← Book details Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 89

Sashe 40

Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ce"Subhanallah! Wato mun lura Assayyada kina kaurara harshenki, amma la ba'asa ni dai har zuciyata na yafe miki, sai dai yaya za ki yi da faÉ—in Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama na cewar kada mace ta É—aga muryarta sama da ta mijinta? Assayyada idan fa ba ki kula ba kin fara yi min biyayya za ki iya shiga halaka al azeem, bi ma'ana halaka mai girma".

Na ce"Ba sai na ƙara zama da kai zan halaka ba? Ka ga ka yi maganar da ta kawo ka gidan nan".

Ya shiga shafa gemu yana yi min wani fitinannen kallo yana narke idonsa masu cike da sha'awa ya ce"Maganar aure ce Assayyadda, maganar kome, bi ma'ana ta neman sasanci, Assayyada tun da dai Allah Ya sa jikinki ya yi ƙwari, don Allah ki cire komai a ranki, ki wuce mu tafi izuwa gidanmu, domin mu ɗora daga inda muka tsaya, bi ma'ana rayuwar aurenmu ta cigaba, amma fa ba irin ta baya ba".

Ya gyara zama ya janyo ledar kusa da shi ya buÉ—e ta, yana cewa"Idan kika yi duba da abin da yake cikin ledar nan za ki yarda da kalamina na cewar ba irin rayuwar baya ba".

Na kalli ledar na ga kaza ce 'yar tsamurmura ta sha gashi, ga ta nan a gudanta ba a yayyanka ba, na kau da kai na ce "A tunaninka saboda ba na cin nama ne zan guje ka".

Ya ce"A'a Assayyada, na san ba haka ba ne wallahi, maƙasudin ai batu ne na raya sunna, bi ma'ana kina da rauni a fannin kashe arna, to in sha Allah na yi miki alƙawin za mu yi minus one, kin san a baya ma ai mun yi, ranar da abun ya faru ma wallahi ba don na ga cinyarki ba da ba lallai haka ta faru ba, to wannan kallon ita cinyar ne ya haddasa komai, amma yanzu bisa adalcina na yi miki alƙawarin za a yi minus two, bi ma'ana an cire na rana, an cire na asuba shi ma, sai dai zan dinga dawowa kasuwa kamar ƙarfe shida haka, idan na dawo sai ki ba ni dama ki taimake ni na 'yan mintuna kafin sallar magriba, daga nan kuma sai daren, ai a baya na faɗa miki shi na daren a shi na fi samun nutsuwa".

Na ce"Ni fa bari na faɗa maka gaskiya, wallahi na gama aurenka, ba zan sake zama da kai ba, gara ma kawai ka yi wa kanka ƙiyamul laili ka sake ni".

Cikin rashin gane magana ta ya ce"Ƙiyamul laili ai ina yi Assayyada, ke ce ma kike da wannan raunin ba kya yi yadda ya kamata, kuma batun saki sai dai na ce Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, subhanallah!".

Ya É—aga hannunsa sama ya buÉ—e ya fara addu'a ya ce"Ya Allah ni bawanka Ashir ina nemawa matata Assayyada yafiyarka, bisa wannan babban zunubi da ta aikata, wato ma'ana zunubi azeemee, Allah na yafe mata, Allah Ka yafe mata ba don halinta ba, ba don aikinta ba, sai don rahamarka ga bayinka, ya Arhamar Rahimin".

Ya shafa a fuskarsa, sannan ya kalle ni a rikice ya ce"Assayyada, shin mantawa kika yi da haramcin mace ta nemi saki babu dalili ko kuwa kin jahilci lamarin ne?"

Na ce"E Nei jahila ce kuma ba na fatan na san wa'azin nan na son zuciyarka".

Ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ce"Haƙiƙa abun azeemun ne, bi ma'ana mai girma".

Ya fara matsowa kusa da ni, yana cewa"Maganar nan ba ta fatar baki ba ce, na lura cewa kin yi kewata, duk da kin fusata, to kuma kin san shi raya sunna irin wannan yana wanke zuciyoyin ma'aurata, bi ma'ana yana kawo sasanci da fahimta juna, daure ki taimake ni ko da al ƙublatu ne, wato bi ma'ana sumba, inda zan yi na minti shida na san za mu iya samun daidaito kafin gobe na zo mu yi zama na musamman".

Na matsa gefe ina cewa"Ko zuwa dubu za ka yi ba zan canza maganata ba wallahi, ni da kai zama ya ƙare, ko hannuna ba za ka sake riƙewa ba".

Ina rufe baki ya fizgo ni, na faɗa jikinsa, ya rungume ni ƙam, zuciyata ta dinga bugu, na kasa ƙwacewa har sai da ya sassauta riƙon ya fara lalubar jikina sannan na samu damar ture shi, na fita daga ɗakin har ina tuntuɓe, na faɗa ɗakin Mama i a fashewa da kuka, shi kuma ya fice daga gidan ko sallama bai yi wa Mama ba, Mama ta ce"Lafiya? Me ya yi miki?"

Na ce"Ba komai".

Ta ce"To kukan na mene ne"

Na ce"Cewa ya yi ba zai sake ni ba".

Ta ce"Shi ne kike wahalar da hawayenki? Saki ai ya zama dole kuwa, don haka ki ma kwantar da hankalinki, ai musulunci bai yarda da zaman aure mai cutarwa a cikinsa ba, shi yasa aka samar da saki, don haka ki rabu da shi, ya ƙaraci zaryarsa har ya gaji ya sallame ki".

