Sashe 76
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zuciyata ta dinga bugawa da sauri, na kalli Isma'il na ga yadda ya zuba min ido ko ƙwaƙƙwan motsi ya kasa yi, sai fitar numfashinsa da ya canza, ya jefo min wayar a cinyata ya tashi ya bar falon a fusace, na fashe da kuka, kuma har lokacin Saddam bai kashe wayar ba, don haka na fara surma masa Allah Ya isa ina faɗin ba zan yafe masa ba, kuma muddin mijina ya zarge ni har aurena ya lalace sai na yi shari'a da shi, sai ya fara dariya ko a jikinsa yake cewa"Sayyada, yanzu da gaske sai ki yi shari'a da ni? Kenan kin fara son shi ko?"
Da sauri na cire ƙunshin hannuna na watsar na kashe wayar, na yi saurin share hawayena ganin mai yi mana wanka ta dawo ɗakin.
08028966015
[15/11, 8:44 am] Sadiya Abdulrazak: 45
Fargaba da kunya suka kama ni, na shiga rashin nutsuwa sosai ga zulumin yadda Isma'il zai ɗauki abun, ko da na haihu bai daina rabon kwana ba, yau ranar kwanana ce, amma haka ya ƙi zuwa ɗakina, ya kwana a wajen Hajiya, bacci rabi da rabi na yi, tsoro fal raina.
Washegari suna a masallacin unguwarsu aka yi raɗin sunan, na yi zaton Isma'il zai shigo da safe mu tattauna ko kuma ya ga lafiyar ɗansa, duk da yana fushi da ni, amma sai aiko min da kayan raɗin suna ya yi, wajen ƙarfe goma na kira shi a waya ya ƙi ɗauka, na dinga jera masa kira bai ɗauka ba, na tura masa sako na ce masa ya yi haƙuri don Allah ya zo mu tattauna, shiru bai dawo da amsa ba, na kasa daurewa na dinga hawaye. Shadda kala uku ya ɗinka mana wacce za mu yi ankon suna, hatta style ɗin hotuna da vedios mun gama tsarawa, amma haka Sadam ya rusa min komai, domin kuwa tun fitar da ya yi da safe bai dawo gidan ba sai dare, kuma don wulaƙanci wai sai ga Hajiya Halima tana faɗa wa yan'uwana ya ce duk abin da ake buƙata a tambaye ta, haka aka yi taron suna aka watse ina ta yaƙe.
Bai daina rabon kwana ba duk da na haihu, kuma ranar sunan ni ce da kwana, amma haka ya ƙi zuwa sashena, ya kwana a ɗakin Halima, na yi ta kuka ni kaɗai, na sake yarda Sadam ba alkhairi ba ne a rayuwata, guba ne, wanda burinsa ya yi ta azabtar da ni kawai, na ƙara tsanar shi, tsana mai tsanani kuwa, sai yanzu ma nake godewa iyayena da suka hana ni auren shi, kuma suka kwaɗaitar da ni auren Isma'il, sai yanzu nake son mijina da jin ko me zai faru ba zan bari na bar gidan shi ba.
Washegari ma ban gaji ba na dinga kiran shi bai ɗauka ba, ko rabon naman suna da aka yi sai Hajiya Halima aka kaiwa nashi, ita kuwa abun nema ya samu sai fiffika take yi tana shan ƙamshi, ni fatana ma a ce bai faɗa mata komai ba, saboda wannan sirrina ne, ko iyaye ban yi niyyar faɗawa ba sai dai idan shi ya faɗa babu yadda zan yi, saboda sun san ni a kan son Sadam, kuma ba sa ganin zuciyata ballantana su yarda na daina son shi. Yau kam na yi niyyar dole sai mun haɗu, don haka dab da zai dawo daga sallar isha'i na fita tsakar gidan na ja kujera filastik na zauna, ai kuwa ana idar da sallah da kaɗan sai ga shi ya shigo, na tashi na tare shi ya ɗan dakata yana kallona, na ce"Don Allah ka tsaya mu yi magana, na gaji da wannan horon da kake yi min".
Ya ce"Ba ki da abin da za ki faÉ—a min Sayyada, tun da kunnena ya jiye min komai ai".
Na ce"Wallahi ba haka ba ne, tun da aka yi auren nan bai taɓa kirana ba sai ranar, bibiyata yake yi da sharri".
Ya ɗaga min hannu alamar dakatarwa ya ce"Ko kuma kuke biyar juna ba! Na yi bincike tun washegarin ranar na ji wane ne Sadam, na ji irin alaƙarki da shi, da kuma yadda kike son shi, saboda haka ƙarya ne ki faɗa min wai ba ku saba waya a gidana ba, Sayyada ba ki da adalci, shin mene ne laifina da ba za ki so ni ba?"
Na katse shi da faɗin"Wallahi ina sonka, wallahi ba ni da sauran alaƙa da shi tun kafin na yi auren nan".
Ya ce"Ki je ki yi duk yadda kika tsara, rayuwarki ce, na yi kuskuren tunanin zan iya yin abin da za ki so ni, amma yanzu na gane duk wanda ba ya sonka to ba zai taɓa sonka ba".
