Sashe 83
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai kuwa ta ɓata rai, ta tashi ta haye cinyarsa, ya ce"Subhanallah, Rauda jirana take yi fa kar abun ya zama cin fuska, bari na je kin ji, haƙurin na kwana uku ne kawai".
Ta narke a jikinsa ya ƙi ba shi damar tafiya, jin ya amsa sallamar da take yi ya sa ta buɗe ƙofar ta shigo, ta same su a wannan yanayi, ranta ya ɓaci, amma ta daure ta ce"Sannunku da aiki, baiwar Allah mun wuni lafiya?"
Rauda da take ta kallonta tana taɓe baki ta ce"Lafiya ƙalau".
A ranta tana mamakin ashe ma babba ce matar tashi, wata mara aji ma, har take kishi a kanta da tunanin kar ta ƙwace mata miji, yanzu wannan ai ba ta hango ta inda za ta ƙwace mata shi ba.
Rakiya ta ce"Malam ina ta jiranka ne dama, na ji shirun ya yi yawa".
Ustaz ya ce"To Rauda bari na je sai da safe".
Rauda ta narke a jikinsa kamar ba ta ji me ya ce ba, Rakiya ta ce"Don Allah ka taso mu tafi, kai fa malami ne, ka san bai dace ka dinga kwaso ranar kwanana kana kai mata ba, ka ji tsoron Allah".
Ustaz ya sauke Rauda daga jikinsa, ya tashi, Rakiya ta ce"Ke kuma kin ci bashi wallahi" Ta kama hannun Ustaz suka tafi.
Suna shiga ɗaki ta saka sakata, ta yaye hijjabin jikinta, gabansa ya faɗi ya ce"Subhanallah, haba Ruƙayya mene ne haka? Shin ba kya gudun shaiɗanu?"
Ta ce"Na yi azkar dai, ni dai mu je don Allah".
Sai ya koma da baya, yana haÉ—e gira ya ce"Ke wai me kika mayar da ni ne? Bi ma'ana me kika É—auki aure? To ki sani fa ba iya kashe arna ba ne aure akwai fira, akwai kula da juna, yanzu da na dawo sai ki tambaye ni ya aiki? Ya na dawo? Sannan ki kawo min abinci a kai min ruwan wanka da dai sauran abubuwa, kuma bari ki ji na faÉ—a miki gaskiya, ni idan kina farmakata irin haka zan raina ajinki, ki dinga bari sai na neme ki".
Ta ce"To zan yi ƙoƙarin hakan in sha Allah".
Ya ce"Yawwa, sannan ni fa ina yin sallar dare, kuma ba zai yiwu a hana ni bacci ba".
Ta ce"A'a ta nan dai ka rufa min asiri don Allah".
Ya ce"Na rufa miki ni na tona nawa? Kenan na kwana ina yi miki hidima ban runtsa ba na tabbata asararre, to asara mana, kin ga dai na É—aya ban ribaci lahirata ba, ban yi sallah ba, na biyu kuma zan rasa duniya, tun da zan dinga gyangyaÉ—i a wajen aiki, ke kuwa da rana za ki sha baccinki, don haka ba zai yiwu ba, dole a yi jadawali a fitar min da hakkina, a ba ni lokacin bacci da ibada".
Ta ce"To ka fitar da kanka".
Ya ce"Ma sha Allah! Kin ga yanzu dai lokacinki ne, zan kasance da ke daga yanzu takwas da rabi zuwa sha É—aya da rabi..."
"Wallahi ya min kaÉ—an" Ta katse shi da faÉ—in haka, tana yin kicin-kicin da fuska.
Ya ce"To ni dai iya haka zan iya, tun da da safe ma za a yi abun nan, ai ba zai yiwu na daina ibada saboda ke ba".
Ta ce"Na ji, amma gaskiya da na san kai rago ne tun farko da ban aure la ba wallahi".
Ya ce"Alhamdulillah an zo daidai wajen, to ai ni ma da na san jarabarki ta kai ko ibada ki hana da ban aure ki ba wallahi, yanzu ma idan kin ga ba za ki iya ba sai ki yi bayani na sallame ki cikin amince, bi ma'ana na sake ki, ki je ki nemi wanda ya fi ni".
Sarai ta san Ustaz ya yi ƙoƙari, ita duk auren da take yi ma ba ta ga wanda ya kai shi jarumta ba, tana yi masa gorin ne kawai don ya yi zuciya ya ƙara ƙaimi, amma babu batun rabuwa, ai ba hauka take yi ba, ita kam yanzu ta ga mijin zama, don haka zama daram".
Ta ce"Ka yi haƙuri, yanzu dai ni a uzurce nake".
Ta janyo shi ta fara rana shi da kayan jikinsa, ransa duk a ɓace yana jin kamar ma raini ne wannan, sai kace ita ce mijin shi ne matar? Haka aka shiga yaƙin nan, awa uku ana abu ɗaya, Ustaz bacci ya fara fizgar shi, ya ce"Ruƙayya ya ake ciki? Ni dai bacci nake ji, kin san na faɗa miki ba zai yiwu kina hana ni sallah ba".
Ta sake ƙanƙame shi ta ce"Ka rufa min asiri Malam, wallahi da saurana, inda jiya ka yi haƙuri mun kwana ƙila yanzu idan aka lissafa da na jiyan sai na gamsu, yanzu hau ka haƙura mu kwana cirr, in sha Allah idan ka yi min na safe shikenan gobe da daddare na yafe maka sai dai ka yi min na awa biyu sai mu yi baccinmu".
Ustaz ya ce"Wallahi ba zan kwana ina yi ba, ai ni ba jaki ba ne".
Ta ce"Kenan nufinka ni jala ce?"
