciya ɗaya? Duk halaccin da na yi miki da tarin alfarma ashe a mara adalci kike kallona? Ke kika nuna kina sona, ke kika nace sai da na fara sonki har na aure ki, muna tare wannan larura ta same ki har ta kai ga an cire mahaifar babu halin haihuwa, a tunanina adalcin da zan yi miki shi ne na zauna da ke da kyautatawa da soyayya kamar yadda muke a da, sannan kar na juya miki don na yi aure matar ta haihuwa, iya yina na yi ƙoƙarin yin hakan, amma ke ma a tunanina za ki yi min adalci ai, a zatona da kanki za ki ba ni shawarar na ƙara aure, tun da dai ina da lafiyar da zan haihu kuma ina da halin riƙe wata matar bai kyautu na zauna na ce ba zan yi aure na samu zuri'a ba".

Ta ce"Don Allah ka yi haƙuri, na san ban kyauta ba".

Ya ce"Ai ba maganar hakuri ba ce, Halima 'yan'una duk irin yadda suke nuna ba sa sonki abun ciwo yake yi min, sun sha zuwa su ce kin yi musu abu kaza, ki saka ni a gaba da kuka ki ce ba ki yi ba, kuma na yarda da ke, idan kin je sabgarsu kullum sai kin ce sun yi miki wani abun, ƙarshe ma saboda ba na so a ci zarafin matata na hana ki shiga jikinsu, na raba alaƙarku, mahaifiyata ce fa Halima? Idan kina da kara da adalci za ki daina zuwa gaishe ta ɗin? Kina kallo za ta yi jinya amma ba za ki je ba, abun fa ba ya yi min daɗi, na yi auren nan kika nuna kin karɓi yarinyar nan hannu biyu-biyu, kike nuna ita ce fitinanniya ba ta so a zauna lafiya, ki ce ta yi miki rashin kunya, ta ci zarafinki ta yi miki gorin haihuwa, ashe duka ƙarya kike yi, burinki kawai ki haɗa ni da matata, to ai kuwa kin ɗauki alhakinta, idan ba ta yafe miki ba sai an yi muku hisabi, ni ma kuma faɗan da kika dinga sakawa ina yi mata ki sani kin ɗauki alhakina, domin ta daɗe tana yi min kallon mara adalci".

Cikin kuka ta ce"Ku yi haƙuri don Allah, ku yafe min, na canza in sha Allah ba zan sake irin haka ba, kishinku ne ya ja komai".

Ya ce"Haba Halima, ki yi min adalci mana, mene ne ba na yi miki? Kishin kuma har da yarana za ki yi? Ai kuwa duk maso uwa ya so 'ya'yanta, inda da gaske kina sona tsakaninki da Allah ba za ki ƙi ɗana ba, har kina aibata shi da ce masa mai ƙaton kai, sannan wane magani ne ake ba ki shawarar ki zubawa matata? Na mutuwa ne kenan ta tafi ta bar ki sannan su ma yaran a hankali ki ga bayansu ko?"

Ta ruɗe ta fara girgiza kai alamar a'a, ta ce"Wallahi ba kashe kowa zan yi ba, na zubar da ciki ne, kuma dama ba yi zan ba, don Allah ki yi haƙuri, na yi nadama".

Ya ce"Nadama mara amfani, tun da ba ki yi domin Allah, don haka ban yarda da nadamarki ba".

Ta riƙe ƙafar shi tana gursheƙen kuka ta ce"Na san ban yi maka adalci ba, don Allah ka yi haƙuri, ka yanke min hukuncin da zan iya ɗauka, kai ne duniyata ba zan iya rayuwar aure da waninka ba, ban kyauta ba, ka zauna da ni da zuciya ɗaya na sani ka yi min komai, shaiɗan ne ya rinjaye ni, ka yafe ni".

Ya ce"Ki shirya gobe za ki je ƙasarku".

Ya tashi zai fita, ta riƙe shi gam tana kuka sosai ta ce"Don Allah ka yi haƙuri, ka rufa min asiri, idan ka sake ni ban san wanda zan aura na rayu cikin salama ba, kun uwansa ba za su ɗauki goron haihuwa ba, na san idan shi bai yi min ba danginsa za su yi min ko kishiyoyi".

Ya ce"Ai gorin kike nema tun da dai har kike ƙaryar an yi miki, ki shirya dole gobe za ki bar gidan nan, ba sakinki na yi ba, amma ki je na daina ganinki na kwana biyu, duk lokacin da na huce na faɗa miki ki dawo".

Bai sake sauraronta ba ya fice daga ɗakin, ya shiga ɓangaren Sayyada, ya shiga ɗakinsa ya kulle, da ta buga masa ma ya ce ta rabu da shi yana buƙatar kaɗaici.

Washegari duk magiyar da Hajiya Halima ta dinga yi masa ya ƙi ji ya ce sai ta tafi gida, da ta matsa ya ce to zai sake ta idan har ta ƙara yin musu da shi, a dole ta haƙura ta tafi ɗin.

Ni dai ban yi masa maganarta ba, shi ma kuma bai yi min ba, jikinsa a sanyaye yake har kwana biyu, daga nan kuma ya warware muka cigaba da rayuwarmu hankali kwance, duk da laulayin nan haka nake ƙarfafar jikina ina kyautata masa, ina yin duk wani ƙoƙari don ganin na cike masa duk wani gurbin matar shi, saboda kar ma ya ji kewarta, ni duk a zatona sakinta ya yi, kuma har zuciyata ba na so ta dawo gidan, domin yanzu da ba ta nan rayuwar gidan ta fi yi min daɗi, kullum ina da miji a kusa da ni, kullum ya zo ɗakina zai shiga, da ni kaɗai zai yi fira da dai sauransu, lallai kishiya ba ta da daɗi, indai irin Hajiya Halima ce, sai idan ta zama dole ne babu yadda za ka yi.
[21/11, 9:14 am] Sadiya Abdulrazak: USTAZ ANGON RUKY
Chapter 87 · 0% Book details