Sashe 3
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ya isa haka!" Ya daka min tsawa, sannan ya dora da faɗin"Duk wannan shirmen da kike yi ba zai hana ni bin umarnin mahaifiyata na yi aure ba, ko ki mutu ko ki rayu zan yi aure, don haka kina da zaɓi, ko ki kwantar da hankalinki ki cigaba da bin uamarnina mu zauna lafiya, ko kuma ki tada hankalinki ki yi ta shiga ƙunci da damuwa, kina kallo kuma ni zan samu kwanciyar hankali da matata".
Ina kuka na ce"Ba zan yi maka biyayya ba, ba zan sake bin umarninka ba, kuma ba zan sake kwana a gidanka ba matuƙar ka auri wata, sai dai ka sake ni wallahi, ai ba kai kaɗai ba ne namiji".
Wannan karon dariyar rainin hankali ya yi ya ce"Ba ni kaɗai ba ne namiji, amma ni kaɗai ne namijin da za ki rayu da shi har abada, ke da zaman aure da wani sai a lahira idan ana yi, kuma aurena da ke ki saka a ranki takalmin kaza ne, mutuwa ce kaɗai za ta rabu, don haka nan gaba idan kin tashi azabtar da kanki a wuyanki za ki saka wuƙar ba hannu ba, shashasha!".
Ya tashi yana harara ta ya ce"Kar ki sake ki kira wani ki ce za ki yi kuskuren sanar da shi, zan nemo wacce za ta kula da ke, saboda ba zan iya kwana a asibiti ba".
Na ce"Ba na buƙatar taimakon kowa, kuma ka kawo min wayata!".
Ya fita ba tare da ya sake ce mini komai ba.
Gida ya koma ya yi wanka, yana fitowa ya shirya ya nemi waje ya zauna ya riƙe kansa, bai taɓa tunanin ƙarfin zuciyar Sayyada ya kai ta aikata haka ba, ana wannan halin kiran Safna ya sake shigowa wayarsa, ya ɗauka a sanyaye yana faɗin"Baby".
Ta ce"Beb lafiya ba ka ƙaraso ba?"
Ya ce"Sorry ba zan samu zuwa, a halin yanzu ba na cikin nutsuwata ma wallahi".
Ta ce"Subhanallah! Mene ne ya faru?"
Ya yi guntun tsaki ya ce"Wannan mahaukaciyar yarinyar ce ta yanka jikinta".
Gabanta ya faÉ—i ta ce"Ban gane ba, yankewa ta yi ba ta sani ba?"
Ya ce"Ba na faÉ—a miki ta takura min sai ta haihu ba?"
Ta ce"E ka sha faÉ—a min".
Ya ce"To shi ne da na hana ta fita yau ta ɗauki wuƙa ta yanka hannun za ta cire".
Safna a ranta ta ce'Matsiyaciya dama ta mutu, na huta'
A fili kuwa sai ta nuna alamar damuwa, ta ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Amma dai yankan bai shiga sosai ba ko? Yanzu tana ina, na zo na duba ta?"
Ya ce"Ki kwantar da hankalinki ai ba abar tausayi ba ce, a kanta aka fara kishi?"
Ta ce"A'a bai kamata fa ka ce haka ba, ka san kowace mace da kalar nata tunanin wajen kishi, ka yi mata uzuri, ni wallahi tausayi take ba ni ma, yanzu kuna asibiti?"
Ya ce"Na dawo gida, ba ta isa ta saka ni kwanan asibiti saboda haukanta ba, tunanin wacce zan nema ta kwana da ita nake".
Da sauri ta ce"I can! Ba sai ka nemo kowa ba ni zan zo na kwana da ita".
Ya ce"A'a Safna, kar ki takura kanki, kuma kin san idan ta gane ke ce ba za ta ji daÉ—i ba".
Ta marairaice ta ce"Na yi maka alƙawarin ba za ta gane ba, wallahi ba zan nuna mata komai ba, ko dai ba ka yarda da ni ba ne Beb?"
Ya sauke numfashi ya ce"Wallahi na yarda da ke, kawai dai na yi mamaki, na yi zaton kishi ba zai bari ki je ba".
Ta ce"Wallahi tamkar yadda zan zauna da ƙanwata uwa ɗaya uba ɗaya haka zan zauna da Anti Sayyada".
Ya ce"Na gode sosai my wife to be, amma a gida za a bar ki?"
Ta ce"Duk da dai yau ba dutyn dare gare ni ba, amma zan ce zan karɓawa ƙawata saboda ɗanta ba shi da lafiya, za a iya barina".
Ya ce"Wow! To bari na zo na É—auke ki ko?"
Ta ce"A'a, kar ka zo za a zargi wani abun, bari na zo kawai gidan sai ka kai ni".
Ya ce"Za ki taho min da abincina da kika yi min? Yunwa nake ji".
Ta ɗan yi shiru na sakanni kafin ta ce"A'a ba zai yiwu na taho maka da shi ba, za a zargi wani abun, ka ga an san kai na yi wa girkin, kuma yau ba ni da aikin dare, idan na yi ƙaryar zan karɓawa wata an yarda, ba za a yarda da ni ba idan na ɗauki abincinka".
Ya ce"Good! Kina da tunani".
Ta ce"Amma dai idan na zo zan dafa maka".
Ya ce"Na gode sosai ina jiranki a bakin titi".
Suka ajiye waya, yana sauke ajiyar zuciya.