Na sauke numfashi gabana ya a faduwa, ni tsorona É—aya kar wataran ya yi min fyaÉ—e a gidan namu a sha kunya, da alama Mama ba ta gama sanin Ustaz ba ne.

Na ɗakko kazar na kai wa Mama, ta taɓe baki ta ce "Ai wannan kazar a baya ne kike buƙatarta ba yanzu ba, wato da nama zai yaudare ki saboda ya mayar da ke kura".

Mama dai ba ta ci ba, ni ma kaɗan na ci na ajiye sauran, can wajen sha ɗaya na dare sai ga kiran shi, na ƙi ɗauka, sai da ya yi min kira bakwai a na takwas na ɗauka na ce "Lafiya?"

Da irin wannan Muryar da take razana ni, wacce idan na ji na san kwanan zancen ya ce"Assayyadata, me yasa ba za ki taimake ni ba? Ina cike da buƙatar matata da son kasancewa da ke, don Allah ki taimaka, yau ya zan yi? Ai na ce miki za a yi minus two ko? Don Allah ki vedio call mu yi".

Na kashe wayar ban ce masa komai ba, na kashe ma gabaÉ—aya zuciyata na bugu, tunawa da irin rayuwar da na yi, samun nutsuwa ko azaba? Wallahi gani nake kawai ya kashe min sha'awa ko wani auren na yi ba zan sake jin sha'awa da son raya sunna ba, ya azabtar da ni da ni, ya zama kamar horo a wajena ba nishaÉ—i da nutsuwa ba, na lumshe ido, a fili na ce"Alherin ya kai maka har gadon baccinka Sadam".

Hawaye ya zirararo min na share, ina tuna abubuwa masu dama, masu daÉ—i da akasinsu, haka na kwana zuciyata cike da fargaba, gani nake kamar idan ya matse lamba Baba zai canza shawara ya ce sai na koma.

A ɓangaren Ustaz kuwa, a birkice ya koma gida, hankalinsa duk ya tashi, sai da ya yi nadamar taɓa Sayyada, saboda wata fitinanniyar sha'awa ce ta taso masa kamar za ta kashe shi, ya yi wanka wajen sau biyar babu sassauci, ya kwanta ya kasa bacci, ya sauka daga gadon ya dinga zagaye yana sambatu shi kaɗai, kafin dai ya yi tunanin kiran Sayyada ko za ta yarda ta rage masa zafi ko ta waya ne, amma ina, sai ta kasa fahimtar halin da yake ciki, ya dinga juyi a gado, ƙarshe dai sai istimna'i ya yi, wato ya biyawa kansa buƙata da taimakon man shafawar Sayyada wani lotion, yana yi yana Astagfirullah,ya yi wanka wani wahalallen bacci ya ɗauke shi da ƙyar, mai cike da mafarkai barkatar duk a kan kashe arna.
[22/10, 7:08 pm] Sadiya Abdulrazak: 25

Washegari da sassafe sai ga kiran shi, ban ɗauka ba, can wajen ƙarfe bakwai ma ya ƙara kira, ban ɗauka ba, sai ji na yi ana sallama da Sayyada, na kalli Mama, ita ma ta kalle ni ta ce"Wane ne kuma da safen nan? Leƙa ki gani".

Na saka hijjabi na fita, na ga Ustaz ne tsaye hannunsa riƙe da leda, na haɗe rai ban ce komai ba, shi kuma ya yi murmushi ya ce"Assalamu alaikum, barka da safiya, mu shiga daga zauren ko?"

Na juya na koma , ya shiga shi ma, ya tsaya yana kallona yana lashe baki kamar tsohon maye kafin ya ce"Assayyaddata".

Ban amsa ba, ya ce"Jiya na kwana da mafarkanki masu birkita mutum da son kasancewa da ke, shi yasa dama na ce zan so na zo na gan ki da safen nan, bi ma'ana na samu sassaucin abin da nake ji a zuciya da gangar jikina, musamman ma dai gangar jikin".

Ni dai ina tsaye kamar an dasa ni, ko kallon shi ba na yi, ya ce"Assayyada, don Allah ki yi haƙuri mu koma haka, wallahi sam ba na Cikin nutsuwata, domin sallah ma yau makara na yi, sai ƙarfe shida na yi sallah, kin ga kuwa idan rayuwa ta cigaba da tafiya babu ke haƙiƙa za a samu babban giɓi, bi ma'ana babbar matsala, don Allah mu koma rayuwarmu, ai na faɗa miki na yarda zan canza, zan rage, tun da Hausawa sun ce da babu gara ba daɗi, ko sau ɗaya ne yanzu na yarda, indai dare zai yi na samu inda zan raba a kula da ni a taimake don Allah, ni zan iya dauke miki girki ma da duk hidimarsa gida, domin ki dinga samun hutu don Allah".

Ganin ba zan kula shi ba ya ce"Shikenan Assayyadda ga wannan, dama kayan karin kumallo na kawo miki, tun da ai hakkina ne na ciyar da ke ko?"

Na ce"Na gode, amma a nan gidanmu ma ba a gaza ba, kuma ba za a gaza ba in sha Allah".

Ya ce"Ai dama ni ma ban ce an gaza ba Sayyada, kawai dai sanin hakkina ne shi yasa na ga dacewar na kawo É—in".

Na ce"To an yafe maka".

Na juya zan tafi, ya riƙo hijjabina yana kirana murya can ƙasan maƙoshi, na fizge na ce"Don Allah daga yau kar ka sake taɓa ni, idan ba haka ba za ka daina ganina har abada, don na lura ba ka gane karatun da nake yi har yanzu".
Chapter 40 · 0% Book details