Ya ce"A'a dai ban ce ba, amma wallahi bacci zan yi, a to ba zai yiwu ba".
Ya matsa gefe ya juya mata baya, ta ce"Amma dai da asuba za ka ƙarasa".
Ya ce"Allah Ya kaimu".
Ya tashi ya yi wanka, ya kwanta, bacci mai nauyi ya É—auke shi, a cikin baccin yana ji tana ta shafa shi, tsoro duk ya kama shi a ransa ya ce'Wannan dai an yi mayya'. Ya yi kamar bai ji ta ba, shi dai ya fi tunanin ba ta yi bacci ba, don duk farkawar da zai yi sai ya ji hannunta a jikinsa.
Ya tashi ya yi sallar dare, zai koma bacci ta ce ya taimaka ya yi yanzu, ya ce sai dai idan za ta yafe na asuba, ta ce ta yarda, ya cigaba da yi har asuba, amma da safe ta hana shi fita sai da ya sake yi, ya matsu ya bar ɗakinta ko ya huta, da daddare da ya dawo sai ya shigo mata da karkarwar ƙarya, ya haye katifa yana faɗin"Ruƙayya ban bargo ko zanin gado don Allah".
Ya kwanta ya duƙunƙune yana ta girgiza jikinsa, wai karkarwa yake yi.
Ta ce"Subhanallah, ba ka da lafiya ne?"
Ya ce"Wallahi kuwa, zazzaɓi ne ya rufe ni, kuma na san rashin bacci ne wallahi, dama haka nake idan ba na samun cikakken bacci, wayyo Allah sanyi nake ji".
Hankalinta ya tashi, ba wai damuwa ta yi da zazzabin ba, a'a fargabarta ɗaya ya ce ba zai yi mata komai ba saboda ba shi da lafiya, ta ɗakko zanin gado ta lulleɓe shi tana yi masa sannu, a gida ya yi sallar magriba da isha'i saboda ta yarda da gaske ba shi da lafiya, domin ya duba ya ga indai yau ya biye mata ta jigata shi tsotse komai za ta yi, gobe idan zai koma ɗakin Rauda ya rasa abin da zai kai mata, don ita ma tsaf ya gane a uzurcen take da lamarin, haka dai Rakiya ta haƙura a ranar, amma kwana ta yi tana shafa shi.
Washegari da ya shiga É—akin Rauda don yi mata sallamar tafiya kasuwa, ta ce ba ta san zance ba, ai tun da kwananta ya shiga to sai ya ba ta hakkinta, haka ya amince don ya yi adalci, ai kuwa ba ta bari ya bar gidan ba sai wajen sha É—aya.
Da daddare sai ya yi mata na awa biyu ya ce to a yi bacci haka, ta ce sam ita bai ishe ta ba, dayake ita ma ta go shaye-shayen maganinta, saboda tunanin ya yi mata kishiya kar ya fi jin daɗi a can, da ƙyar Ustaz ya samu kansa dab da asuba, ya jigata ko sallar dare bai yi ba, da ya ga take-takenta da safe so take ya ƙara sai kuwa ya yi farat ya ce ai an shiga kwanan Ruƙayya domin shi kwana ɗaya-ɗaya zai dinga yi ba biyu ba, da sauri ma ya fice daga ɗakin, yana shiga ɗakin Rakiya ya tarar za ta shiga wanka, ta yi masa sannu da zuwa, ya ce"Yawwa, dama ban yi muku bayanin kwana ba, gaskiya kwana ɗaiɗai na raba, ta ce"Kana nufin yanzu kwanana ya shiga kenan?"
Ya ce"E".
Ta washe baki ta ce"Alhamdulillah, dama jiya kwana na yi da kewarka wallahi, ta jefar da zanin tana cewa ka ga kawai na haÉ—a na yi wankan idan an gama".
Ya ce"Subhanallah na faɗo hannun 'yan sari, Ya Allah kai ne ka ƙaddara wanzuwata a tsakanin harijai biyu, sannan ka ba ni ƙarfi irin na hariji ɗaya, Allah Ka taimake ni ka yayewa matana wannan larura ko da ita Ruƙayya ce".
SAYYADA
Da alama dai cewa da ya yi da ƙyar zan shawo kansa iya fatar baki ne, domin kuwa ana gobe zan koma ɗin da daddare ya kira ni muka daɗe muna yin waya, har na kasa haƙuri na ce"Mai martaba wai ina matarku wacce take sonku?"
Ya ce"Au ke ba kya sona ko?"
Na ce"Ni wai me yasa ka daina yi min jam'u?"
Ya ce"Ai na ga kin fara raina ni, nema kike ki mayar da ni abun wasanki, na daina yi miki magana da jam'u, amma ke kuma dole ki yi min jam'u matuƙar kina so mu shirya".
Na ce"Ai yanzu na fara yi ranku ya daÉ—e, kuskuren baya ma a yafe min tuba nake".
Ya yi yar dariya ya ce"Sayyada kina sona?"
Na ce"Ni ma ban sani ba".
Ya ce"To shikenan, tun da dai ke ba za ki daina wannan yangar ba, sai kin sakko sai kuma ki hau, amma dai na san kina nan kina kewata, ni kuwa ba ruwana da kewar wata tun da ga matata nan kodayaushe a kusa da ni, tana yi min duk yadda nake so".
Kishi ya kama ni, na ce"Dama ai ban ce ka yi kewata ba, kamar yadda ni ma ban yi kewarka ba".
Ya ce"Idan kika cika baki fa sai na bar ki sai wani satin za ki dawo".
Na ce"Don Allah a bar shi É—in, ni dama ba matsuwa na yi ba ai".
Ya ce"Kuma kika nema? Ke fa kika ce za ki dawo".