Sannan ya tashi ya fita da mota, bayan ya ɗakko ta a hanya tana ta nuna jimaminta, kamar ta fi shi son Sayyada, da suka ƙarasa gidan ita ta gyara wajen da jinin ya ɓata, sannan ta shiga kitchen ta ɗora masa macaroni jollof, a falo ya zauna yana ta danne zuciyarsa, da kuma shaiɗan ɗin da yake ta ƙissima masa ya gwada sa'arsa a kan Safna, ta taimake shi ko da romance ne, lokaci ɗaya fitinanniyar sha'awa ta taso masa, duk da Safna ko hijjabi ba ta cire ba.
[21/09, 5:00 pm] Sadiya Abdulrazak: *KU YI MANA ADALCI*
NA
Sadiya Abdulrazak
Page 3
3
Allah Ya sa aurenta yake son yi, duk da mutum ba ya hana kan shi jin sha'awar wanda ya yi masa, amma a yanzu dai ba irin yanayin baya yake ji ba, ji yake kamar ya gwada ta ko za ta amince ko sumbatarta ne ya yi, wata zuciyar tana hana shi, tunawa da yadda daren farkonsu da Sayyada ya kasance, ya ci wa daren buri sosai, amma ƙarshe sai ga shi ya zo masa a baibai, a ranar ko sha'awarta bai ji ba, haka suka kwana ƙalau ba wani abu da ya shiga tsakaninsu, haka aka kasance babu wani marmari da shauƙin juna, to gaskiya yana son yin ƙara'i a wannan sabon auren da zai yi, don haka ya daure ya dinga yaƙi da shaiɗan har ya samu ya fi ƙarfin zuciyarsa bai nunawa Safna komai ba, a baki ta dinga ba shi abincin, kuma har vedio ta yi masa, dama ta yi wasu a kitchen, bayan ya gama ci ta ce ya ɗakkowa Sayyada wasu kayan ko za ta yi wanka, ya ɗakko suka tafi, da abincin da kuma ruwan zafi.
A hanya yake cewa"Allah Ya sa dai kar ta gane, don Allah ki yi iya yinki don ganin kin kaucewa yadda za ta sanki, tukuna ma me za mu ce mata? Ke wace ce?"
Ta ce"Sai mu ce ni 'yar'uwarka ce, na zo zan kwana biyu, kuma za ka iya sirri da ni shi ne ka ce wa Momy na zo gidanka na kwana biyu kafin na tafi".
Ya ce"Kai na gode Allah, da ya ba ni mace mai basira, i love You".
Ta yi murmushi ta ce"Ai ka cancanci hakan ne Love".
Lokacin da suka ƙarasa ɗakin bacci take yi, suka tsaya suna kallonta tana ta bacci, ya taɓe baki ya ce"Kin dai ganta, ga shirmen da ta yi abin da ya ja mata".
Safna ta ce"Allah sarki, Allah Ya ba ta lafiya, kai ma kuma bai kamata ka kafe a kan ba za ta cire tsinken ba, yanzu ga shi ta cutar da kanta".
Ya ce"Share ta".
Ya fita ya siyo kayan shayi, biredi, kaza da fruit, ya kawo ya ce idan ta tashi sai ta saka ta ci abincin, suka zauna suna ta fira, yana tambayarta anya za ta iya kwana kuwa, dariya kawai ta yi ta ce ni da na saba kwanan asibiti, babu komai ka je kawai".
Ya ce"To na gode sosai Baby, ku kwana lafiya".
Ya fita yana waiwayenta yana murmushi, a ransa kuwa daÉ—i yake ji sosai, don ya fara hango yadda gidansa zai wanzu da zaman lafiya idan ya aure ta.
Bayan fitarsa ta bi Sayyada da kallon wulaƙanci, wayarta da ya ba ta ta ajiye mata ta ɗakko, a hakanli ta ɗago yatsan Sayyadar ta ɗora a wayar key ɗin ya fita, ta sauke ajiyar zuciya ta matsa gefe, lambarta ta fara ɗauka, sannan ta shiga cikin wayar ta fara bincike, ba ta ga komai na rashin gaskiya ba, don haka ta ajiye mata, sai ta dubo lambar tata a whatsApp ta tura mata vedion Sadam wanda take ba shi abinci a baki, da kuma wanda take yin girki a kitchen, ta tura mata shi amma ta once, yadda idan ta kalla sau ɗaya shikenan ba za ta sake kalla ba, ta haɗa da rubutu a ƙasan ta ce"Ya kamata ki gane miji irin naki ba wanda za ki nasaka kanki a kansa ba ne, kin dai gani kina asibiti shi kuma yana tare da wata, cewa ya yi ya ji daɗin baki gado da aka yi ma, sannan ba zai iya kwana da ke ba, yanzu haka yana can tare da wata, ta yi masa girki kuma za ta kwana a gadonsa, ban faɗa miki don ki tada hankalinki ba, sai don ki nutsu ki gane da wa kike tare, mijin ƙaton mane min mata ne".
Tana ta kallo a wayarta, don ta kunna data ba ta ga Sadam online ba, dama ya ce mata da wuri zai yi bacci, har ta gama ta yi bacci, Sayyada ba ta tashi ba, ita ma ta kwanta a sallaya ta lulluɓa da hijjabinta, bayan ta zare layin da ta tura mata saƙon da shi daga cikin waya, ta fara baccinta hankali kwance.
SAYYADA