← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 89

Sashe 33

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko kallon inda yake ban yi ba, ya koma, na yi zaton ma zuciya ya yi, sai ga mutum ya dawo ya shigo falon, zirr haihuwar uwarsa, gabana ya faɗi amma ban nuna ba, ya ƙaraso ya ɗauke ni cak ya kai can ɗakin gadon, ya yi yadda yake so, gani nake yau har da mugunta yake yi, baƙinciki kamar zuciyata za ta yi bindiga, ga yunwa da nake ji, ban san adadin lokacin da muka ɗauka a haka ba, ni dai ban so na dakatar da shi ba, na so ya kwana yana yi, ni ban san ma daɗin me yake ji ba a kiɗa da rawar da yake yi shi kaɗai, ban da ranar farko da nake ɗan jin shaukin abun da kuma son na kyautatawa mijina da na taya shi na ba da tawa gudunmawar don sama masa nutsuwa, wallahi duk sauran lokacin kwanciya nake kamar ruwa, amma na ga hakan ba ya damunsa ma, tun da dai bai taɓa ƙorafi ba. Ganin numfashina yana neman ɗaukewa kamar zan mutu ya sa ni fashewa da kuka ina ture shi, bai yi musu ba ya rabu da ni yana jero hamdala, sai da ya fito daga wanka sannan na tashi na fita daga ɗakin, jiri na ji yana kwasata kamar zan faɗi, ƙafafuna suka fara rawa kamar an kunna wata na'ura, tun da can ba ni da juriyar yunwa, don haka na gane ita ce ke neman kai ni ƙasa, har wani duhu nake gani, a haka na ƙarasa kitchen, na ci karo da kayan shayin da ya siyo na karyawar gobe, na taɓa fulas na ji akwai ruwan shayi, na kuwa juye shi a kofi, na zazzage shegiyar madarar guda ɗay wacce nake jin da ita gara babu, na juye sugan, na kaɗa na kafa kai, sai da na sha rabin kofin sannan na ajiye, na ɗauki biredin na matse shi don ya fi danƙo, na dinga ci ina korawa na cinye shi tass, na ajiye kofin na dafe kaina na fashe da kuka, Allah ne shaidata na gaji da auren nan, amma wane ne zai fahimce ni? Na bawa kaina amsa da faɗin babu, babu wanda zai gane ya cece ni sai bayan raina, amma ina fatan ko bayan raina a gene ga baƙincin da ya kashe ni, domin ya zama izina ga iyayen da ba sa bincike a kan matsalar gidan auren 'ya'yansu, Kodayake ni ce na yi wa kaina lambar da dole Baba ba zai sake yarda da ni ba, shi yasa duk runtsi ake so ka yi ƙoƙari a sanka a mutumin kirki, ko a gaba ka kuskure za a ce ƙaddara ce ko tsautsayi, ni kam na zubar da wannan damar.

Banɗaki na shiga don yin wanka, sai na ga jini kaɗan ya biyo bayan fitsari, gabana ya faɗi na fara jin tsoron kar wani abu ya samu cikina, haka na yi wanka jikina har yanzu bai daina karkarwa ba, falo na koma na kwanta, na daɗe kafin bacci ya ɗauke ni, cikin baccin na farka da ciwon mara amma bai yi tsanani ba, na ji fitsari na je na yi na sake ganin jini kaɗan, na koma na kwanta, na daɗe ban koma bacci ba, ina tunanin gobe dole zan je asibiti, da kuma ta yadda zan faɗa masa zan je ɗin, saboda ba ni da kuɗi kwata-kwata, babu komai a cikin account ɗina, wannan tunanin da fargaba shi ya ɗauke ni tsayin lokaci, ina jin lokacin da ya fito ya yi alwala hakan ya tabbatar ƙarfe uku ta yi, ban dai samu bacci ba sai bayan an yi kiran sallar asuba na farko, sai a lokacin bacci ya ɗauke ni, ban sani ba ko ya tashe ni sallar asuba, ko ya tashe ni ni dai ban ji ba, don bacci ya yi min nauyi, jin mutum a jikina ne ya farkar da ni, na kalle shi cikin duhun asubar, babu kaya a cikinsa, na lura daga jiya zuwa yau ya ƙaro wulaƙanci, to ban da wulaƙanci a kan me zai dinga yin tsirara yana ƙara tsorata ni?Ƙoƙarin fizgewa nake yi don na tashi, na tuna ban yi sallar asuba ba, amma ya riƙe ni gam, ya ɗauke ni zuwa ɗakin gado, baƙinciki na kasa cewa komai, har ya sada ni da gadon ya fara yin yadda ya so, yau tsananin azaba da na dinga ji ta fi ta koyaushe, marata ta dinga ciwo, ina ture shi ya ƙi turuwa, cikin kuka na ce"Ka rabu da ni sallah zan yi, idan na yi sai na dawo ka kashe ni, dama ai ka gama kashe min rayuwa, ka kashe ni a matsayin mace, ina tafe ne gawa, ka rabu da ni".

Kamar wanda ake zugawa ya ki saurarata, sai da na ce"Allah Kana kallo, Allah kai ne adalin sarki, Ka É—ora alhakin sallar da ban yi ba a kan wannan azzalumin bawan naka".

Kalamaina sun yi tasiri a kansa, don haka ya rabu da ni, yana cewa"Haƙiƙa ban yi dacen matar aure ba, Allah Ya sani Assayyada kina cutar da ni, Ya Allah na yafewa matata Assayyada, kar ka kama ta da laifin hana ni hakkina na wannan lokacin".

