Sashe 11
Ku Yi Min Adalci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
08028966015
[28/09, 7:32 pm] Sadiya Abdulrazak: Yayan babana shi ne ya tsaya min tsayin daka, bayan ya gama yi min nashi faɗa da nasihar, ya ce hannunka ba ya ruɓewa ka yanke ka yar, sannan ba za a bar Sadam ya ci bulus ba, ya zama dole ya aure ni, shi ya shige gaba ya je gidan su Sadam ya sanar da su ya riga ya lalata ni, don haka auren nan babu fashi, idan kuma ya ce ba zai aure ni ba to za a yi ƙararsa a kan lalata min rayuwa da ya yi, shi ne mahaifinsa ya ce ba damuwa zai aure ni, yayinda mahaifiyarsa ta yi tsallen baɗake ta ce ba zai auri mara tarbiyya ba, aka dinga kai ruwa rana, ƙarshe dai aka fi ƙarfinta, aka sake saka ranar aure sati biyu masu zuwa, Baba ya ce ko ya shirya ko bai shirya ba za a ɗaura idan ma a kafaɗa zai yi yawo da ni sai dai ya yi, da aka sanarwar babana sai ta ce babu ruwan shi fa a magana, kuɗin kayan ɗaki dama ya daɗe a wajen kafinta kuma aka yi sa'a Baba bai karɓe ba, kayan kitchen ɗina ma tuni an gama haɗa komai, don haka ba a da matsala ta nan ɓangaren.
Kuma wani abun mamaki Sadam shi ma ya amince da auren, bai nuna mini wani ɓacin rai ba, firarmu muke yi hankali kwance, sai yake nuna min shi fa dama ba auren ne ba ya so a yi ba, kawai dai ƙaryar da ya yi tun farko ne bai faɗawa iyayensa zai yi aure ba, ya sa shi fargaba, hakan ne ya ja komai, ni dai kawai bin sa nake da kunne, amma ina tsoracewa kaina kalaman da aka yi ta faɗa min na cewar ko an yi auren ba zan yi daraja ba a idonsa, ba na fatan hakan ta tabbata, bai kawo lefe ba, kuma ba wanda ya tambaye shi, saura kwanaki uku auren dai ya kawo kaya a ɗinke kala biyar, da takalma biyu jaka biyu, sai mayafai da sarƙa, ya ce na yi fitar biki.
Haka aka ɗaura auren, ba a yi wani taro ba, sai 'yan'uwa na kusa ne kawai suka zo, aka je aka jera min kayana a gidan, an tarar ma ya zuba kujeru masu kyau, kayan kallo da babban firji a falo, haka ɗakinsa ma ya saka gado, aka jera sauran kayan a ɗakunan da suka yi saura, a daren da za a kai ni ɗakina Maman Anisa ta saka ni a gaba zuwa gidanmu don na nemi yafiyar iyayena, Mama ta ce ta yafe min ita dama ba ta ƙullace ni ba, yayin da Baba ya ce ba zai sake cewa komai a kaina ba, amma dai na sani ya bar wa Sadam ni har abada, kar na sake na ce zan zo gida na kwana ko da ziyara ce ballantana yaji, idan zai dinga yankar naman jikina yana ci kar ma a faɗa masa ballantana a yi tunanin zai ɗauki mataki, tun da har na iya yin watsi da tarbiyyar gidansa to na je na rayu da wanda na zaɓa rayuwa ta har abada.
Na ci kuka a ranar kamar babu gobe, na san na yi laifi, ban yi wa iyayena adalci ba, amma a ganina ko ma me na yi bai kamata Baba ya yanke wannan hukuncin mai tsauri ba a gare ni, tun magriba kowa ya watse, wajen ƙarfe tara Sadam ya zo shi kaɗai ya ɗaukata duk an yi zaton ma dai gobe ne kai amaryar, tare da Baban su Anisa muka tafi ni ina bayan mota shi yana gaba, sai da ya raka ni har ɗakina, ya haɗa mu ya yi mana nasiha, sannan Sadam ya mayar da shi gida, ina zaune ina ta share hawaye ya shigo gidan, hannunsa ɗauke da ledoji, ya ajiye, sai na ga jikinsa a sanyaye fuska babu yabo babu fallasa, sam babu wani zumuɗi na angwaye, ya zauna a kusa da ni muka yi shiru na ɗan lokaci, kafin ya ce"To Sayyada daga ƙarshe dai aurenmu ya tabbata, sai mu ce Alhamdulillah! Allah Ya ba mu zaman lafiya, Sayyada ina son ki, kuma ina fatan za ki cigaba da bin ra'ayina a komai, idan kika yi min biyayya a zamanmu na yi miki alƙawarin samuna yadda kike so, ba ana cewa wasu mazan mijin ta ce ba? To ni kam zan zame miki kan ta ce".
Ni dai na kasa cewa komai, ya ce"Kin yi shiru, ko dai ni kaÉ—ai nake farinciki da wannan ranar?"
Sai na fashe da kuka sosai, na kwanta a jikinsa na riƙe shi na ce"Ni amana ce a wajenka, Babana ya ce ya zare hannunsa a lamarina ya sallama maka ni, ya ce ko yanka ni kake yi bai amince na koma gidansa ba, ballantana yaji, ziyara ya ce ba zan sake zuwa na kwana ba, Sadam kai kaɗai ne da ni a yanzu, ka dubi Allah ka yi mini adalci a zamanmu, ka yi wa iyayena adalci ka kula da ni, ko haka zai wanke musu ƙuncin da na saka musu a zuciyoyinsu, don Allah ka rufa min asiri mu bawa maraɗa kunya".
