← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 89

Sashe 38

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Likita ya É—ora da faÉ—in, yana da kyau a ce an lura da canje-canjen da ta samu kafin faruwar haka, mutum yana zama mai yawan yin shiru, rashin cin abinci, sannan da tsoro da tsarguwa, rashin yarda da kai ma gabaÉ—aya, da kuma mantuwa, idan yarinyar nan ta tashi na tabbata za a ji haka ta faru da ita, sai kuma wani babban lamari da muka lura da shi, wanda shi ma zai iya kawo mata wannan faÉ—uwar, mun gano an sadu da ita lokaci kaÉ—an kafin kawo ta asibitin, idan tana cikin halin rashin lafiya hakan ta faru musamman ba da son ranta ba, ko an yi abin da ya cutar da ita, tabbas hakan zai iya tada ciwon ta yi irin wannan faduwar".

Mama ta ce"Tabbas haka ta faru, ni ma na ga alamar ya sadu da ita, kuma dama hariji ne, ta ce ta gaji tun tuni, tun tana kawo kukanta har ta gaji ta daina".

Likitan ya ce"To wannan shi ne babban kuskuren da kula yi, ta ya za ku ɗauki yarinya ƙarama irin wannan ku haɗa ta da wanda ya fi ƙarfinta?"

Bana ya ce"A yi haƙuri Likita, ni da fari ban yarda ba, na yi zaton shaƙiyancinta ne kawai".

Likitan ya dinga yi musu nasihar 'ya'ya amana ne, don ka aurar da 'yarka ba shi yake nufin ta fita daga hannunka ba har abada, ya zama dole ka dinga bibiya kana sanin halin da take ciki da mijinta, Baba ya yi nadama sosai, jikinsa duk ya yi sanyi, ya fara jin tausayin Sayyada.

Likitan ya ce"Idan mijinta ya zo a turo min shi, sannan sai ta farfaɗo za a sake jin ƙarin bayanin cutar da yake yi mata daga bakinta, bai kamata ku bar case ɗin nan, zan iya shige muku gaba ku yi ƙararsa ku ƙwatarwa yarku 'yancinta, domin ya raunata mata zuciya da gangar jiki".

Baba ya ce"Anya a yi haka kuwa likita? Lamarin nan aure ne ya haɗa da ba fyaɗe ya tare ta a titi yake yi mata ba, a ganina idan aka kai ƙara kamar an bankaɗa sirrin dake rufe ni, a bar zancen kawai Allah Ya ba ta lafiya, amma dai batun aure babu shi, sai ya sawaƙe mata kawai, idan ya cuce ta Allah zai saka mata".

Likitan ya ce"Shikenan, amma duk da haka ku turo min shi idan ya zo, tun da idan ya rabu da ita ai wata zai je ya aura, haka zai yi ta nakasa yaran mutane, yana san ya san hukuncin wannan abin da yake aikatawa da sunan aure, domin fyaÉ—e ne mummuna, me ya hana ya yi bayanin larurarsa kafin aure?"

Baba da Mama suka zauna jiki a mace suna jiran farkawarta, Baba ya kalli Mama ya ce"Amma da ke duk kin ga wannan canjin da ta samu shi ne ba ki faÉ—a min ba?"

Mama haushi ya ƙume ta, ta galla masa harara ta ce"Idan na faɗa maka me za ka yi? Tun da har na faɗa maka hariji ne kuma kai ka san me ake nufi da hariji ai na gama faɗa maka komai, sannan kai ba makaho ba ne, kana kallon yarinyar nan ka san ba ta cikin nutsuwa, amma ka yi biris kawai saboda ba ka sonta, ka ƙi ka yafe mata laifin da ta yi tun a baya, ai ga shi nan yanzu ka kaita inda aka nakasata aka kashe mata rayuwa".

Baba ya ce"Wallahi na yafe mata, na daɗe da yafewa Sayyada, kawai dai ni na duba yadda sunanta yake neman ɓaci ne, wannan ya zo neman aure a kore shi wannan ma ya zo, da haka magana za ta dinga yaɗo har wanda bai san ta aikata ba ma ta sani, duka duniya a ji, shi yasa na roƙi Malam Ashiru ya aure ta, saboda na yaba da halayensa, kuma a ganina duk wanda ya ji wannan abin da ta aikata bai ƙyamace ta ba, ai ya cancanci a zauna da shi duk yadda yake, wallahi da na san cutarwar ta kai haka da zaman aurensu bai kai haka ba".

Can bayan azhar Mama ta tafi gida ta shiryu kayan da za a buƙata na zaman asibiti, Baba kuma yana zaune ransa duk ya yi baƙi, sai ga Ustaz ya ƙaraso emargencyn, da jallabiyarsa da hirami, ga kuma leda a hannunsa ya siyo lemo na ɗari biyar, ya zo ya sunkuyar da kai ya ce"Baba ina wuni?"

Baba ya ƙi kallon shi, bai damu ba ya ce"Ya mai jikin take?"

Baba ya ce"Da sauƙi ya ranka?"

Ustaz ya ce"Tooo...Baba akwai matsala ne? Na ga kamar ana yi min magana a hasale haka, sannan na lura kamar kana jin haushina, wallahi mukullin na nema na rasa ne, sai da na je na siyo, kuma ina dawowa gidan Allah da ikonsa kawai jiri ya kwashe ni na faÉ—i ni ma, kuma hakan ya samo asali ne da wato ainahin shi fargaba da na shiga ta wannan laruri da ya samu ita Assayyada, to amma da yake dai hankalina bai gushe ba, sai na tsinci bakina da furta ayoyin Allah, bi ma'ana Allah Ya nufe ni, shi ne a hankali na dawo daidai, yanzu ya jikin nata ta farka? Jinnu ne?"