Ya gota ni zai wuce na tare shi na faɗa jikinsa kuka mai ƙarfi ya ƙwace min, wanda yake fitowa tun daga zuciyata, ya yakice ni ya matsar gefe ya shige sashen matarsa, na koma nawa sashen na tisa kuka a gaba na yi mai isata, tun daga ranar zaman gidan ya ishe ni, na rasa me yake yi min daɗi, kullum sai na kira shi ba ya ɗauka, haka zan yi masa text massage ya ƙi kula ni, ta whatsApp ma babu amsa, kwana biyar bayan suna na yi masa massage na ce ma zan tafi gida, sai ga shi ya dawo min da amsa ya ce Allah Ya tsare hanya, sai ga direban shi ya turo yana jirana, na shiga sabon ɓacin rai, tun da aka yi hakan dole na tafi, don ni da ban yi zaton zai bar ni na, haka na kira Mama na ce mata zan dawo gida na ƙarasa wanka, ta ce sai na zo, muka tafi ko sallama bai bari mun yi ba.
Da muka je gida Mama ta gane ba ni da nutsuwa, ta shiga tambayata mene ne yake damuna na ƙi faɗa mata na ce kawai ba na jin daɗi ne, ta tambaye ni dole na yi wa mijina ya bar niena taho? Tun da da farko ya nuna ba ya so, na ce a'a ba dole na yi masa ba, a ranar kuwa zazzaɓin na gaske ya rufe ni, washegari Mama ta raka ni asibiti, muna fitowa daga cikin asibitin sai ga Saddam ya zo shiga, ban taɓa zaton zai iya yi min magana a gaban Mama ba, sai ga shi ya taho inda muke da saurinsa, ya fara faɗin"Sayyada, Sayyadata ashe da gaske kin haihu ko? Yanzu Shikanan kin ci amanata ba za ki dawo mu cigaba da rayuwar aurenmu ba? Kin ga ita ma Safna ta ƙi dawowa, yanzu wa zai riƙe mata 'yarta?"
Gabana ya dinga faɗuwa, Mama ta kalle ni ta kalle shi, ya ce"Mama ina kwana, don Allah ki saka baki Sayyada ta dawo ɗakinta, na tura mata kuɗin hayar gidanta ma, amma ta ƙi dawowa".
Mama ta damƙi hannuna ta ja ni muka bar wajen, sai kuwa ya biyo mu da sauri yana kirana, Mama tana juyowa ta wanke shi da mari, muka tsayar da adaidaitasahu muka shiga muka tafi, idan ba idona ne ya faɗa min ƙarya ba sai na ga Sadam kamar ba ya cikin hayyacinsa, kuma kamar wanda yake cikin maye, na yi tsuru-tsuru, Mama ba ta yi magana ba har muka ƙarasa gida, Baba yana nan bai fita ba, na yi ɗakina ita kuma ta shiga ɗakinsa, babu jimawa sai ga su sun shigo ɗakin nawa, sai da gabana ya faɗi, saboda Baba bai cika shigowa ɗakina ba sai da dalili mai ƙarfi, na ajiye Daddy da nake shirin shayar da shi na ce"Sannunku".
Baba ya ce"Sayyada ashe ba ki rabu da yaron nan ba Saddam? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un".
Mama ta ce"Ba su rabu ba, domin da alama sun haÉ—a baki ne za su haÉ—u a asibiti kamar yadda suka saba, tun da ba ta san zan rakata ba sai da safen nan".
Da sauri na ce"Mama na rantse da Allah ba na tare da kowa sai mijina, wallahi na manta da Saddam a rayuwata, ban san ma za mu haÉ—u wallahi, na canza halina, na tsane shi tun kafin na yi aure". Na fashe da kuka.
Mama ta ce"To wane kuÉ—in haya ne ya ce ya ba ki?"
Na fara inda-inda kafin na ce"Ƙarya yake yi, ni babu wani kuɗin haya".
Baba ya ce"Kawo wayarki".
Na É—auka na ba shi gabana yana faduwa, sai yanzu na san na yi kuskure da ban goge alert É—in da massage din ba, wani tsautsayi babba, salatin da Baba ya fara yi ne ya sa na fahimci lallai ya gani, Mama ta ce"Akwai maganar ko?"
Ya ce"To ai ba wannan ba, shi ma mijin nata ya sani, ga shi nan tana yi masa massage ɗin ba da haƙuri ya ƙi sauraronta, Saddam ɗin gidanki ya zo ko mijin ne ya gamu da shi a wani wajen?" Ya ƙarasa da daka min tsawa.
Na ce"Wallahi babu É—aya, na rabu da shi da gaske".
Ya ce"To ga shi a nan ya ce ga kuÉ—in hayar ki, ga kuma alert dubu É—ari uku, shin kin sayi gida ne dama ba mu da labari?"
Na zayyana musu komai na yadda ya ce ya bar min gidan, sannan na faÉ—a musu yadda ya kira ni a waya muna tare da Isma'il É—in, na É—ora da faÉ—in"Wallahi ba da son raina ba dama ina niyyar mayar masa da kuÉ—insa, wallahi na rabu da shi har abada".
Baba ya ce"Ai shikenan, yanzu tun da an yi haka ni dai ba za ki saka na dinga jin kunya ba, domin ina ga wannan Saddam ɗin tare kuka rayu a cikin mahaifa, kuka yi gware kuka fito duniya, shi yasa kika kasa rabuwa da shi, zan roƙi mijinki alfarmar ya sake ki kawai, don ba za ki mayar da ni ƙaramin mutum ba".
Ai sai na ji wani sabon tashin hankalin, na fashe da kuka na ce"Baba don Allah ka yi haƙuri, wallahi ina son mijina, ban san yadda zan yi da Sadam ba, ya zamar min annoba, ba ni da ƙarfin yakice shi daga rayuwata ni kaɗai sai kun taya ni".
Mama ta ce"Tun da mu ne muka taya ki kika kawo shi cikin rayuwarki ko? Ki je ki yi ta yi, kowa ya yi na gari kansa".