Sashe 80
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umma ta ce"Ni fa tausayinka nake ji, har ka manta yadda yarinyar nan ta birkice lokaci ɗaya ta dage sai ka sake ta? Kuma dole haka ka sake ta ɗin saboda iyayenta sun ɗaure mata, yanzu ma tsaf wani abu zai gifta rana ɗaya ta ce sai ka sake ta, kuma da ita ga dogara, ai gara ka auri wanda ɗin, ko ba komai gida biyu maganin gobara, ina fargabar ka zo nan gaba ka rasa macen aure, amma ita Rakiya tun da larurarku ɗaya in sha Allah ƙalau za ku zauna, kuma ka ga 'yar talaka ce irinka, don haka ba za ta rainawa ƙoƙarinka ba".
Ustaz ya sunkuyar da kai ya ce"Umma wannan ƙarin auren umarni ne ko shawara?"
Ta yi masa wani kallo"Umarni ne, idan kuma ban isa ba sai ka faÉ—a min".
Ya fara girgiza kai"Lala-lala wallahi kin isa Umma, shikenan za a san abun yi in sha Allah, amma ina rokon ki taya ni da addu'a, bi ma'ana yadda zan shawo kan ita Rauda É—in, tun da gaskiya tana cikin mata masu zafafawa, bi ma'ana ta fannin kishi".
Umma ta ce"Allah Ya ba ta haƙuri, ya kawo komai cikin sauƙi, kai dai fatana ka zama mai adalci a tsakanin matanka, kowacce a cikinsu da ranarta a gare ka, ka ga ita matarka ta yi maka halacci ta so ka ta zauna da kai, sannan mahaifinta ya yi maka halacci ya ba ka aikin yi, ita kuma Rakiya da za ka aura irin larurarka ce da ita, ka huta wannan raɓe-raɓen da kake yi, to don haka ka riƙe su su biyun da adalci, Allah Ya sanya alkhairi, sai a saka sati uku ma ya isa".
Suka yi sallama Ustaz ya tafi, jikinsa a mace ya koma gida, ya kasa ɓoye damuwarsa har sai da Rauda ta fahimta, ta tambaye shi mene ne? Ya ce"Rauda akwai matsala, wallahi ina son ki, ina fargaba da ɗari-ɗarin rabuwa da ke Raudata".
Ta ce "Subhanallah me ya faru da kake tunanin za mu rabu?"
Ya fara girgiza kai ya janyo ta jikinsa ya ce"Rauda ina sonki, ina son farincikin iyayena, shin za ki iya taimaka min na yi musu biyayya domin na rabauta? Bi ma'ana su ɗaga min ƙafafu na shige aljanna? Kin san a yanzu ni aljannata tana ƙarƙashin ƙafarsu, kafar yadda taki take ƙarƙashin ƙafata, don haka ya zama wajibi na yi musu biyayya matuƙar dai umarnin nasu bai saɓawa shari'a ba".
Ta ce"Hakane".
Ya ce"To dama, akwai wata yarinya zan ce ko mata ma oho, da ita Umma bi ma'ana mahaifiyata, sai ta ba ni umarnin da na aure ta..."
Kafin ya ƙarasa Rauda ta mike daga cinyarsa, ta fara muzurai "Ka aure ta?"
Ya janyo hannunta, ta ƙwace ta ce"Kenan dai har yanzu ban ishe ka ba wata kake hange a waje ko?"
Ya fara girgiza kai"Subhanallah, Rauda ki ji tsoron Allah, ki sani ni mijinki ne, ba a É—agawa miji murya, ballantana kuma a É—aga masa hankali, amma la ba'asa idan don ta ni ne na yafe miki, sai dai ya za ki yi da hukuncin Allah?"
Ta banka masa harara ta ce"Ka ma jingine wa'azinka a gefe, don ya daina tasiri a kaina".