Ya fara shafa bayana yana cewa"In sha Allah Sayyada zan yi iya yina na ganin na yi miki adalci, in sha Allah babu wanda zan bawa damar yi miki dariya, za mu zauna lafiya matuƙar za ki cigaba da yi min biyayya".
Mun ɗan dade a haka kafin ya ɗago ni ya ce na je na yi alwala mu yi sallah, bayan mun idar ya miƙo min ledar da ya shigo da ita, na kai kitchen na juyo mana kaza a faranti tare da kofina, muka ci muka ƙoshi, raina duk babu daɗi, jiki a mace, shi dai ban san mene ne a zuciyarsa ba, bayan mun kammala ya shiga ɗakinsa ni ma na shiga nawa, na sake yin wanka, na saka rigar bacci mai ɗaukar hankali, tun da a yanzu babu wata kunya tsakanina da shi, na koma ɗakin nasa na tarar shi ma ya fito daga wankan, ya saka kayan bacci ya kwanta yana cewa na kashe hasken ɗakin, shiru na yi bayan na kwanta ina jiran ta inda Sadam zai fara taɓa ni ko ya matso kusa da ni kamar yadda na san zai yi wuya ango ya kasance a daren farko bai ko kai hannu jikin amaryarsa ba, amma sai na ji shiru, a zatona yadda yake mararina idan mun haɗu a yau da na zama mallakinsa zai yi fiye da kullum, sai na ga saɓanin haka, sai ni ce na ja na matsa kusa da shi, na kwantar da kaina a jikinsa, a haka bacci ya ɗauke mu.
Da asuba ya tashi, ya tashe ni, sannan ya tafi masallaci, bayan ya dawo ya sake kwanciya, ni kuwa zaune na yi ina ta tunanin wannan sabuwar rayuwa da na shiga, ina kuma istigfari har gari ya waye, na tashi na shiga kitchen na haÉ—a mana abun karyawa, komai na kayan abinci akwai a store É—in dake kusa da kitchen É—in, ina kammalawa na gyara gidan sannan na yi wanka na yi kwalliya na je tashinsa, na same shi yana shiryawa, na yi masa murmushi na ce"Ashe ka tashi".
Shi ma ya mayar min da murmushin ya ce"Na tashi, ai na makara ma, zan je wajen aiki".
Na ce"Aiki? Ina alƙawarinmu da kai, na cewar za ka ɗauki hutun sati ɗaya idan mun yi aure?"
Ya ce"Ban manta ba, abun ne ya zo babu shiri kin ga ai, ban kammala wasu ayyukan ba, ga shi Abba yana gari, idan ya ga ba na zuwa Company za mu samu matsala".
Na marairaice na ce"Kuma ni kaÉ—ai za ka bar ni a gidan?"
Ya ce"Ki yi haƙuri, next zan ɗauki hutun sai mu huta".
Ya kammala shirin ya fito, muka ci abinci na raka shi ƙofar falo ya tafi, na koma na yi wanke-wanke na kwanta ina ta tunanin yadda zaman aurena zai kasance.
A ranar dai ya kusance ni, abun dai kamar yadda muka saba, amma bambancin É—aya ne a baya idan mun gama zai ta yabo na, da nuna jin daÉ—insa, yau kuma sam bai yi wannan ba, washegari ma hakan ce ta faru, mun kammala na fito daga wanka yake cewa"Ni wai Sayyada ko irin gyaran amaren nan ba a yi miki ba a gidanku? Ta ya zan ji ki yadda na saba jinki a waje?"
Na yi shiru na ji duk na kunyata na muzanta, sai yanzu ma na tuna ya kamata na gyara jikina, amma ai a ƙa'ida buduruwa gyarata ake yi ba ita za ta nema da kanta ba, wata zuciyar ta ce min ai ke kin zubar da garinki shiyasa, kuma na yarda da hakan.
A sanyaye na ce"Kenan ba wani daÉ—i da ka ji?"
Ya ce"Ina fa daÉ—i abu salam? Dama haka ake amarya? Gaskiya ya kamata ki gyara ko ki ce a gyara ki".
Na ce"To a yadda auren namu ya kasance wane ne zai yi tunanin gyara ni? Kuma yanzu kowa yana jin haushinta wa zan tunkara da batun gyara?"
Ya ce"To ki san dai yadda za ki yi, don idan aka tafi a haka ni fa sam ban mori amarci ba, ji nake ga maganin nan ana ta tallansa, ki nemi inda za ki siya zan ba ki kuÉ—in".
Na ce"To zan nema in sha Allah".
Na kwanta jikina duk ba ƙwari, sai ya matso kusa da ni ya kwantar da kansa a jikina, saitin kunnena da shu'umar murya ya ce"Baby, don Allah ina neman wata alfarma".
Na ce"Allah Ya ba ni ikon yi maka".
Ya ce"Yanzu idan kin gyara jikinki sabuwar rayuwa za mu buÉ—e mu dinga shan amarcinmu daidai gwargwado, haka kuma ba zai yiwu ba muddin kika samu ciki, gaskiya dama ni a tsarina na fi so sai mace ta yi shekara É—aya mu huta da juna sosai mun sake fahimtar juna mun ga tsara zaman mu sannan ta fara haihuwa".