Baba ya ƙi kallonsa, takaici ji yake kamar ya tashi ya shaƙe shi, shi kuma Ustaz bai gane ba, ya yi zaton duk jimamin rashin lafiyar ne ya saka shi banza da shi, ya tashi ya zauna a kusa da Baban, ya cigaba da faɗin"To sai dai wani hanzari ba gudu ba Baba, su fa asibiti idan aka kawo mutum wani lokacin ko sun ga jinya ba tasu ba ce sai sun tsaya sun tatsi kuɗi kafin su faɗawa mutum gaskiya, a gaskiya jinyar Sayyada ba ta asibiti ba ce, akwai shaiɗanun aljanu a tare da ita, waɗanda nake kyautata zaton su ne suka saka mata tsakar auren ma kwata-kwata, sannan idan aka yi duba da yadda take guduna da nuna rauninta a fannin raya sunna, za a iya cewa ƙila aljani jinnul ashiq ne a jikin ta, bi ma'ana ya aure ta, shiyasa ba ya so na dinga raɓarta, ka ga ni kuma ana tauye mini hakkina..."

Daidai nan Baba ya miƙe kamar walƙiya, babu zato ya wanke fuskar Ustaz da mari, ya ce"Buhun ubanka kai da hakkin naka!"

Ustaz hankali tashe ya ce"Ya subhanallah! Subhanallah, Baba me ya yi zafi haka? Ko dai aljanun nan sun yi magana sun ɓata ni a idonku?"

Baba ya sake zabga masa mari ya ce"Uwarka ce mai aljanu, mutumin banza da wofi, ashe cutar yarinya kake yi haka, ka ajiye ta a gida kana so ka haukatata ka kashe ta?"

Ustaz ya ruÉ—e ya ce"Subhanallah! Baba me aka ce ya same ta ne? Amma gaskiya ban tsammaci haka daga gare ku ba, irin yadda na rufa mata asiri na aure ta a yayin da mutane suka guje ta..."

Baba ya ce"Koma ka tona mata, na ce bankaÉ—a asirin kowa ya ji, kuma bari ka ji, ba don na duba rufin asirin da ka yi mata ba da yanzu wata maganar ake yi ba wannan ba, don so aka yi a kai case É—in ga hukuma, yanzun ma ka je likita yana nemanka, idan ka cuci Sayyada kuma Allah Ya saka mata".

Ustaz ya ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Don Allah Baba a yi haƙuri don Allah, na san na yi kuskure amma in sha Allah zan gyara, kuma wallahi tana da matsalar aljanu a duba lamarin da ai ba haka take ba".

A fusace Baba ya nuna masa hanya ya ce"Fice daga asibitin nan tun ban kwantar da kai ba, ka fita na ce kar a yi abun kunya, idan har da sunan duba Sayyada za ka zo asibitin nan kar na sake ganinka, mutumin banza malamin ƙarya, macuci, kuma ka aiko mata da takardarta cikin salama".

Ustaz ya ce"To shikenan Baba, yanzu ranka a ɓace yake dai, idan ka huce ma yi magana, Allah Ya sani ban cuci matata na, ni kuma idan an cuce ni na yafe".

Duk wannan abin da ake yi bai ajiye ledar hannunsa ba, har ya tafi ya dawo ya ajiye ya ce"Ga wannan tun da na riga na siya, Allah Ya rufa asiri Ya huci zuciya".

Ya ajiye ya tafi, bai bi ta kan likitan da aka ce yana neman shi ba ya bar asibitin.

Yana tafe gabansa yana faɗuwa, yana karanta La haula wa la ƙuwwata illa billah, babban tashin hankalinsa a yanzu shi ne a ce ya saki Sayyada, samun wacce za ta aure shi ba lallai ya zama matsala ba, amma akwai ƙalubale guda biyu wanda za su iya kawo tsaiko kafin auren, domin ba kowacce mace za ta yarda ta auri talaka irinsa ba, tun da yanzu matan zamanin nan suna da bori da shagala, na biyu kuma yana jin tsoron a yi auren matar ta kasance mai rauni kamar Sayyada, daga lokacin da ya fara auri saki hankalin mutane zai dawo kanshi a fara binciken dalili, idan aka gano shi hariji ne ya zai yi da rayuwarsa? Wannan shi ne abun fargabarsa, don haka ya gama yankewa ba zai saki Sayyada ba duk runtsi, sai dai duk wacce za a yi a yi.

Ban farka ba sai dare, ko da na farka ba na cikin hayyacina, cin abinci, wanka, shan magani da allura, wannan duk ina yi ne ba tare da na tuna ko ni wace ce ba, sai bayan kwana uku na dawo daidai, ban yi mamakin ganina a asibiti ba, tun da dama na san a halin da nake ciki komai zai iya faruwa, jikina ya yi min nauyi, amma kaina ya yi sauƙi ciwon kan nan ya ragu da kaso saba'in cikin ɗari, na kalli Mama dake sallaya tana jan carbi, abubuwan da suka faru suka shiga dawo min, na fara hawaye, sai da na fara kuka me shassheƙa sannan Mama ta ankara na tashi, ta zo ta zauna ta kama hannuna ta ce"Sayyada, sannu ya jikin naki?"

A hankali na furta Mama me yasa ban mutu ba? Don Allah ki faÉ—awa Baba ya fahimce ni wallahi ba zan iya wannan zaman ba".

Mama ta ce"Shikenan, Babanki ya fahimce ki Sayyada, ki kwantar da hankalinki kin ji?"
Chapter 38 · 0% Book details