Ya ce"To shikenan, ki yi haƙuri ki saurare ni, ita fa Rukayya ba sonta nake yi ba, ke ce zaɓina, saboda haka ke ce da riba, Umma ce ta nema min ita tun kafin ki dawo gare ni, bi ma'ana lokacin da muka rabu, to yanzu kuma sai ta ba !ni umarnin da na aure ta lallai-lallai na haɗa ku biyun, don Allah Rauda ki yi min adalci ki bar ni na aure ta, bi ma'ana na cika umarnin mahaifiyata, Rauda duk fa mai saɓawa iyaye ba zai yi albarka ba, idan na ɓalɓalce ke ma ba za ki ji daɗin zama da ni ba".
Rauda ta ƙi sauraron shi, ta shige ɗaki, sai da ya yi sati yana lallaɓa ta, kafin ya shawo kanta, ta haƙura ta yarda da auren, nan ma kuma aka zo batun ɗaki, aka dinga tataɓurza ta ce ba za ta zauna mata a gida ba, ƙarshe dai sai zuwa ya yi ya sanarwa mahaifinta, ya ce shi babu ruwan shi a sabgar gidan shi, da ƙyar Rauda ta yarda ya gina wani ɗakin a tsakar gidan, ɗaki ne kamar ciki da falo, amma na cikin ɗan ƙarami ne sosai, shi ne za a mayar kitchen, dama akwai banɗakin tsakar gida.
Haka dai ya dinga lallaɓa ta, tana sha masa ƙamshi, taimakon da Allah Ya yi masa shi ne ba ta haɗe masa yanzu duk faɗan da suka yi idan dare ya yi za su jone. Ya bawa Rakiya kuɗin aure dubu ɗari biyu, Rauda kuma ya ba ta dubu ɗari ya ce ta sayi kayan kwalliya,kuma ta karɓa a ranta ta ce ai raba arne da makami ibada ne.
Aka ɗaura aure cikin rufin asiri, da rana 'yan'uwanta suka zo suka kawo kayanta, katifa ce babba sai kayan kitchen, don ta ce ta daina yin kayan gado da kujeru don asara suke zame mata, ƙarshe auren ya mutu ta siyar da su a banza, har aka yi jeren aka gama ba su ga idon Rauda ba, don kulle ɗakinta ma ta yi, ko 'yan'uwan Ustaz da suka zo kawo abincin masu jere ba ta bari sun ganta ba, ballantana masu jeren, kishi take yi na gaske a kan mijinta. Da daddare abokan Ustaz guda biyu masu mota suka je suka ɗakko amarya da tsirarun 'yan'uwa, da aka kawo ta haka aka dinga ƙwanƙwasa ƙofar Rauda wai za a ba ta amana, ta ƙi buɗewa, ƙarshe ta kira Ustaz ɗin ta yi masa tass, ta ce idan bai yi musu magana sun shafa mata lafiya ba sai ta fito ta daddana musu na maguzawa, shi ne fa Ustaz ya firgita, don ba ya son fitina, ya kira Rakiya ya ce mata lallai-lallai su rabu da Rauda su ajiye ta a ɗakinta kawai kowa ya kama gabansa, suka tafi suka bar amarya Rakiya zaune, ta tashi ta sake gyara ɗakin komai ya yi mata daidai, ta ɗakko rigar bacci ta saka ta janyo wata leda viva mai cike da kayan mata, ta ɗakko wani abun matsi ta tura, ta baje jarkokik tsumi da zuma, ta samu robar cin abinci ta dinga zuba su ɗaya bayan ɗaya, aka saka gumba, ta zuba madara ta dame su ta ɗaga ta kwankwaɗe, ta mayar da su inda suke, tana jin shigowar Ustaz ta janyo hijjabi ta zumbula.
Æangaren Rauda ya fara zuwa, ya kira ta a waya ta buÉ—e masa, ya yi zaton ma za ta Æ™i buÉ—ewar, don haka ya shiga da fara'arsa yana faÉ—in"Raudata Allah Ya yi miki albarka, Allah Ya bar mu tare".
Ta harare shi ta ce"Ai dama haka za ka ce, ai ni yanzu ba yarda da maganarka zan yi ba, tun da ka nuna min iyakata".