Ban bi ta kan shi ba, na tashi kafaɗa tana harɗewa na bar ɗakin, marata a ƙulle, na yi banɗaki, ina tsugunnawa jini ya fara zuba, a yanzu kam na saddaƙar cikin jikina da nake matuƙar so yana cikin haɗarin barin muhallinsa, haka na yi wankan jikina duk babu ƙwari, na fito na yi sallah a zaune, na ɓingire a sallayar ina ta kuka.

Can da gari ya yi haske, ina nan a sallayar ina murƙususun ciwon mara, ya shigo ɗakin kamar an jefo shi, ya ce"Subhanallah! Assayyada".

Na yi zaton ganin halin da nake ciki ne ya saka shi yin subhanallah, sai ji na yi ya ce"Assayyada, ina abun karyawata? Kar dai ki ce min kin dafa shayin kin juye suga har na naira É—ari kin shanye, sannan na ga ledar biredi, me hakan yake nufi?"

Na yi banza da shi, ya ce"Wato ba lura akwai raini azeem da ya shiga tsakanina da ke a 'yan kwanakin nan, shin me kike nufi ne?"

Nan ma dai ban kula shi ba, ya ce"Kaico! Kaiconki Sayyada, tirr da macen da take wofantar da mijinta, hakika ina jiye miki azabar Allah, don haka na yafe miki, komai za ki yi ki je ki yi, sai dai ki sani ni ba bawanki ba ne da zan dinga yi miki girki da sauran hidimomin gida, daga yau na janye duk wani tallafi a gareki hakkina kuma dole ki ba ni, ba zan san kina cikin damuwa da baƙinciki ba ai sai kin mutu, har ni mace za ta dinga yi wa wannan raini azeemi? Da kin san matan da suke bi na da kalmar so, da burin na aure su wallahi da tuni kin shiga hankalinki, da kin gane ni'imar da Allah ya yi miki, ki je ki tambaya mata da yawa suna can a gidajen aure cikin wani hali, saboda sun auri lusaran maza masu sharɓar bacci cikin dare, inda su ne suka samu mai wannan ni'ima irin tawa da har goya ni za su dinga yi, amma shikenan, idan ba ki godewa ni'imar Allah ba gaba za ki godewa azabarsa, zan fita, wannan ɗari biyu da hamsin ɗib da na umarce ki ki siyo kayan miya kika ƙi, yau sai ki siyo da ita, idan ba haka ba kuma ki zauna da yunwa".

Ya fice daga ɗakin, ina jin fitarsa daga gidan, so nake yi na yi kuka amma ya ƙi zuwa, sai azabar ƙunci da yake rugurguzar zuciyata. Bai daɗe da fita ba jini ya ɓalle min sosai, azabar ciwon mara ta ƙaru, na dinga juyi ina kiran Allah, da tuba a gare shi, sarai na san cikin jikina ne ya lalace yake neman hanyar fita, wata zuciyar tana faɗa min na kunna wayata na kira shi, ko na kira Mama, wata zuciyar kuma tana tuna min wace ce ni a yanzu, ni ba kowa ba ce face mara 'yancin da aka aure ni saboda na zama baiwar da za a dinga kwanciya da ni babu dare babu rana, mene ne amfanin rayuwata? Gara na mutu kawai na huta, har kalmar shahada na dinga karantowa, amma ita mutuwa lokaci ne, kuma lokacina bai yi ba, a hankali na fara jin sassaucin ciwon, sakamakon fitowar halittar gabaɗaya, na kalli yadda na yi kaca-kaca a cikin jini, haka na tashi jiki babu ƙwari na gyara jikina, sannan na gyara wajen, a yadda nake jin kaina dai kamar babu komai a cikina, amma ina tuna wata ƙawata da ta ce ta yi ɓarin ciki a gida ba ta je asibiti ba, ashe bai gama zubewa duka ba, silar haka daga baya ta samu matsala sosai, kamar za ta mutu, don haka na ji tsoron, na ga dacewar zuwa asibiti, Mama ya kamata na kira na sanarwa, amma idan na kira ta tamkar a kunnen Baba na faɗa, ni kuma ba na so Baba ya sake jin wani ƙorafi daga gare ni, gara kawai ya ga gawata, don haka na fara tunanin kiran Anisa, wata zuciyar ta ce min ai daɗi za ta ji, tun da ba ta farin ciki da rufin asirinki, take na fasa, na ɗauki wayata na kunna, na san san babu komai a account ɗina, sai ko naira ɗari huɗu idan ban manta ba, amma haka dai na duba kuɗin ciki, kwatsam sai na ga ina da kuɗi a ciki har kimanin dubu ɗari shida, gabana ya ba da rass, ni kuɗu mai yawan wannan bai ma taɓa shiga account ɗina ba, to wannan kuɗin daga ina? Da yake ina da kati sai na sayi data na shiga App ɗin bankin, da na duba transaction sai na gane ta P.O.S aka tura kuɗin, na fara tunanin ko wane ne wannan tabbas mistake ya yi ba ni ya zo turawa ba, na shiga na duba massages ɗin kan waya, sai na saƙo da sabuwar lamba, bayan sallama aka rubut"Sayyada ga kuɗinki nan, ba na son ajiyar kuɗin wani a hannuna, kuɗinki ne ke kaɗai, ki yi amfani da shi hankali kwance".
Chapter 33 · 0% Book details