Ya janyo ta jikinsa yana"Haba Raudata, uwargida ran gida, kuma ran Ashir, domin idan kika guje ni na kaÉ—e".
Ta ce"Ba wani nan".
Ya ce"Allah kuwa, zan yi kewarki fa".
Ta ce"Ni dai je ka, kar ka saka min rai a kan abin da yau ba nawa ba ne".
Ya ce"Wallahi naki ne, don yanzu kika ce kina so za ki samu".
Ta ce"A'a ba na so, ka je can ka kwana kana bata".
Ya yi dariya kawai, ya miƙa mata leda guda ɗaya ya ce"Ga kazarki, ko na zauna na ba ki a baki?"
Ta ce"A'a ni dai tafi".
Ya tafi yana waiwayenta, ta rufe ƙofar ta zauna ta fara hawaye.
Idan Ustaz ya ce ba ya zumuɗin auren ya yi ƙarya, sai dai ya ce ba sonta yake yi ba kawai, amma yana ɗaukin ganin tata jarumar, ko Rauda da ta zama 'yar hannu tana gamsar da shi ne ba wai ya ƙure ƙarfin sha'awarsa ba, don haka zai so a ce ya samu wacce za su kwana suna yi ba tare da tunanin ya shiga hakkinta ba, shiyasa yake jin Rakiya za ta zame masa matar biyan buƙata da samun nutsuwa, ita ma Rauda sai ta huta a ranakun kwanan da ba nata ba.
Da sallama ya shiga ɗakin, Rakiya ta amsa, tana kallon shi ta haɗiyi yawu muƙut, abubuwa suka fara motsa mata, ta yi murmushi ta ce"Sannu da zuwa".
Ya ce"Yawwa amarya mai araha, wacce ba ta rowar fuskarta".
Ta yi yar dariya ta ce "Haba Malam, wannan fa shi ne aurena na shida, to kunyar me zan ji kuma?"
Ya ce"Hakane, aurenki na biyar kuma na ƙarshe bi izininllah! Bi ma'ana indai har da gaske rashin gamsuwa ne matsalar dake kashe miki aure to kuwa ki saka a ranki kin zo gidan magani, waraka ta zo bi izininllahi".
Ta yi murmushi ta ce"Alhamdulillah, duk da dai ba girin-girin ba ta yi mai".
Ya ce"Hmm Ruƙayya kenan, yanzu dai bari na yi wanka, ki yi alwala kafin na fito".
Ta tashi ta fita ta zuba ruwa ta kai masa, kafin ya fito ta yi alwala, ya saka jallabiya suka yi sallah raka'a biyu, ya yi musu addu'o'i, yana zare jallabiyar haƙurin Rakiya ya fara ƙarewa, don dama tun daga gida a matse take daurewa kawai take yi, Ustaz ya tura mata keda ya ce ga wannan, sai ki cire kayan shayin, ga kuma kaza, idan akwai ruwan zafi ma zan so a haɗa min shayin, tun safe ban ci komai ba".
Rakiya haushi ya fara kama ta, yadda take a uzurce har wani dahuwar shayi yake nema shi, to da tun daga nan gabanta ya fara faÉ—uwa, ta fara inkarin harijancinsa, ta ce"Ni ba ni da wani ruwan zafi".
Ta cire hijjabin ta tashi ta fara yan gyare-gyare a ɗakin, dayake tana da diri sai surarta ta fizgi Ustaz, ya haɗiyi yawu, sai ya tashi yana cewa"Bari dai na yi shaf'i wal wutur, domin ban san yaya za a kaya ba idan aka shiga fagen dagar nan Ya Ruƙayya".
Ta ji sam ba za ta iya jurewa ba, nema yake ya ƙure haƙurinta, don haka ta ƙarasa ta janyo shi ya faɗo jikinta, ta shiga sarrafa shi tana faɗin"Haba dai Malam, sai na fito fili na faɗa maka a uzurce nake sannan za ka fahimta?"